YAR SADAKA 1-END

YAR SADAKA Page 31 to 40

Daga Mata Kai nijlah tayi tana murmushi ahaka husna ta riqa diban nijlah da hira har suka Shiga gidanta..

A falo suka zube tana jerawa nijlah sannu itako sai amsawa take tana qara shigewa jikin husna” kunsan dai nijlah dasan jiki lolxx..

Suna Zama mujaheed ya shigo Yana cewa oyoyo sai kuma yakasa karasawa ya zuba nijlah Ido Baya kio qiftawa” da gudu Ayman ya zo ya wuce Mujaheed da niyyan rungume mahaifiyar tasa husna tasa hannu ta dakatar dashi tana cewa’Kai tsaya mana bakaga aunty kwance akan cinyana ba,,Koso kake Ka qarasa laifin daba naka ba?

Dariya Ayman yayi irin Nasu na yara Yana cewa’ mami aunty ne?

Eh aunty ne,na kawoma kana so’ cikin gwaranci Ayman yake magana’ mujaheed kam kasa magana yayi sai Ido daya zubama nijlah..

Mujaheed yaji husna ta Kira sunansa’ Sosa Kai yayi Yana cewa’ na’am aunty ina kika samamana wannan kyankyawar babyn?

Oh kaidai Ka cika tambaya Ka Bari dai na huta Naci abinci, itama ta Samu nutsuwa danba lafiya gareta.

Murmushi yayi Yana cewa to ai ni yinwan harya tafi’ Amma dai bakomai jeki shirya yafada Yana sake kallan nijlah da zuwa yanzu tafara lumshe ido sabida bacci dake idanta.

Tashi husna tayi ta riqe hannun Nijlah nan ta kaita wani Dan qaramin daki me dauke da gado sai mudubi da ‘yar qaramar wardrobe.

Kan gadon ta kwantar da nijlah tana cewa’kwanta ki huta Naga alama ko wanka bazaki iyaba’ nijlah batayi magana ba ta lumshe ido nan da nan bacci ya dauketa.

Sai yanzu husna ta safke ajiyar zuciya,ta karanta adduoi ta tofa Mata, Saida ta qarewa nijlah kallo cike da tausayawa ta fita tare da jamata kofa ..

Dakinta ta Shiga ta cire kayan jikinta ta fada toilet’ bayan ta fito a wanka ta dauko doguwan Riga tasa da hijabi ta tada sallah.

Tayi rakaa biyu aka shigo dakin da sallama ganin tana sallah yasashi kwanciya Kan gadon Yana latsa wayar hannunsa.

Saida husna ta idar da sallah ta tashi a hankali ta hau Kan gadon ta lallaba ta rungumeshi ta Baya tana dariya’

Ture ta yayi Yana cewa ni ba ruwana dake kin dawo koki nemeni bayan tin tini mujaheed yajemini da daddadan labari.

Kashe murya husna tayi tare da langwabar dakai tana cewa’ eyyah hubby na’ ayi hakuri sauri nake nayi sallah nasan idan Muka hadu bazan iya aikata komai ba.

Far yayi da Ido kama mace alaman tinani sai kuma ya sauke idon akanta Yana cewa’kuma fa hakane husna kedince ta dabance kin iya salan Jan hankali.

Allah ko daddy Ayman?

Dage Mata Gira yayi Yana cewa ni duk ba wannan ba’ wacece kika shigo da ita gidannan tazo ta daga hankalin kaninki?

zaro Ido husna tayi tana cewa hubby kamar yaya?

Eh abinda Muka Dade muna nema’ duk da yace yarinyace Amma Shi tayi masa a hakan….

Dariya husna tayi ta daga hannu Sama tana yiwa Allah godiya.

Sai kuma ta safke tana cewa’Kai mujaheed ya iya zumudi’ daga ganin sarkin fawa sai Miya tayi zaqi ko shiyasa yanzu naketa ganin kiransa.

Shine mana’ Nima tinda kika dawo ya takuramin sai magiya yake nazo nagayamiki kibarshi yayi magana da ita.

Ikon Allah aiko da yazo bazan bashi wannan damar ba sabida kanwata Hutu take buqata yanzu ba surutu.

Ah dear ko kin manta yadda muke addu’a akan yarannan Amma yanzu munsamu yaga Wanda ya furta da bakinsa Yana so zaki dakatar dashi.

Rungume sa tayi tana cewa’ hubby kennan wallahi inaga nafi kowa farin ciki da hakan sedai..

Sedai me ya katsata tare da zuba Mata manyan idanunsa.

Hubby na yarinyar batajin dadi a yanzu Hutu kawai take buqata.

To wai ni wacece ita’ kodai yarinyar aunty aysha ce? Yayar husna kenan.

Ah ah fa hubby..

To wacece ita’?

A ina kika sameta?

Menene dalilin………..

Comment & share

*Momn sultan ce ✍ ✍✍*

???????? *’YAR SADAKA..*????????

*STORY & WRITING …*

         *BY*

*MOMN SULTAN*

*DEDICATED TO…..*

*MMN AMATULLAH*

*SPECIAL GIFT TO…*

*HABASIYA TKM….*

*AYI HAKURI DA RASHIN JINA” NI KAINA BA HAKA NASO BA. NAGODE SOSAI DA YADDA KUKE NUNA KULAWANKU AKAINA,,WADANDA SUKAMIN MAGANA BAN AMSA BA SUYI HAKURI.*

7⃣2⃣&7⃣3⃣

Shiru husna tayi tana kallansa ba tare da tayi magana ba’ tana tinanin ta yadda Zata fara gayamasa, sabida sanin halinsa musamma yanzu da mujaheed ya Nuna itace zabinsa..

Cike da San jin zancen ya katseta ta hanyar janyota jikinsa’ yasa hannu ya zagaye qugunta tare da hura Mata iskar bakinsa Yana cewa’ dear kinyi Shiru’ kefa nake sauraro ya qare maganar a shagwabe’

Ajiyar zuciya husna ta safke tana Wasa da kwantancen gashin bakinsa’ sedai har zuwa yanzu husna bata Sami kwarin gwiwan bashi labarin nijlah ba,, tome ma ta na sani game da nijlah mezan gayamasa?

Husna ta tambayi kanta jikinta na rawa’ 

Ido ya zuba Mata Yana nazarin ta kafin yasa hannu biyu ya janyeta Yana jefa Mata wani irin kallo Wanda ya qara dagama husna hankali tayi saurin sauke nata idon qasa tana addu’a.

A hankali ya bude bakinsa Wanda yayimasa nauyi Yana cewa’ husna meyasa zakimin haka?

Ko Dan kinga kanina ya kwallafa Rai akan yarinyar nan shiyasa kikesan bata Raina?

Dasauri husna ta Shiga girgiza masa Kai sedai har yanzu bata Samu kwarin gwiwan yimasa bayani ba..

To menene ni Dan Allah ki gayamin’ kema kinsan bakya laifi a gurina.

Saiya tashi ya matsa inda take zaune Kan bed ya zube kafafunsa a qasa Yana rokon ta’

Dear ki tausayawa mijinki’ ai husna bata Bari ya qarasa magana ba itama tayi saurin zubewa a qasan qirjinta na halbawa har Yana iya jiyo sautin bugun zuciyarta,, 

Cike da tashin hankali da firgice husna ta fara magana’

Hubby na kayi hakuri da aika aikan danayi’ wallahi bada niyya na daukoma Wanda bansani ba na kawo cikin gidanka,, nayine sabida muma mu qaru da samun ladan taimako..

Sosai kanshi ya daure ya kuma kasa ajiye hakan a cikin zuciyarsa har Saida ya amayar da abinda ke cikinta ta hanya yin magana cikin sanyin jiki..

Dear ban gane abinda kike nufi ba, kiyi magana yadda Zan gane?

To husna tace bakinta na rawa’ ta cigaba da magana.

A hanya ne ina tafiya na tsinci nijlah kwance a titi Mai napep din gaba ya bigeta,,Allah ya tsare ina kallan gabana ban taka taba,,Saina tsaya na sata a mota na kaita hospital,,daga nan Naga ya dace ta zauna damu kodan Kona wani Dan lokacine kaga saimu nemi iyayenta’ cikin kuka husna ta qare maganar..

What,,husna yanzu yaya kikeso ayi,,kina nufin haka zamu maida nijlah ga iyayenta batare da mujaheed ya Samu soyayya taba,,sai ya tashi tsaye Yana girgiza Kai hankali sa a mugun tashi yace’

Wallahi bazan taba maida nijlah ga iyayenta ba har sai ta Samu soyayyar Dan uwana kafin ta koma ga iyayenta,,ta yadda bazata taba San a rabata dashi ba…

Tinda husna taji Yana furta baza’a maida nijlah ga iyayenta ba,zuciyarta tafara bugawa da qarfin gaske,,take jikinta ya dauka rawa itama ta tashi tsaye tana zagaye dakin zuciyarta na cigaba da dokawa Dan ba iya kunnanta maganar ta tsayaba har cikin jikinta takejin kalamansa na yawo, da kyar ta janyo jamuntarta tace..

Haba mijina kafasan yadda batan dan mutum keda tsayawa iyaye a rai,, har gwara suga gawar Dan Amma zakace haka,, yanzu fisabilillahi idan Muka bar yarinyar nan har zuwa lokacin da soyayyar mujaheed Zata Samu gurbi a zuciyarta,, kana ganin munyiwa iyayenta adalci?

Kama saukar aradu haka yaji maganganunta na jiyake kama ya kamata yayimata tsinan nan Duka koya Samu sauqin takaicin da maganar ta ta bashi sedai baze iya hakan ba..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button