YAR SADAKA 1-END

YAR SADAKA Page 31 to 40

Ka sakeni ka Bude kofan kaji’ nijlah ta fada a hankali’ be Iya tashiba Saima kafeta da yayi da tsummamun idanunsa Wanda ya canza Kala Daga fari zuwa ja’ sabida tsabar tashin hankalin dayake ciki.

Sai da yayi kusan minti 3 ahaka kafin yayi yaqi da zuciyarsa ya Tashi a hankali ya safka Daga Kan gadon Yana kallanta’ kasa kallan idanshi nijlah tayi sabida tsabar Kunya nan ta fara gyara riganta tana San zubda hawaye’ 

Dasauri mashkur yace’ shhhhhhiiiitttt Karki soma hawaye kinga Dai mummy na jirana.

Zaro Ido nijlah tayi tace baba fa kace’ wayyo Allah Na kado wallahi dukana zatayi kaga saita zube Akan bed tana neman inda zata buya’ Duk da halin da mashkur Ke ciki Saida yayi murmushi.

Kinga jeki Shiga toilet Karki Bude indai Bani Nace ki Bude ba kinji’ Bata Iya amshiba ta kwasa a guje ta fada jikin toilet da zaninta a hannu,,tana Shiga tasa key ta ciki ta kulle jikinta Na rawa sabida tsabar tashin hankali..

A hankali mashkur ya soma takowa zuwa jikin kofan tamkar Wanda egg ya fashewa a ciki’ hannunsa Na rawa yafasa zare key.

 Haryanzu mummy Bata Dena fadaba tana Kiran sunansa ahaka harya gama Bude qofan ya sauke idonshi ana mummy.

Tsaye take a falon tana sababi kama Wanda aka bama gasar Cin kofin duniya’ Ai tana ganin ya Bude tayi cikin Dakin Ranta a bace tana huci kama kububuwa’ Ke kina Ina Dan ubanki ki fito Nace wallahi Yau sainayi maganinki ‘Yar masu yawan Jeje da bakin halin tsiya wallahi Baku isaba kurwan Dana tafi karfinku matsiyata banza matsiyatan Wofi kina Ina mummy ta fada cikin ihu da amsa kuwwa, kai kace da sa’arta take fada.

Jikin nijlah ne ya dauka rawa Amma Duk Da haka Bata zauna ba Saida ta tashi ta zo jikin kofan tasa jikinta ta qara turawa yayinda bakinta be bar ambatan Sunan Allah da neman dauki a gurinshi ba..

Sai yanzu take danasanin Qin bin hajiya Khadija da tayi.

Sosai mummy ta Shiga zagaye Dakin tana neman nijlah Amma Bata gantaba.

Takowa mashkur yayi harya qaraso inda mummy Ke tsaye yasa hannu ya riqe nata Yana Magana a hankali’ mummy Wai Wa kike nema nifa kadaine a dakinnan Babu kowa..

Be kai Ida maganar ba mummy ta Daga hannu cikin fishi zata daukeshi da Mari’ 

Dasauri mashkur ya rufe idansa Dan Baze Iya kallan wannan baqar ranar ba sedai jin Shiru yasashi budewa idon a hankali,, itama mummy sauke hannunta tayi Dan bazata taba Iya Marin autan nata ba ta zuba masa Ido cike da bacin Rai..

Mummy kiyi Allah Dan Allah’ mummy kidena Daga hankalinki wallahi Babu abinda nakeso fiye da ganin farin cikin ki da kwanciyar hankalinki,,mummy Idan kina irin wannan tashin hankali Zaki dorawa kanki hawan jini kisa mu Shiga uku.

Kaine Zaka doramin hawan jini auta, Sau nawa Zan gayamaka banasan tarayyarka da kusanci ka da wannan aljanar yarinyar?

Cikin sanyin murya yace mummy wacce yarinya kike magana?

Nijlah nake Magana Ko kanaso kace Bata cikin. Dakin nan?

Bakinsa da rawa yace mummy batanan fa tana…

Tana gidan ubanka ko? Kayimin Shiru,,wallahi ka qarasa Magana tam Dinka.

 tana Ina Ko kanaso kace ba ita Naji kuka yanzu ba, wato kai Har Zaman aure kakeyi da ita Ko?

Kasa ya safke idonsa Yana cewa’ eyyah Mummy bafa haka bane laifi tayimin shine na duketa kikaji kukanta yanzuma dakyar ta Samu Na saketa shine ta boye, mashkur ya qare maganar cikin rashin gaskiya.

A Ina ta Boye Naga Dai ba kofan fita ta Baya?

Mummy bansani bafa,, Dan Allah muje ki zauna kibar tada hankalinki akanta.

To Ya kakeso nayi da rayuwata mashkur? Kodan kaga Na Dora soyayyana akanka shiyasa zakesan Bani wahala?

Ah ah mummy inaso ne Dai ki fahimceni’ mummy nijlah Amana aka Bani ita,Kuma matatace ta Sunna Na tabbata Idan Na zalinceta Sai Allah ya sakamata gashi marainiyace.

Kayimin Shiru Ko yaya,,Sai anyi Magana kace marainiya marainiya, shin ni Ina nawa iyayen Ko ita kadai kake tausai?

Ah ah Mummy nidai ki zauna Ko lemo kisha.

Anqi a zauna’ kaga mashkur ka kiyayeni, wallahi matuqar kanasan farin ciki saika Maida yarinyarnan garinsu” 

Shidai beyi Magana ba Yaja hannunta suka zauna kan daya Daga cikin kujerun dake ajiye a falon’ Tashi yayi ya kunna TV tare da daukomata ruwa da lemo masu sanyi yafara tsiyaya Mata a cup.

Mummy amsa wannan Kisha nasan kin debo rana?

Amsa mummy tayi tafara sha tana hararansa,,shidai mashkur hakuri kawai yake bata harta gama sha ta tashi tsaye tana cewa’

Jeka nemomin ita aduk inda ta Shiga Dan wallahi Bazan barta nan ba tazo tana samaka damuwa kaga saura 3 days afara bikin nan kada azo aganka a rame Dan wannan Har jini zata Iya tsotsema..

Zaro Ido yayi cike da tashin hankali yace’ mummy kibarta anan Duka zata sha Nifa Ko abincin kirki ba Bata Nike ba shiyasa kikaga ban damu da zamanta anan ba..

Ah ah Dai auta jeka kawomin ita ,,Dan gaskiya hankali Na Baze kwanta ba indai wannan ja’ irar tana tare da kai..

Magana zeyi mummy ta katseshi’ kaje Nace Ko.

Babu yadda ya Iya haka ya Shiga Dakin Yana Kiran nijlah.zuciyansa na quna.

Nijlah ki Bude nine fa, tana budewa ta saki kuka tana cewa honey ta tafi Ko?

Bata tafi ba,, kinga abinda taurin kanki Yaja Miki Ko nijlah gashinan mummy tace dake zata tafi..

Wani irin takaici da haushine suka cikata tare da Dana Sani mara amfani’ nan ta fara hawaye tana cewa’ kado Dan Allah kace aunty Khadija ta dawo Allah Zan bita,, wallahi Bazan qara yimata musu ba,,nadena Allah nadena Nijlah ta fada cikin kuka da tausayama Kanta..

Janyota jikinshi yayi Yana cewa’ kiyi hakuri Nida kaina zansa a satoki a hannun mummy kedai kawai kiyi biyayya ki bita ki Kuma Nuna Mata bakyasan Zama dani kinji?

Cike da sallamawa farin ciki nijlah ta dagamasa Mai tana goge hawayen fuskanta da gefen rigarta tace’ shikenan tinda haka kace, Amma tayaya za’a Iya satoni a wannan gidan naku,, nidai kawai kace mutuwa zanyi..

Kije kawai yafada yana Dagamata kai nan suka fito tare,, hankada qeyarta mummy tayi tana cewa wuce muje dangin Hau irin masifa Wanda Basu San komaiba Sai yawo a dawa.

Nijlah Na kuka suka fita ahaka ta sata cikin Mota ta juyo inda mashkur yake tana cewa.

Kai auta ka Kula da kanka Nina tafi sabida Yau inada manyan baki’ 

Cikin Dakiya da nuna rashin damuwa mashkur yace’ mummy wasu irin baqi kuma?

Wallahi su linda ne zasu zo wadannan nake aikin a NGOs dasu na Hada musu liyafa ta gani ta fada fatan kaima Zaka zo ayi Taran dakai, tinda jiya nake nemanka Sai yanzu danazo da kaina Na ganka.

Murmushi mashkur yayi Danya Samu hanyar ganin nijlah’ ya Kuma San yadda su Linda Ke ba mummy mahaukanta kudi sabida aikinsu Nada kyau Kuma mummy ta Iya aiki sosai shiyasa indai suka zo qasar Basa Iya tafiya Sai sun zo gidan mummy..

Shikenan mummy Nima yanzu Zan zo,, wanka kawai zanyi.

Dasauri mummy ta Shiga Mota tana cewa kadai zo da. Wuri nasanka da nawa,, Har mummy ta Shiga Mota ta juyo tana cewa kai auta, kada ka manta ka tahomin da diyata.

Diyarki Kuma mummy?

Kaci gidanku Ina da wata diya data wuce Yasmeen’ ka kawota itama su gaisa Ko?

Ciki ciki yace to mummy ya Koma ransa a mugun bace.

Kan gado ya kwanta tare da dafe kansa Yana tinanin halinda nijlah zata Shiga a hannun mummy’ 

Dasauri ya tashiga Shiga wanka Yana tinanin ta hanyar daze bullowa mummy’

Badan wankan ya Zama Dole ba da Baze yiba..

Suna tafiya nijlah Na kuka ahaka Har suka qarasa gidan Mummy’ driver ne ya Bude musu suka fito’ nan fa mummy ta Shiga rankwashin nijlah tana zaginta tare da tsintsine mata’ 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button