YAR SADAKA 1-END

YAR SADAKA Page 31 to 40

Dariya nijlah tayi tace’ Kai yayanane fa aunty sedai Baya Sona Yana dukana kingama irin ciwon.

Ah ah basai nagani ba’ au yanzu Duka ya qare tinda Saiya ganki ze dakeki ko’

Eh, nijlah tace tana kallan husna sai kuma ta sunkuya har qasa tana gaisheda daddyn Ayman kasan cewar Basu hadu ba tinda tazo gidan.

Amsawa yayi Yana cewa zoki zauna kici abinci’ ga wani yayan kinsamu’ na tabbata Shi baze dakeki ba kinji yar albarka.

Cike dajin dadi nijlah ta zauna tana cewa’ ni a Baki zaka Bani so dai Kado ma a Baki yake bani’.

Sabida Jin dadi mujaheed kasa rufe Baki yayi haka ya fara bata abincin tana ci tana lumshe ido.

________________

Da mugun gudu daddy ya qarasa hospital manyan likitoci suka amsa mashkur suna qoqarin Dan ganin jinin dake zuba a bakinsa da hancinsa ya tsaya’ sun Jima suna fama kafin suyi nasaran tsai da jinin.

Nan suka dawo Kan numfashinsa suna Danna qirjinsa a hankali har Saida ya ja numfashi’

A firgice mashkur ya Farka Yana cewa’tana ina daddy anganta, nijlah Dan Allah ki dawo gareni.

Wallahi mutuwa zanyi sai kuma yafara salati tare da waiwayen inda yake,, be damu da inda ya Gansaba yafara qoqarin fizge ruwan dake daure a hannunsa Yana surutai kamar na masu hauka irin saban kamun nan.

Daddy dake tsaye a kofa ya shigo da gudu Yana bashi hakuri’

Hayi hakuri mashkur za’a ganta kaji?

Cike da zafin ciwo gami da tashin hankali mashkur yace’

Sai yaushe daddy ni wallahi a yau nakesan ganinta’ daddy inasan nijlah ta Zama jinin jikina bazan iya qara awa guda batare da ita ba daddy Ka taimaki rayuwana..

Comment & share

Share this

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button