YAR SADAKA 1-END

YAR SADAKA Page 31 to 40

Tana fitowa Mashkur ya bugamata tsawa Yana cewa’ mayafi Nace ki dauko ko hijabi?

Turo baki nijlah tayi ta juyo tana San yin Kuka mashkur yace’ wallahi kikamin kuka tam..

Tana komawa Dakin ta kwanta Kan gado tana birgima tare da kuka mara sauti..

Kallan mashkur hajiya Khadija tayi tana hararansa tace’ haba Malam haka Ake kula da baby ?

Murmushi mashkur yayi Yana cewa kai hajiya nijlah rigimanta Sai ita Ni wallahi Har ciwan kai take samin’ 

Sai kaje gurin Yasmeen yake sauka Ko? Cewan jabeer cike da tsokala.

Mashkur be kulashiba Saima Bata fuska dayayi..

Dariya hajiya Khadija tayi tana cewa nibari Na barku naje gurin yarinyata Naji haryanzu Bata fito ba,,Bata jira amsar Suba ta Shiga Dakin jabeer Na cewa Ke Khadija waya gayamiki ana Shiga turakar masoya kai tsaye..

Duka mashkur yakaimasa Yana cewa’ kaidai wallahi bakaji Naga alama tsokana ta kawai kake.

Niba tsokana nayi ba gaskiya ne kawai bakaso’ eh Naji cewan Mashkur ya Tashi ya kunna TV..

Sosai nijlah Ke kuka tana birgima kan gadon Har tazo daidai bakin bed zata fado hajiya Khadija tayi saurin tare ta ta fada Kan hannunta’ tureta nijlah ta shigayi tana cewa’ 

Ni Dai ka sakeni banaso kaida kayimin fada Allah barina dakai.

Toba Shi bane nice’ hajiya Khadija ta fada tana murmushi.

Ahankali nijlah ta Bude Ido tana kallanta’ Daga Mata kai Khadija tayi tana cewa’ nijlah Ko bakisan aunty?

A hankali nijlah tace’ inaso.

To indai kinaso saikin Dena wannan kukan Ko bakisan Idan mutum yayi aure hankali yake ba?

Turo baki nijlah tayi taqi magana, Khadija Bata damuba ta shigaba da Magana.

Idan kinasan Zama Dani Saina daukeki Na kaiki gidana ki muyi zamanmu acan Ko?

Ni uhmn uhmn’ dasauri Khadija tace au bazaki Bini ba?

Dena kukan nijlah tayi ta Bude baki a hankali tace’ Ni a gurin honey Zan zauna.

Zaro Ido Khadija tayi tace ho… Me?lallai mashkur wato soyayya take koyamata tinkafin ta waye Kenan.

Sai kuma tayi dariya tace’ Koda kinbini Shima Ze Riga zuwa ganinki kullum.

Cike da yarinta nijlah tace nidai bazan Koma can ba.

Shikenan saiki Koma gidan mummy Danni Bazan zauna dake kinamin rashin kunyaba sukaji mashkur ya fada Yana shigowa cikin Dakin..

Kallan nijlah Khadija tayi tana cewa au wai Dama Har rashin kunya take ma?

Gatanan ki tambayeta’ Ina Magana tana mayarmin saikace sa’ata.

Qasa nijlah ta sauke kanta tana bashi hakuri.

Bazan hakura ba saikin bita Idan Kuma kinqi to.

Tinani nijlah ta fara tana hango Zaman da zatayi awani guri,, ta Sani tinda tazo birni Bata taba haduwa da macen data tausaya Mata ba Daga masu zaginta Sai me dukanta Dan haka tasa a Ranta bazatabi kowa ba qafanta qafan mashkur sedai Idan yagaji da Zama da ita ya maidata ruga..

A hankali Khadija ta matso kusa da nijlah tana murmushi ta Dafa ta,, nijlah kinyi shiru,,Zaki Bini Ko?

Girgiza kai nijlah tayi tare da janye jikinta ana Khadija ta rarrafa ta Koma Bayan mashkur ta rungume.

Kallansu Khadija tayi tana cewa’ Duk yadda akayi kasaba mammatse ta shiyasa batasan rabuwa dakai..

Kasa Magana mashkur yayi Saima janye nijlah ya shigayi Yana San yimata wayo…

Kai typing wahala,,kuyi hakuri da wannan nagaji..

Kuriqa sharing

*Momn sultan ce*✍✍✍

???????? *’YAR SADAKA..*????????

*STORY & WRITING BY…*

         *BY*

*MOMN SULTAN*

*DEDICATED TO…..*

*MMN AMATULLAH*

*SPECIAL GIFT TO…*

*ALL MY FAN’S….*

6⃣2⃣&6⃣3⃣

Qara riqeshi tayi ta sakar masa kuka me karfi tana girgiza Masa kai’ mashkur be Iya Magana ba Saima qara janyeta dayake a jikinsa,,aunty Khadija Ko rungume hannunta tayi a qirji tana kallan Ikon Allah,,sosai salon nasu ke burgeta Duk da ba Wani Abu ta gani ba..

A hankali mashkur ya Bude baki Yana mata Magana ‘

Nijlah bazan Miki Dole ba, sabida Na daukarwa kaina alqawarin baki farin ciki,,Amma zanso ki yarda kibi hajiya Khadija ta Hane kadai zamu Samu farin ciki a Zaman mu, Sai ya sunkuya ya Kuma janyota jikinshi,,wallahi nijlah Ina tausayama rayuwarki shiyasa kikaga Ina jure Duk Wani wahala naki, sedai Kash nijlah bakya ganin Duk abinda nake sabida ke.

Cikin kuka nijlah tace’ Dan Allah kayi hakuri Allah Ina gani, nasani kana qoqari dani,Kuma Na tabbata Bayan kaka da malam Babu Wanda Ze juri dawainiyata Sai kai,,kayi hakuri ka zauna Dani Allah Bazan qara ba.

Bawai zamane banasanyi dake ba,, nijlah Ni kaina a dole Zan rabu dake na kwana biyu,,ki kwantar da hankalinki ki bita nasan zakiji dadin Hakan a gaba.

Turo baki nijlah tayi ta matsa Daga kusa dashi tana kunkuni, gaba dayansu suka zuba Mata ido Suna mamaki.

Dakyar aunty Khadija ta Bude baki a hankali tana kiran sunanta’ nijlah nijlah zokiji kinji ‘yar kanwata.

Maqale kafada nijlah tayi tare da rumgume jikin kofa, fuskanta a shagwabe.

Khadija Bata damu da Hakan ba ta Tashi tsaye ta nufi inda nijlah take’ Ai nijlah Na ganin zuwan aunty Khadija ta tafi da gudu ta Boye Bayan mashkur tana kuka,, ture ta mashkur yayi Yana cewa’ 

Kedai kin cika tsoro Amma Idan tsiwa zakiyi Ai kin iya’ Ni matsa Daga jikina yafada Yana qara tureta’

Wayyo Allah nah’ Dan Allah kayi hakuri Allah dukana zatayi nijlah ta fada tana sakin kuka tare da Kiran kaka.

Murmushi aunty Khadija tayi tana cewa’ kaga mashkur ka bita a hankali ni Sai yanzu nagane abinda yasa batasan Zama dani’ 

Hmmm hajiya Khadija Kenan me Kika gano’ Bata da Wani uzuri rigimane kawai.

Bafa haka bane mashkur’ kaifa ka kaita inda aka taba lafiyan jikinta kaga yanzu ma Dole zatayi tinanin dukanta zanyi’ bakaga tinda Na shigo Dakin take guje guje ba?

Murmushi yayi ya Maida kallansa ga nijlah Yana cewa’ amarya Wai hakane?

Nijlah Bata amsashiba Saima murguda masa baki day tayi.

Dariya hajiya Khadija tayi ta Bude kofa tana fita adakin tare da cewa’ Idan ka lallabata saika kirani mu tafi Dan Yau qafana qafanki’ Amma fa bance kayimata Wani Abu ba.

Dariya mashkur yayi Shima yabi Bayan Khadija’ a falon suka taran da jabeer bacci yafara daukanshi’ Duka mashkur yakai masa Yana cewa kai Dai wannan Ko kasa haka ta ganka ta kyale.

Nan suka nemi guri suka zauna sedai mashkur be Iya Magana ba sabida Kunya aunty Khadija daya lullubeshi.

Jabeer ne ya Bude baki cikin Maye irin masu Jin bacci yace’ 

Harta gama shiryawa Ko?

Dariya hajiya Khadija tayi tana cewa’ inafa yarinya Dai tace Bata zuwa mijinta Kuma ya zuba Mata Ido Sai Wani lallabata yake, shida Ze zare Mata Ido ta yadda zata amince da tafiyan..

Dasauri mashkur yace’ kai hajiya bafa laifina bane’ kina kallo ita taqi yadda.

Tashi jabeer yayi Yana cewa to ai shikenan Ni Bari naje Na fito da ita tinda ana San ayimata Gata tana Qi ita ‘yar shagwaba Ko.

Tare sa mashkur yayi Yana dariya’ kaga abokina waya Saka,ka barni da kayata ninasan ta inda Zan bullo Mata,,Zaka Wani Tashi da karfinka..

Dariya jabeer yayi Yana cewa’ kingani Ko Khadija wallahi Shima bayasan rabuwa da ita,shiyasa nayi haka sabida Na gane abinda yake nufi.

Ita Dai Khadija Bata Iya Magana ba Sai dariya da take tana addu’a Allah yasa nijlah ta amince su tafi Dan kallo daya tayima yarinyar Taji ta Shiga ranta.

To Dan sa Ido Naji’ Amma yanzu bazaku tafi da itaba Dan gaskiya Idan Kika dauketa a haka Ni kaina Bazan Samu nutsuwa ba,,sabida nasan rigima zata tayi acan.

Zaro Ido Khadija tayi tana cewa’ to ranka ya Dade Dama Naga lokaci yaja’ Amma Dan Allah karka Bari a wuce gobe Ko jibi Dan gaskiya banasan ayi daurin aurenka ban dauke nijlah ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button