YAR SADAKA 1-END

YAR SADAKA Page 31 to 40

DA gudu Yasmeen tayi Kan Abba tana boyewa a bayanshi’ hannu yasa ya riqeta sosai Yana murmushi,,nan da nan Yasmeen ta shagwabe masa tana cewa ita bazataci wannan abincin ba.

Indai wannan ne Karki damu kinji ‘yar Lele, hannu Abba yasa a aljihunsa ya Ciro kudi masu yawa ya miqa mata’ kinga amsa wannan kije Duk Wani restaurant dayamiki a fadin garin nan kici Duk abinda kikeso kinji ‘yar lelen Abba.

Wani irin Dadi Yasmeen Taji Dan harga Allah abbanta Na nuna Mata kauna irin Wanda Bata taba gani ana nunama wasu ba’ rungume hannun Abba tayi tana cewa’ abbana nagode Allah yaqara Budi da wadata yarabaka da ‘yan bakin ciki.

Ameen ‘yarta Tashi kije kada yinwa ta kamamin Ke’ dariya Yasmeen tayi tana cewa Abba Nida kawayena ne gasu can ma.

Sai yanzu Abba ya Kula dasu mubeena nan suka sunkuya Har qasa Suna gaidashi,,fuska sake ya amsa Yana tambayan Basu iyayen,,wasu kudi ya Ciro ya miqa Yasmeen Yana cewa’amsa wannan Ku qara aibansan kunada yawa haka ba..

Ah ah abba kabarshi wannan ma ya isa’ kidai karba Dan bakisan dawa zaku hadu a gurin ba amsa Yasmeen tayi ta koma daki da gudu ta dauko mukullin Motan ta ta dawo tana cewa kuzo mu wuce.

Girgiza Kai mama tayi ta zuba nata abincin ta dauka tana kallan abba sedai batace komai ba ta shige daki tamejin takaicin lalata Mata yarinya dayayi’ da Ido abba ya vita Yana cewa’ hajiya yau kuma ba sannu da zuwa,kika wuceni kina harara..

Ko juyowa mama batayi ba ta,,ganin haka yasa abba bin bayanta Yace’ wai bakiji ina magana ba?

Dagowa mama tayi ranta a bace tace’ eh banji ba.

Hmmm nasan kinjini sarai’ da dai kince sarautankine ya motsa zanfi yadda.

Cike da takaici da mama ta bude baki ahankali tafara magana’ haba abban Yasmeen sai yaushe zaka dena Dora yarinyarnan a keken bera’ kafa kusa kaita dakin miji Amma bazaka dena Nuna Mata wannan gatan ba’ sai kuma ta sassauta murya tana cigaba da mama’ wallahi ina tsoran auran da Yasmeen sabida babu namijin daze iya Nuna Mata gatan dakake bata Dan wannan ya wuci gata sai dai barna.

A kul bakinki ya qara furta irin wannan maganar’ wai shin saunawa Zan gayamiki kidena samana Ido’ kodan ke Baki tashi cikin irin wannan gatan ba’,,shiyasa kikesan yiwa yarinya baqin ciki?

Dafe qirji mama tayi tana kallan abba,,bakinta na rawa tace’bakin ciki fa kace?

Eh shine mana’ aiban ganekiba sai yanzu dazan auran da ‘yar Lele Naga har wani qiba kika qara sabida farin Zata tafi tabar Miki gidan ko?

Wasu hawaye masu zafi suka fara bin quncinta nan tasa hannu ta gogesu’ bata qara cewa komai ba ta fita tabar masa dakin’ yinin ranar ki abinci mama bata iya ciba…

Dr na dauka mashkur ya gayamasa abinda ke faruwa’ nan da nan Dr Ahmad ya harhada takaddun gabansa ya da fita da sauri ya nufi gidan mummy’ da zuwansa yafara dubata,,ya Jima Yana ‘yan gwaje gwajensa kafin ya dago Kai Yana kallan mashkur’

Dr lafiya dai Naga kana kallona’ Dan Allah Kada kace da matsala’ gyara zaman glass dinsa yayi Yana cewa’ba wani matsala’ bane sedai mummy ta Samu buguwa sosai shiyasa takasa takawa Amma nan da hour daya Zata iya Jin daidai.

Ajiyar zuciya mummy ta safke daga ita har mashkur suna godema Allah dayasa bata qarye ko taji ciwo me yawa ba’ tashi Dr Ahmad yayi Yana cewa’abokina nizan wuce sabida nabar patients suna jirana.

Tashi mashkur yayi Yana masa godiya ya rakashi har jikin mota’ anan ne Dr Ahmad yake cewa kaga na manta da Allah ayimata ruwan dumi yanzu sabida taji dadin gurin.

Yanzu ki zansa ayimata Dana Shiga ciki’ dariya Dr Ahmad yayi Yana cewa’

Mijin kwaila angon Yasmeen ina Ka boye nijlah bangantaba?

Rasa Rasa gaban mashkur ya Fadi sedai ya danne Yana cewa’ Kai niwai narasa meyasa kuka samin ido’ to indai nijlah ce babu me sake ganemin ita.

Dariya Ahmad yayi Yana cewa ango ango nan ya tada mota ya tafi mashkur na daga masa hannu.

Dr Ahmad na tafiya mashkur yafara zagaye gida Yana Neman nijlah,sedai duk inda ya duba be gantaba hankalinsa yafara tashi’ nan yafara kwala Mata kiran..

Nijlah nijlah nijlah’ ya Kira sunanta yafi sau burin masaqi ganin bata amsaba yayi tinanin ko bacci tayi tana wannan rigiman nata..

Nan ya yaci gaba da nemanta sedai duk inda yakesa ran zeganta ya duba bata nan’ dasauri ya dawo bakin get Yana cewa’

Malam Musa Kai malam musa’ da gudu malam musa’ ya fito Yana karkarwa yace

ranka ya Dade gani’ 

Dan Allah Dan annabi kayimin Rai Kada Ka koreni daga wannan gidan’ wallahi bazan qaraba’

Kai malam musa’ niba wannan ba’ Baka ga wannan yarinya ba?

Ranka ya Dade wacce yarinya?

Cikin fada mashkur yace’ waiya ina tambayanka kana dawomin da tambayana’

Nijlah nake nufi tana ina mashkur yafada cikin tashin hankali.

Bakin Musa na rawa yace’ ranka ya Dade ai tinda kuka Shiga ciki Naga ta fito da gudu ta fita wace.

What! 

    What,, me kakesan gayamin’ kana nufin nijlah ta fita?

Eh ranka ya Dade ai tafi hour da fita a gidan nan.

Hannu mashkur ya Dora akai Yana cewa’shikenan malam musa’ Ka kasheni’

Wata wawar chakuma mashkur yakaiwa Musa hankalinsa a tashi ya matse masa wuya Yana haqi Yana cewa’ wallahi saika nemomin matata nan da nan tari ya tirniqe mashkur Amma duk da haka be saki Musa me gadi ba..

Tin Musa na qoqarin kwatar kanshi harya kasa yafara kakari Yana riqe da hannun mashkur.

Jin ihun yayi yawa yasa masu aikin ban ruwan fulawa suka fito da gudu suna kallan tashin hankalin dake faruwa’

Sunyi iya Kar qoqarin su akan suga sun kwaci musa a hannun mashkur sun kasa hakan yasa suka Shiga ciki da gudu suna Kiran mummy’ 

Mummy dake zaune ta kasa tashi’ taji hayaniya yayi yawa a kofan falon’ nan ta Kira Maryam tana cewa’ Maryam jeki duba kiga abinda ke faruwa’ nasan koma menene baze wuci wannan aljanar ta hadashiba.

Dasauri Maryam ta fita itama sai gata ta dawo tana cewa mummy mashkur, mashkur ne zeyi kisa.

Ai mummy mantawa dayi da ciwan kafanta sai gata ta tashi tana dingisawa tare da bin bango ta fito tana salati, daidai lokacin daddy yayi horn, Maryam ce ta iya budema daddy Aida gudu daddy yayi Kan mashkur Yana cewa.

Kai mashkur Baka da hankali Meka sha’ Ka sakeshi nace saika kashesa?

Sabida zuwa yanzu Musa yagama galabaita harshensa harya zazzago sabida azaba.

Mashkur be iya magana ba sabida yadda yake jinsa,,haka majiya karfi suka taru suka banbare mashkur a jikin musa’ nan take Musa ya zube qasa sumamme..

Lafiyayyun Mari daddy ya safkewa mashkur Yana cewa’Baka da hankali kisan Kai zakayi kome’ mashkur be damu da Marin daya Shaba Saima qoqarin kwato Musa yake daga hannun jama’a Yana cewa.

Karku fita dashi wallahi Saiya dawomin da matata,, ganin abun na mashkur ya wuci qima daddy yafara tofa masa adduoi.

Banda kuka babu abinda mummy take gashi an tambaya mashkur abinda ya hadashi da Musa yaqi fada ko ince yakasa magana’ matata kawai yake kira,, ganin babu alamun nijlah yasa mashkur fasa wani irin ihu ya zube a qasa..

Nan da nan jini yafara bin hancinsa sabida ya riqa ya sallamawa samun farin ciki yakuma San nijlah bazata iya dawowa da qafantaba….

Cike da tashin hankali daddy yasa mashkur a mota ya tashi hospital dashi’ nan mummy ta zauna tana tsinewa nijlah.

_____________

Cikin bacci yakumbo tafara surutai tana Kiran nijlah tare da shiru Shure da qafanta’

A hankali malam yafara tashin ta ta hanyar taba hannunta Yana cewa’ yakumbo, yakumbo.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button