YAR SADAKA 1-END

YAR SADAKA Page 31 to 40

Jikinsa a sanyaye ya qarasa Shiga falon sedai abinda ya gani yayi bala’in Daga masa hankali Har besan Sanda ya riqa tsallake kujerun daya Bayan daya ba’ ji yayi tamkar Ze Rasa mahaifiyar Tashi sabida Jin sautin bugawan da zuciyarta keyi.

Yana zuwa inda take yayi saurin rungumata jikinshi Yana jera Mata sannu’

Lafiya mummy badai haduwa kikayi ba?

Mummy Bata Iya Magana ba Dan Iya azaftuwa ta azaftu Banda nuna masa cinyanta Babu abinda take tanayi tana kuka.

Shiru yayi Yana Jin kukan nata kama ana diga masa dalma’ da kyar ya Iya tashin mummy ya kaita Kan carpet Yana jera Mata sannu’

Mummy Bata Iya amshiba Sai cije lebe take tana Kiran wash wash’ sannu mummy Wai garin Yaya Hakan ta faru?

Nijlah ce da Maryam suka shigo suka bar Musa nata zagaye faluwa yana sumbatu cikin tashin hankali.

Cikin wannan Hali Mummy ta dago kai’ tana cewa’ ku ficemin da wannan shegiyar yarinyar banasan ganinta’ Sai kuma tasa kuka tana cewa’ Auta kaga abin bake gayama Ko,, gashinan tayi sanadiyyar gurguncewar uwarka Dan banza kawai da Baka Kishina…

Baba ni kuma, menayi Miki Nijlah ta fada tana nuna Kanta?

Ki fita nace, fita Dan ubanki’

Kallan Maryam mashkur yayi bakinsa Na rawa yake tambayanta?

Maryam meke faruwa kiyimin bayani Dan Allah,, mashkur ya qare maganar cikin rauni da tausayama rayuwarsa.

Bakin Maryam Na rawa take gayamsa abinda ya faru ta qare da cewa’

Nidai bansan yadda akayi ta fadi ba’ Iya abinda nasani Na gayama.

Bata Ida rufe baki ba mashkur yayi Kan nijlah ya fizgota fada Kan kujera’ nan ya zare belt Yana daka Maryam tsawa’

.fita a Dakin nan kafin Na Hada dake..

Sosai jikin nijlah ya Shiga rawa tana bashi hakuri tare da cewa’ wallahi Bani bace wasu aljanu nagani inaga itama sune suka Bude Mata Ido kaga Kuma tayi qatuwa da yawa bazata Iya gudu ba shiyasa suka cutar da ita..

Haushi mashkur yawaraji Dan Dama ya tsani ta Kira Mummy da qatuwa gani yake kama raini ne’ 

Bude baki tayi da niyyan cigaba da bashi hakuri Amma ya rufe Ido ya Daga hannu ya safke Mata belt din a bayanta’

Razananniyar qara nijlah ta saki Dan tinda take ba’a taba yimata irin wannan Duka me Shiga jiki ba Dan Ko Dukan da Yasmeen tayi Mata bekai wannan zafi ba.

Saida tadena Ji Na wasu ‘yan lokuta kafin jinta da ganinta su dawo’ 

Rikice masa tayi ta Kuma Rasa inda zata sa Kanta Taji Dadi Banda juya kai Na azaba Babu abinda nijlah take,,kuka takesanyi sedai kukan yaqi zuwa haka ta kife a gurin tana birgima.

Daga belt din ya kumayi Yana cewa’ kin Tashi kin Bata hakuri Ko saina qara miki’ nidai banga lokacin da Zaki hankali ba nijlah Anya Ko kinaso mu zauna lafiya?

Bata Iya Magana ba Saima shesheqan kuka ta riqayi numfashinta Na sarqewa’ amma Duk da haka be kyaketaba ya dakamata tsawa Yana koranta waje.

Da gudu nijlah ta Tashi ta fita a Dakin cike da tashin hankali ta fita.

Tana fita mashkur yasa hannu ya goge hawayen tausan nijlah Dan ba’a San ranshi yayi Mata haka ba yayine kawai sabida mummy Taji Dadi ta Kuma barshi da nijlah Dan yasan Babu makawa mummy zata Iya cewa saiya saki nijlah adaidai wannan lokacin Duba da halin daya tsinceta a ciki..

Kallan Mummy mashkur yayi Yana cewa’

Mummy kiyi hakuri nizanyi maganinta,, yanzu ki Tashi Na kaiki hospital’ 

Cike dajin ciwo mummy tace ‘ Bazan Iya tashiba auta’ ka Kira Dr kawai yazo ya dubani anan..

Beyi Magana ba yayi dealing number likitan..

Nijlah na fita ta zauna bakin kofa tana kuka tare da Dana sanin yadda da rabuwa da kaka Ashe dai talauci yafi Wani tashin hankalin sauqi,dama shirme nake danake ganin Zan Samu farin ciki Idan nayi aure ya Allah nijlah ta furta daqarfi tana yarfe hannu sabida Har yanzu bayanta be gama saisaita ba.

Hannu tasa ta shafa gurin aiko tana cirewa taga jini kwance a hannunta’ wayyo Allah nijlah saita Tashi da gudu tana zagaye get din tana Kiran kaka da laman’ 

Dama haka aure a birni yake gashi Na kawo kaina inda za’a kashemini’ wallahi Bazan zauna ba gida Zan tafi’

Bata qara neman shawaran zuciyantaba ta tashi,,Bata Ko dauki takalmi ba ta fita da gudu tayi titi’ Sai da tayi tafiya mai Nisa kafin taga me napep ta tsayar dashi’ .

Qoqarin tsayawa yake nijlah Tasha gabansa Aiko ya bigeta ta fadi gefe’ tsoro da tashin hankali suka sa me napep ya gudu Sai wata matashiyar budurwa dake Bayan me napep dince ta tsaya kasan cewar layin ba mutane sosai ta nemi dauki Bata samu ba,,haka ta cire mayafinta ta dauka nijlah tasa a Mota tana mejin tausan yarinyar ta tafi asibiti da ita…

_________

Haba kawata yakamata ace munyi shagali a bikin nan gashi wannan corona tazo tayi kaka gida Har ansa dokan ta bashi a kowanne state kinga Ko Dole a Daga biki suwa Bayan Sallah..

Zaro Ido mubeena tayi tana cewa’haba kawata keda Zaki addu’a ayi bikin nan a gama saiki kawo wata magana’ Naga Dai ba dolene ayi chasu a biki ba.

Ke kinga mubeena kibari kawai muyi a lokacin da zafi mana Dadi Ko bakisan ita Yasmeen’yar Gata bace Dan haka yakamata lokacin Duniya tasan da aurenta,, zee ta fada tana kallan yasmeen.

Yatsina fuska Yasmeen tayi tana hararan mubeena’ Sai kuma ta Kalli Zainab tana cewa yauwa zee gayamata gaskiya to Idan ba’a Daga biki ba Sai ki gayamin ta inda abokan Abba zasu shigo qasar kinsan abbana bashida abokai dayawa anan yawancinsu ba ‘yan qasa bane..

Gaskiya ne kawata suka tafa da zee’

Cikin rauni Yasmeen tace’ zee nifa inaga kama mashkur Baze yadda da Hakan ba?

Dan Wallahi ya matsu da maganan auren nan’

Ai Toba Dole ya Daga qafa ba,,nifa Dama gani nake wannan mijin naki zee mugun takura Ke Allah yasa kin tsuma jiki sosai,,dariya suka sa zasu qara Magana mama ta shigo Dakin tana cewa’

Ku Kuma bakijin yinwane kuketa Hira haka Baku neman abinci Yasmeen..

Kuyi hakuri kwana biyu banajin dadi sosai.

Comments & share

*Momn sultan ce*✍✍✍

???????? *’YAR SADAKA..*????????

*STORY & WRITING …*

         *BY*

*MOMN SULTAN*

*DEDICATED TO…..*

*MMN AMATULLAH*

*SPECIAL GIFT TO…*

*BABBAN YAYA’ H_UMAR….*

6⃣8⃣&6⃣9⃣

Mama yanzu zamun fito suka fada cike da ladabi” ku Tashi haka itama hiran ba Dadi takeba ana Jin yinwa.

Basu qara Magana ba suka Tashi sukafi Bayan mama data fita tana cewa’ kudai ‘yan Mata Baku da aiki Saina rawan kai Idan kukaji biki’ kai ni nagaji da wannan shirye shiryen Baku daqi chi yaqi chinyewa.

Jummai’ kina ina’ banga kin Hada kayan abincin ba?

Hajiya nagama yanzu Zan kawo’

DA gudu jummai me aiki ta fara jera manyan kuloli Akan dining tana cewa’ 

Ranki ya dade Dama Yasmeen ce tace kada Na raqa aje kayan abinci Idan ba Zama akayi za’a Ciba.

Murmushi mama tayi taja daya Daga cikin kujerun ta zauna tana cewa kai ita Dai wannan yarinya ta fiye tsirfa’ Amma bakomai kema kin kusa hutawa da jaraban yasmeen’ dariya jummai tayi tace’ eyyah hajiya aiba komai..

Bata fuska Yasmeen tayi tana cewa’ to Idan kin gama gulman saiki Bani wuri Ko?

Sum sum jummai ta shige kitchen tana Bada hakuri.

Mama ta Kalli Yasmeen tayi Dan qaramin tsaki tana cewa’ Wallahi Yasmeen ki gyara balinki,, shikenan Ke baki da aiki Saina tsanar tsalaka’ shin Ke kikaba ubanki arziqin da kike tinqaho dashi? Shiru Yasmeen tayi mama ta qara daka Mata tsawa tana cewa’ tambayanki nake? Bakin Yasmeen na rawa ta Bude baki zatayi da Magana sukaji gyaran muryan Abba dake shigowa cikin falon.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button