YAR SADAKA 1-END

YAR SADAKA Page 31 to 40

Banda kuka Babu abinda nijlah take tana ba mummy hakuri Dan ba qaramin zafi rankwashin yake Mata.

Sai da mummy ta gashi Dan Kanta kafin ta kyale nijlah ta Shiga ciki..

Kusa da motan nijlah ta kwanta tana birgima tana ihu( ah lallai Yau Nijlah an tuna ruga lolxx)

Mummy Na Shiga falon wayanta ya fara ringing tana dauka Linda take gayamata sun qaraso Aida sauri mummy ta katse Kiran ta amsa Na Mai Gadi sabida ya hanasu Shiga ciki yace yanzu Bakar fatama tsoranta akeji balle farare wadannan ba Yan qasa ba.

Mummy Na dauka get man yace’ hajiya wasu masu corona ne suka zo sukesan shigowa gidan Dan gaskiya Ni Ko tsayawa sauraransu banyiba Na gudu cikin lambu’

Kai dallah gafara can shashasha angayama Koma keda corona zaka dakatar dasu to wallahi ka Bude kafin kayi a bakin aikinka’ Linda ce Baka Sani ba ko yaya?

Ah hajiya Dama Linda ce Ai ban Sani ba sabida Ni Ina ganin Jan kunne na tafi ta gudu Na boye kinsan….cikin tsawa mummy tace ka Bude musu ba shegen surutu Na tambaya ba..

Nan get man ya bude suka fara shigowa.

Nijlah dake kwance tana kuka ta dago kai’ Aiko tayi arba da masu jajayen kunnuwa saita Tashi tsaye tana ihu tana neman dauki’

Wayyo Allah Na baba ta kawoni lahira Allah Na tuba wayyo dodanni ,,nayi gamo da aljanu’ nijlah ta fada tana nuna su Linda da abokanka da suka tsaya sukayi cirko cirko Suna kallan Nijlah..

Ganin yadda suke qara tahowa inda suke yasa Nijlah Tashi da gudu tayi cikin falon tana cewa mummy, mummy fito ki gani wadannan abebadan da Ake gani cikin kayan kallo sune suka fasa suka shigo Dan tinda nijlah ta tashi zaune taga inda take ta tabbata ba a lahira take ba a Duniya ne nan ta Tina a inda ta taba ganinsu….

Da gudu mummy ta fito tana gyara daurin dankwalinta yayinda Maryam me aiki Ke biye 

da ita a Baya..

Ai Suna zuwa daidai dining kujera ta harde qafan mummy tayi taga taga saiji kake timmmmmm mummy ta wintsila ta fadi kasa dagwash……..

Comments & Share.

*Momn sultan ce*✍✍✍

???????? *’YAR SADAKA..*????????

*STORY & WRITING …*

         *BY*

*MOMN SULTAN*

*DEDICATED TO…..*

*MMN AMATULLAH*

*SPECIAL GIFT TO…*

*R.HUSSAIN….*

*Alhmdllh,,komai yayi farko zaiyi qarshe’ kawata mmn amatullah marubuciyar rayuwar zainab’ ina tayaki murnar kammalashi da kikayi Allah yabi ladan fadakarwa ya yafemiki laifin da kika aikata a ciki,, haqiqa labari yayi Dadi Babu abinda zamuce dake Sai godiya” Allah ya rayamana yaranmu da albarka ya qaramana Zaman lafiya da kaunar juna,, nagode sosai da karamcinki gareni’ momn sultan na Miki San so,,duk da kedin kawar hy hy ne*????????????

6⃣6⃣&6⃣7⃣

Tinda mummy ta fadi ta saki Wani qara tana cewa’ wayyo Maryam quguna shikenan Na karye wayyo Allah’ surutai ta shigayi tana kukan azaba, Maryam Ko bataji faduwan mummy ba ta fita da gudu tanasan Duba nijlah sabida Allah ya doramata San nijlah ba kadan ta,,ita shirmen yarinyar shike qara birgeta da ita.

Shiru Linda da dasauran tawaganta sukayi Suna sauraran shirme da ihun nijlah’ tin Suna daukan abin wasa Har tsoro yafara kamasu’ bashi suka cire choko chokon takalmansu suka riga kwasa da gudu Suna neman dauki,,anan suka zubda kayan hannunsa Suna rige rigen fita.

Shiko get man dadine ya ishesa Dan Dama yace a wanne dalili zasu shigo gidan Suna Ake zargi da yada wannan cuta’ sedai fitansu yanzu ba qaramin haushi abin yabashi ba Dan Yau Ko Sisi Basu bashi ba nan yaqara kulewa da kukan nijlah Wanda Dama ta ishesa hakuri kawai yayi ita kada ta sauke masa wannan dararan idon nata tana hararanshi’ 

Kallanta yayi ransa a bace yace’ Ke dallah tashi’ kin zo kinmana baqin ciki ‘mitsitsiyar yarinya dake Sai qinjin tsiya.

Turo masa baki Nijlah tayi tana murguda su sakamakon ganin yadda su Linda suka fita a guje yasata yin hamdala ta Tashi tana Kade jikinta,,daidai lokacin Maryam ta qaraso gurin tana tambayan nijlah’

Lafiya Dai nijlah waya tabaki? Bakiji ciwo ba Dai?

Goge hawaye nijlah tayi tana cewa’ eh banjiba.

Wai da me aka Miki Nijlah?

Maryam gamo nayi’ Kuma wannan mutumin da Baya aski Saina ‘yan iska shine ya Bude musu suka shigo Amma dayaga nayi addu’a Suma da gudu suka fita’ Sai kuma ta Dafa Maryam tana cewa’

Wai’ nafa auna arziqi da Basu daukeni ba.

Ke Dan ubanki ni s’ankine’ ‘yar kauyen kawai dako kwalliya baki iyaba’ gadai Kaya masu kina Sawa Amma a banza.

Murguda masa baki tayi tana cewa’ oho dai Kuma Allah ya isana daka tsoratan.. nijlah Bata gama rufe baki ba get man ya kaiwa bakin Duka Yana cewa’

Kujimin mara kunyan yarinya towai Zaman uban me kike a gidannan da Zaki zauna Harda zagina..

Abinka dame jiran kadan Ai tini nijlah tasa kuka tana birgima tare da Kiran kaka’ Maryam tayi rarrashin harta gaji’ kallan get man tayi tace’

Haba Musa meyasa Zaka biyeta’ 

Ke banasan munafunci’ Ko Ke bakiga abinda tayimin ba?

Naga ita yarinyace be kamata kayi Mata wannan Dukan ba.

Maganar ta safka kunnan mashkur dake qoqarin shigowa cikin gidan da qafafunshi Dan yayi horn harya gaji ba’a Bude get din ba,Dan haka ya fito yaga abinda Ke faruwa..

Kai tsaye gaban nijlah ya isa Yana tambayanta Ke lafiya meke faruwa dake danshi be tsammanin nijlah get man ya dakaba.

Tabe baki nijlah tayi tana nuna Musa dayayi tsuru tsuru da Ido Yana kallansu.

Cike da faduwar gaba mashkur ya Maida kallansa ga musu mai gadi’ bakinsa Na rawa yace’ meya hadaka da ita..

Dasauri Maryam tace’ haka kawai yasa hannunsa me shegen zafi ya bugeta a baki sabida kawai ta…. Ya isa mashkur ya daka Maryam tsawa Wanda tasa hankalin kowa dake gurin tashi’ Hatta ita Kanta nijlah Saida ta firgita ta zabura ta miqe tsaye tayi Kan mashkur tana qoqarin riqeshi ya tureta idonshi rufe batare dayasan waya bige ba yayi Kan Musa da zuwa yanzu yafara magana cikin tsoro da tashin hankali.

Maryam kiji tsoran Allah’ ranka ya Dade wallahi niba dukanta nayi ba rashin kunya tayimin nasa hannu Na bige b…..

Be Iya qarasawa ba yaji Wani lafiyayyan naushi a bakinsa’

Cikin Daga murya mashkur ya soma magana da zafin zuciya Dan shiyake kama ya cireta ya cillar koze huta da abinda yakeji.

Wallahi sainayi Sharia dakai matata ka doka Har kana Iya maimatawa a gabana.

Ba Musa Mai Gadi ba Hatta Maryam Saida maganar ta girgiza, a tare suka maimata maganar’

Matarkafa kace?

Fuskan mashkur a Hade kama hadari yayi Kan Musa Yana cewa’ ka Hada kayanka yanzu basai anjima ba’ Dan wallahi bazakayi kwanan farin ciki ba, ka kumayi sa’a bantaba fada Da Wani ba da tau Saina kusa kasheka..

Hannu Musa ya Dora aka Yana cewa’ wallahi ban daketaba sharri kawai Maryam tayimin’ Ke Maryam Dan iyayenki ki gayamasa Karya kike wayyo Allah Na Ni Musa Ina Zan Samu ogah kamarka me tausai dajin kai’ Na tuba ranka Shi Dade nizan Bata hakuri.

Be jira cewan mashkur ba ya rarrafa zuwa ga nijlah Yana kuka da hawaye Yana cewa’ 

Kiyi hakuri ranki ya dade Banda abinki Ai bayani ake’ Ina zanyi tunanin ogah Ze sauri wannan abun,,kiwa Allah ki ceceni.

Nijlah Bata kulashi ba Saima turo masa baki tayi tana fulatanci Wanda nikaina bansan abinda take Gaya ba..

A fusace mashkur ya fuzgo Musa Yana cewa’ kai Wai haka be ishekaba saika samin ita a gaba’ to Bari nayi maganinka saika dawo cikin Hankalinka tinda Baka dashi.

Tattare hannun Riga mashkur tashiga Yi Yana qoqarin damqar Musa mummy ta saki Wani ihu Wanda yasa suka dawo cikin Hankalinsu’ be Iya aikata abinda yayi niyyaba ya Shiga cikin falon da gudu zuciyarsa na bugawa da sauri Dan tinda yake be tabajin kukan da ihun mummy Kamar Na yanzu ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button