YAR SADAKA 1-END

YAR SADAKA Page 31 to 40

Firgigit ta Farka tana salati.

Haba yakumbo sai yaushe zaki dena mafarkin nijlah idan ban mantaba tinda nijlah ta tafi saikinyi mafarkinta’ mafarkin dare be ishekiba saikin hada Dana Rana?

Numfashi Kaka ta safke tana cewa’ kayya malam’ wallahi hankalina yakasa kwanciya’ gani nake kama munyi gangancin bashi yarinyar nan ya tafi da ita’

Babu wani Kaka Insha Allah nijlah na cikin kwanciyar hankali.

Hakane Amma gaskiya wannan mafarkin danayi na yanzu ya firgitani’ nidai kawai kaje kayimana sadaka ko hankalina ze kwanta.

Yakumbo sadaka kuma’ Nima dazan Samu me Bani wallahi so nake’ nan yafara zaro aljihun wandansa Yana cewa’ duba nan ki gani’ wallahi Banda naira Goma nan Bani da ko biyar..

Malam kaje ko kuli kuli Ka siyama yara inyaso saika rarrabashi kanana Ka bayar na tabbata Allah ze dubi marainiya da idan rahama koma a wanne Hali take taji dadi’

Idan kuma ba haka ba nizan tafi Gona ko kanya na debo sainayi sadakanta Kaka ta fada tana qoqarin tashi tsaye..

Riqeta malam yayi Yana cewa keda Baki da cikakkiyar lafiya ina zakije’ ki zauna kawai ninasan abinda zanyi..

Hawaye Kaka ta share tana cewa’ malam Ka taimaka ninasan abinda nagani a cikin mafarkina’ sai kuma ta daga hannu tana addu’a..

Yawan comments yawan typing

Pls share.

*Momn sultan ce*✍✍✍

???????? *’YAR SADAKA..*????????

*STORY & WRITING …*

         *BY*

*MOMN SULTAN*

*DEDICATED TO…..*

*MMN AMATULLAH*

*SPECIAL GIFT TO…*

*QUEEN MARYAM….*

7⃣0⃣&7⃣1⃣

Addu’a sosai yakumbo ta riqa yima nijlah tana qara tuba ga Allah Dan ita gani take kama laifinsune da suka kasa bata farin ciki gashi yanzu ta tafi ta barsu,,Basu San halin da take ciki’ 

Fita malam yayi ya sai kuli na naira goman data rage cikin aljihunsa ya raba yara’ abinka da rugan kauye nan da nan yara suka zagayeshi sedai befi mutum goma suka samu ba sauran sai hakura wasu suka koma gida suna kuka..

Dakin Nasir malam ya wuce acan ya sameshi’ bayan sun gaisa ya Shiga yimasa tambayoyi kama yadda ya saba’ a koda yaushe’

 Nasir nidai hankalina yaqi kwanciya dan haka nakeso Ka shirya muje can birni Naga marainiya’

Gaban Nasir ne ya yanke ya badi Amma Saiya dake Yana cewa’ ah ah malam kayi hakuri Dan ko jiya munyi waya da mashkur harya hadani da nijlah mun gaisa,, kaga tamace a gaisheku kuma nan da ‘yan kwanaki zasu kawo muku ziyara.

Washe Baki malam yayi Yana cewa Kai alhamdulillah naji dadin wannan labarin’ Bari na koma gida da sauri na Sami yakumbo itama nasan zatayi farin ciki ba kadan ba’

Sosai ma kuwa Nasir yafada Yana Allah Allah malam ya tafi Dan Shima zuwa yanzu yafara tsorata da lamarin mashkur gashi lokacin tafiyansa gida yayi Yana tsoran cewa zeje Kaka tace bata yadda ba..

Har malam yayi nisa ya juyo Yana magana’ Kaga Nasir duk da haka kayi qoqari idan mashkur din ya Kira saika kirani mu gaisa’ 

To malam zakajini in Allah ya yarda.

Malam na tafiya Nasir ya dafe Kai Yana cewa’Kai gaskiya na hada kaina da aiki’ ni dai fatana daya’ Allah yasa mashkur ya riqe Amana’ 

Tashi yayi ya tafi inda suke waya ya Kira layin mashkur sedai Yana ringing ba’a dauka ba,,gajiya Nasir yayi ya dawo gida ranshi babu dadi..

Sosai matashiyar matar ke gudu akan titi’ kafin ta qarasa hospital harta Kira babban likitansu’ nan ta sanar masa tana da mara lafiya gatanan zuwa asibitin.

Tuni babban likitan yafara hada manyan likitocin dake asibitin yana sanar musu nan suka tsaya zaman jiran qarasowarsu,,yayinda nurses suka qarasa bakin get dauke da gadon tura mara lafiya.

A guje motar ta qaraso cikin asibitin’ matashiyar duk ta hada zufa ta gigice,,hankalinta a tashe, hadda ita suka fara qoqarin fito da nijlah a cikin mota, Kan gadon marasa lafiya aka dorata’ likitoci da Kansu suka Shiga tura gadon da gudu aka Shiga da ita dakin duba marasa lafiya.

Nan take likitoci suka Shiga dubata tare da bata taimakon gaggawa’ Basu jimaba suka samu nasaran dawo da numfashinta daidai’

Da kuka nijlah tafara tana Kiran Kaka tare da birgima akan gadon tana niyyan faduwa qasa’

Daya daga cikin likitocin ya leqa waje Yana cewa’

Bismillah husna zaki iya shigowa’ 

Cike da rawan jiki matashiyar matar da aka Kira da husna ta Shiga tana yiwa Dr godiya’

Kan gadon da nijlah ke kwance ta qarasa tana yimata sannu’ kallanta kawai nijlah keyi sedai zuwa yanzu ta dena kuka Dan ba wani ciwo taji ba illah tsorata da tayi ganin yadda napep din yayi kanta..

Hannu husna tasa da niyyan taba nijlah’ dasauri nijlah ta janye tana turo baki’ tare da cewa ni ah ah.

Murmushi husna tayi Wanda ya bayyanar da kyawun fuskanta tana magana cike da tausasawa kiyi hakuri yarinya nice na kawoki nan bayan hadarin da kika samu’ sunana husna.

Fita likitocin sukayi suka bar dakin husna na qoqarin Jan nijlah da jikinta’

Kanwata ki gayamin sunanki Saina Kira gidanku Azo a tafi dake?

A hankali nijlah ta bude baki tace’ sunana nijlah,, sedai Bani da kowa inda nake basa Sona kullum Duka na suke suna zagina’ saita sauko qasa tana kuka ta kuma riqe qafan husna’

Aunty Dan Allah ki tafi Dani ki kaini gurin kaka’ zasu kasheni..

Tinda nijlah tafara magana husna ta lumshe ido tana mejin tausan nijlah duk da batasan wacece itaba’ hannu tasa ta janyo nijlah jikinta tasa hannu biyu ta rungumeta tana shafa bayanta’

Kiyi hakuri kinji nijlah Insha Allahu Zan Kula dake har zuwa lokacin dazan hadaki da iyayenki..

Aunty Bani da iyaye ance sun mutu’ indai ba lahira zaki kaini ba’ dariya husna tayi tace ah ah Niba lahira Zan Kai ‘yar kanwataba,itama nijlah murmushi tayi tana boye fuska tare da goge hawayenta..

Hannu husna tasa ta riqa goge Mata tana cewa’kidena kuka’ Insha Allahu kukanki ya qare kinji kanwata.

Wani irin murmushi nijlah tayi tana kallan husna tace’aunty dagaske’ dagamata Kai husna tayi Dan ita ba qaramin dadi taji na haduwa da nijlah’ koba komai Zata Debe Mata kewa kafin ta kaita gidan iyayenta..

Suna cikin haka nurse tazo yiwa nijlah allura’ nan fa nijlah taqi tsayawa Saida husna ta bude jakanta ta dauko wasu chocolate ta riqe a hannunta tana cewa’ ki tsaya ayimiki Saina Baki wannan.

Duk da nijlah batasan menene ciki ba Amma haka ta qanqame husna aka yimata alluran’ sallama aka Basu suka tattara suka tafi gida…

Tin kafin ta qarasa wayanta ya fara ringing’ dauka husna tayi ta Kara a kunne’ daga daya bangaren aka fara magana’

Aunty wai ina kika Shiga kinje kinyi zamanki’ kinbar Dan qaninki da yinwa ya qare maganar a shagwabe’

Dariya husna tayi tana cewa’ tome zanmaka ko Kai jaririne’ haka kawai mijina be takurani ba sai kai’ tuzuru da Kai kawai husna ta qare maganar cikin Wasa da tsokala..

Kukan karya yasa Mata itako ta riqa dariya tana cewa kaga mujaheed gani nan zuwa ina hanya ‘ dariya yayi Yana cewa shine kike tsokala na’ na dai gayamiki aure lokacine muna nan dake watarana zaki nemi ganina ki rasa’

Allah ko Baba na soro’ kinga nidai saikin dawo Bari naje dakin yaya Shima ya dawo tin dazu muna jiranki’ 

To ai gani nan sai hankalinku ya kwanta.

Tinda husna tafara waya nijlah ta zuba Mata Ido tana Jin kaunar matar na qara Shiga cikin zuciyanta duba da yadda take waya cikin sakin fuska da nuna kauna da Wanda take wayar..

Safke Ido husna tayi taga yadda nijlah ta tsare ta da ido’ dariya tayi tana cewa’ lafiya dai ko kanwata?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button