NOVELSYAR RAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

YAR RAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

YAR RAWA COMPLETE HAUSA NOVEL

Washe gari da wuri ta tashi, ta ma Mubarak wanka tayi ta saka dogoj wando da riga sannan ta dora boyfreind jarket mai matuqar kyau da ta kusa guiwar ta, ta zira takalmi ta dora mayafi akan ta, tulin gashin kanta data daure ya bayyana ta qasan qaramin mayafin nata, a haka ta tako ta kulle qofa,mai gadin na hango ta ya taso da gudu ya duqa ya gaida ta, amsawa tai cikin sakewar fuska, ” Bala” wani saurayi ne ko nace matashi da ba zai wuce 27 ba ya taho da gudu ya duqa gaban Baba mai gadi ” gani Baba” ” ranki ya dade ga wanda zai na kai ki duk inda kk so,” godiya tai tace mai tana son ya kaita wani kamar wajen cin abici da zata ci ta dan shaqata haka, amsa mata yai da to, ya karbi jakar hannun ta, ya bude mata mota, ta shiga sannan ta mai godiya, mamakin. Ta yake in tana masu godiya, wani qayataccan Hotel ya kai ta, a cikin garin kano, iya haduwa wajen ya hadu, kallon wajen take da sha’awa duk da cewa wajen ba za a kwatanta da ire-iren wuraren da ta saba gani ba, amma ya mata kyau sosai, shiga tai ta ci abinci mai rai da lfy ta tasa aka bawa driver ma dan qin shiga yai ta matsa suka shiga tare, yaci yai qat, yana fadi a ranshi ” da haka masu kudi ke kula da masu aikin su ba za a samu masu masu mugunta ba daga masu aikin sun” bayan sun gama ne tai umarnin a hada mata take away, suna gamawa ta miqe ta fara tattakawa, tana ganin yanayin wajen, a yawon da take ne ta hanqo wani waje da mutane suka taru mata na ta rawa, ana kallo, ana tafa masu, abun ba qaramin burge ta yai ba, tana murmushi, taji wani ya mata magana a gefe…

.
[1/9, 2:48 PM] Haermeebrah: ???????? ‘YAR RAWA ????????

   BY HAERMEEBRAERH

This page is for u dear as promised Hafsat Bello ( Maman Afaf) ki huta ❤

Page 9:

Juyawa tai, wani saurayi ta gani, tare da shi akwai wata budurwa, siririya sosai fara mai kyau, ga hushirya, sai dai ko kadan ba ta kama qafar Lamyah a kyau ba, dan kuwa ban bancin dake tsakanin su kamar na Cute one( Hussy)???? ne da Queen( Hassy)❤murmushi sukai wa juna, daidai nan driver n ta ya iso dauke da take away din su, yana kallon ta gefen saurayin nan sai ya fadada murmushin shi, yace ” Aaa manyan gari ana ganin ku dama? Ko dake dama wane mu direbobi da irin ku matan manya? ” dariya budurwar tai tai fari da ido, tace ” Bala Driver kenan, ai kai na ce maka ina son ka, kai ne dai kk ja baya, ni dai rawa ce ba fasawa zan ba, koma me mutane zasu ce sai dai su fada, amma ni da ka ganni nan ba na yawon banza, rawa a jikina take, dana ji kida zan taka kuwa, so ni ban damu da surutun ‘yan unguwa ba” ta fada tare da daga kafada, mamakin irin wannan surutu na wannan budurwa take, daga magana biyu zuwa uku tai goma ita, budurqar ce ta miqawa Lamyah hannu, tace ” ni suna na Farha, kuma ina zaune a unguwar su Bala amma unguwar da yake aiki nake nifi” murmushi lamya tai bayan ta miqa mata hannun ta daya da wanda bai dauke da mubarak tace ” ni suna na Aishaa amma ana kirana da Lamyah” daga hausar ta ta gane ko wace ce Lamyah, cikin zumudi ta ke magana, ” Laaaahhh ke ce wadda aka ce zaki dawo unguwar mu daga dubai? Woww, i mean woww sai gani ga ki, u have no idea yanda na matsu na ga wace ce ke,
dan labarin ya karade ko ina a unguwar mu, mahaifin ki ya kyautata ma ‘yan unguwar mu ba kadan ba, ya mana alkairi mai yawa, duk da bamu taba ganin shi ba, ta hannun mai unguwar mu ya isar da dikkan saqon da ya ke son isarwa ga wadan da ke buqatar taimako,” Lamyah ce cikin dariya sosai tace ” do u really talk like this all the time?, ” itama dariya tai ta kada ido tace ” yeh haka nake, dan ma kin samu yau bana jin surutu, raina bace yake ban samu shiga rawa ba” ta qarasa cikin jimantawa kanta, kiran sallar azahar ne ya katse su, inda sukai sallama, farha tace ma Bala sai sun hadu a gida, in ba damuwa zata kawi wa Lamyah ziyara, Lamyah ta tabbatar mata ba damuwa, zata so hakan.

Da yamma kuwa sai ga Farha ta iso cikin shigar ta kamar kullum doguwar riga da mayafin ta, wanda cikin kayan qananan kaya ne, sallama tai Baba Mai Gadi ya bude mata, duqawa tai har qasa ta gaida shi, tace mai ina Bala, yace yaje makaranta, dake yana BUK ne , yana a 200 level ne, sallama tai wa baban.ta shiga ciki, knocking tai a qofar inda Lamyah ta bude mata, tayi zufa.sakamakon rawar da ta tiqa, dan da suka dawo tai wanka tai sallah, ta zauna bayan ta sallami Mubarak ta bashi abinci ta hada shi da abin wasannin shi, stumin rawar ta ya motsa, daga nan tai ta rawa, data gaji ta ci abinci tai brush, sannan ta dawo ta dora daga inda ta tsaya, tana kan rawar ne Farha ta katse ta, dan gajeren tsaki tai, tana budewa da ta ga ita ce, cikin sakewa ta bude mata ta mata izinin shiga, dan sai take jin ita kam tayi qawa, dan runguma ta mata irin ta larabawa, ita ko Farha bata saba ba sai taji daban, wajen zama ta nuna mata ta wuce kitchen, kan ta dawo sai ganin Farha tai tana ta tiqar rawa, abun ya burge ta, aje ruwan tau sukai ta rawar sai da suka gaji suka zube kan kujera suna dariya tare da maida nunfashi, ” gaskiya yau naji dadi sosai, ashe kema haka kk iya rawa?” ” Hmmmm ai in kk ce rawa daya kenan, duk qawaye na na fisu iyawa, dan kuwa ko a makaranta in ana yi na fi kowa, dana fara kowa komawa gefe yake ya hau kallona, amma kuma ke taki salon rawar daban yake, BELLY DANCE kk yi,” ” eh haka ne, don mu ta can ita ake yi, rawar Larabawa kenan ai, shiyasa na keyin ta nima, in ina yi Abii yana cewa i am the best dancer ever” tinawa da Abii n ta ya sa kwalla ta kawo mata, tashi tai ta dakko wayar ta ta sake gwada layin shi, amma yanzu ma a kashe, kuka ne ya kwace mata, hankalin Farha ba qaramin tashi yai ba, nan take ta matsa kusa da ita, tana son dora hannun ta a bayan ta ta lallashe ta, tana tantama,janye hannun tai, daga baya kuma ta qara dorawa cikin inda inda, ta fara magana ” me…. ya faru… kk kuka?” ” Farha Abii na tin da nazo bai kira mu ba yaji, ya muke, sannan ina son naji ko yana lfy, gabana na mugun faduwa inna tina shi, hankali na na tashi kwarai” bubbuga bayan ta Farha tai itama ta share hawayen ta da suka fara ambaliya, tace” kiyi hakuri Lamyah kinga gwanda ke, kina da uban da zaki kalla ko mai daren dadewa ki tabbatar da cewa naki.ne, ni kuwa da dama tin kan a haifen nawa ya rasu, tawa uwar ta baro dangin miji da suka takura mata, ta zo nan ta rayu dani, har Allah yai cikawar ta, yanzu shekara biyu kenan, wannan rawar da kk gani dazu, ita ke riqe ni, banda kowa, ba wani nawa dan ban san dangina ba,” kuka ne yaci qarfin ta, wanda ya bawa Lamyah tausayi matuqa, lallashin ta tai, ta labarta mata itama labarin rayuwar ta, gaba daya, da iya wanda ta sani da wanda taji labari, Farha ta matuqar tausaya ma Lamyah, ” Lallau bahaushe yai gaskiya, in kaga jarabawar wani, naka sau ya zama nafila, sai dai ke da gatan ku ,ni kuma banda kowa,” ” Farha kin yi kowa, dan zan so ki dawo nan da zama mu zama kamar sisters, kinga Mubarak yanada yayu uku kenan, duk sanda mukai waya da Yah Amee na zan bashi labarin ki, dan shima tin da nazo bai kira ni ba , bari dai na duba me ke damun wayata ne, dan gaba daya kamar an canjan komai haka take, ita din ce dai amma is like komai ya sauya, No Abii kawai nake iya gani,” dubawa tai sosai sai taga wani sabon layi ne na Nigeria aka saka mata, kuma ba Number din kowa, sai na Abii, itama sai yanzu ta kula sam no kamar ba daidai bace, wani irin tashin hankali ta shiga, meke faruwa ne, ta sunkui da kanta qasa tana nazari, ga zufa dake karyo mata, wani tinani ne ya shige ta, ta miqe kamar an mintsine ta, fadi take” Noooo Noooo pls this is not happining again pls” sai ta rushe da wani marayan kuka, ta durqusa ganin kukan ta ne yasa Mubarak rarrafawa ya rungume ta, yana kuka, lallashin shi Farha tai dan ita Lamyah gaba daya bata hayyacin ta, kuka kawai take” Farha sun kashen Abii na, tabbas shima yasan zasu kashe shi, na rasa shi kamar Ammii na, yasan zasu rava mu da shi, shiyasa ya turo mu nan, Abii meyasa kai haka, baka bari mun kaisu qara kotu ta bi mana haqqin mu ba? Abii me yasa ka basu dama, akan dukiyar ka? Daka sani ka basu, komai ko zamui yawo tsirara, zamu haqura da juna, Abii..” nunfashin ta ne ya fara sarqewa, ruwa Farha tai saurin bata, da kyar ta shq kuka kawai take ba qaqqautawa, ” Abii hannun wa ka bar mu? Ina zan samu Yah Amee na ? Ya zan na samu Baaba Mus’ab ? Ban da tabbacin dangin Ammii zasu karbe mu, na fi son sai Mubarak ya kai matakin Secondary,a qallah dai da wayon shi, sai mu je, don ko sun koren ba zan ji kadaici ya min yawa na rashin Ammii ba” kuka suke dikan su su ukun, kwankwasa qofar akai, da kyar Farha ta tashi ta miqawa Lamyah Hijab din da ta gani a ninke a gefen kujera, ita kuma ta maida rigar ta, sannan ta je ta bude qofar, Bala ta gani, murmushin qarfin hali tai masa, izini Lamyah ta bashi ya shiga, ya zauna a gefe, ” Farha na sha gaya maki ki daina kuka, kowa da kk gani a duniya akwai rayuwar da Allah ya tsara masa, taki jarabawar kenan, dan haka ki ragewa kan ki damuwa, ko kin daina ramar nan da bana so” ya qarasa cikin fara’a, murmushi tai, cike da shagwaba tace” Allah Bala in ka qarasa abunda ke zuciyar ka zamui fada” ” Habaaa ni.na isa nace maki qugu kamar an daurawa tabarya zani? Wane ni?” Ya fada yana kama baki, murmushi sukai, in da Farha ta nemi izinin sanar da Bala komai, dan Farha ta dauke shi aboki, shine dai ke baya2 da ita, dan a unguwar sun dauke ta a ‘ Yar mace, kuma karuwa, Farha batai ilimin boko mai zurfi ba, dan mahaifiyar ta ta rasu tana SS1 so yanz haka shekarar ta 16, wajen karatun islama kuwa, itan A ce ba B ba, dan akwai shi sosai, wannan dalili ne yasa Bala ke koya mata karatun bokon sosai, bayan Bala yaji labarin dika, ya matuqar tausaya ma wadannan bayin Allah, da kan shi….. dan shi ta shi uwar rabuwa sukai da Baba mai gadi wai ba zata iya rayuwa da miji mai gadi ba duk kyaun ta, haka dai ya sallame ta, shi ko Bala yaqi binta dan bata da dalili mai kyau.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button