YAR SADAKA 1-END

YAR SADAKA Page 31 to 40

Cike dasan Jin abinda ze fada husna ta matsoshi tana cewa’ hubby na kayi Shiru’ 

Dan Allah kace wani Abu ta fada tana marairacewa..

Kallanta yayi Sama da qasa kafin ya bude baki a hankali Yace’ dear nifa na Riga na Gama magana sabida kinsan kowane mujaheed a gurina’ husna kinsani Bani da kowa sai shi,,shekara 41 kenan da haihuwan mujaheed Amma be taba ganin wata Diya mace yace Yana Soba,, Mata masu aji da gayu sun kawo Kansu Amma yarannan yaqi amsar tayinsu,,nayi maganin a tinanina ko aljanace ta auresa ance lafiyansa qalau.

Husna mun zauna da mujaheed akan wannan maganar yafi sau burin masaqi Amma ya tsaya ya kafe Kai da fata yace Shi bega wacce tayi masa bane,, sai gashi yau Allah ya kawo mana Mata Hari gida yace yanaso kike neman bata abun,,haba husna meyasa zakimin haka..

Nan nauyan ajiyar zuciya husna ta safke,, babu shakka ta San duk abinda mijinta ya fada daidaine ba qarya a cikinsa’ sedai tana tsoran halin da iyayen nijlah zasu Shiga idan har basu gantaba.

Kallanshi tayi da idanunta da suka qanqance tana cewa’ haba mijina kaifa ubane yaya zakaji idan Ayman ya bata wasu suka boye mana Shi sabida wani burinsu da suke San cikawa.

Hubby na sani dole zamuyi farin ciki da samun yarinyar da mujaheed ya gani Yana so,,kusan ince nina fika Jin dadin haka sabida nice silar zuwan nijlah gidanan sedai inaso kayi hakuri mu kaita GA iyayenta idan yaso daga Baya sai mu kawo bugatarmu..

Cike da fada daddyn Ayman yace’ hakan bazata taba yiwuwa ba husna kinsani munada dukiya Wanda mu kanmu bamusan adadin taba,, muna da kyau sabida mu din jinin fulani ne, na asali,,uwa uba kyan Hali Wanda zeyi wahala kisamu bufulatani mutum baida wannan sedai yanzu da duniyar ta Zama abinda ta Zama ko ince mutanan dake cikinta,, Amma duk da wannan abubuwan dana lissafa miki ace kanina ya Rasa matar aure Wanda idan Siya Ake zamu iya kashe silalla mu siyeta..

Ganin yadda ya dauka zafi dayawa yasa husna sansauta murya tana cewa’ kayi hakuri indai nijlah ce Nima na amince ta zauna tare damu har sai lokacin daka buqaci iyayenta su ganta” kayi hakuri da sa’insar danayi da Kai kasan ba halina bane..

Sansanyar ajiyar zuciya daddy Ayman ya safke yana rungume husna tare da bata hot kissing a kumatunta Yana cewa’ shiyasa nake qara sanki matata,,kedin ‘yar aljannace..

Murmushi tayi tana cewa’ kaima Dan aljannane mijina’ inajin dadin wannan sunan ta fada tana shafa qirjinsa’

A tare suka saki nishin dadi Wanda yasa dukaninsu Shiga cikin wani yanayi Mai wuyar fassara’ qoqarin zuge zip din rigarta yake tayi saurin riqe hannunshi tana cewa’

Kayi hakuri zuwa anjima koka manta inada mara lafiya kuma suruka a gidannan ga kuma kanina najin yinwa kama yayi mu Basu kulawa sai nazo kayi yadda kakeso’

Cike da kasala yace’Allah dear.

Cike da salon Jan hankali husna ta kashe masa ido tare da cewa ai nakane kayi yadda kakeso..

Murmushi yayi ya kama hannunta suka fito a tare suna magana a hankali..

A falo suka tsaya suna kallan mujaheed,,yayi tsaye jikin window dakin da nijlah ke kwance Yana leqawa,, 

Duk da ba ganinta yake ba hakan Bai hanasa Jin dadin ganin ta cikin bargo ba Dan bata Saba da AC me yawa cikin dakin ba, gashi husna bata rage gudun ac ba..

Daddy Ayman ne ya qarasa jikin window Yana murmushi yasa hannu ya janyoshi jikinsa Yana cewa’kayi hakuri kanina indai nijlah ce ta Riga ta Zama taka,, nayima alqawarin auren ta koda Duka dukiyana da qarfina zai qare akanta..

Wani irin daddy mujaheed yaji Wanda yakasa boyesa har Saida ya rungume Shi Yana kukan farin ciki’ 

Cikin kuka yafara magana’nagode sosai yayana haqiqa Kai din Dan uwane na kwarai,, yaya ni kaina nayi tinanin Bani da lafiya sai gashi yau Naga Wanda ta dace da rayuwata..

Yaya Dan Allah Ka ceceni Ka cece rayuwana na Auri nijlah,,idan na rasata Nima zaku rasani…

Husna dake tsaye ta kasa qarasowa inda suke taji kalaman mujaheed na niyyar tarwatsara farin cikin mijinta ta tako a Hankali ta qaraso inda suke tsaye.

Haka nan taji mugun tausayinsu ya qara kamata da kyar ta iya bude baki tace’

To baban ‘ Yan soyayya Shifa Dana Wanda be sababa idan ya tashi yi yafi kowa,husna ta fada cikin Wasa..

Share hawayen fuskansa mujaheed yayi Yana cewa’aunty na Kenan,, ninasan bazaki taba ganewa ba.

Dariya suka da gaba dayansu,husna tace to ai saikace muci abinci tinda bazan gane ba, ko itama yinwan Ka daina ji??

Sosa Kai mujaheed yayi hannunsa riqe Dana daddyn Ayman Yana cewa’ 

Dan uwana kanajin matarka ko?

Murmushi Jin dadi yayi yace’ Toni ina ruwana’ Koso kake na Shiga Ku zo kuna kunyatani…

Dariya suka qarayi suka nufi dinning table,, bayan sun zanzauna husna’ta zuba mujaheed nasa yayinda ta zuba musu nasu ita da mijinta kamar yadda ta Saba..

Shi dinma kamar kullum tashi yayi ya dauka nasa plate din Yana cewa’Nima dai bakusa angon cewa Adena wannan abun a gabana..

Falo ya dawo ya zauna da niyyar cin abincin seda ya zauna yaga baze iya ciba, alhalin nijlah na kwance ita bata ci ba..

Sosai husna da hubbynta sukayi nisa gurin cin Basu abincin’ sedai duk yadda husna ke qoqarin dauke masa hankali abun yaqi yiwuwa Dan Rabin hankali Naga abincin rabi nakan mujaheed daya riqe cokali Yana juyawa yakasa Kai koda cokali guda cikin bakinsa.

Kallan inda yake kallo husna tayi itama idonta ya sauka Kan abincin da mujaheed ke Wasa dashi,,kallo daya zaka masa Ka gane a cikin tinani yake..

Tsam daddyn Ayman ya tashi Dan Shima bayajin ze iya cin abincin Dan uwansa na cikin damuwa.

Kusa dashi yaje ya zauna Yana Kiran sunansa’ a hankali’

Mujaheed’ Mujaheed?

A firgice mujaheed ya juyo Yana kallan yayan nasa a hankali ya janye nasa idon Dan bayaso yanasa Dan uwansa cikin damuwa..

Mujaheed lafiya Ka zuba abinci Ido kana dogon tunani’ ina akan maganar wannan yarinyar ne ai mungama ko?

A hankali mujaheed yace’eh yaya.

To menene kuma’ Naga sai Wasa kake da cokalin hannunka?

Murmushi mujaheed yayi fuskanta cike da kunya ya bude baki Yana cewa’ 

Yaya Naga kowa sai cin abinci yake Amma ita ba’a bata ba..

Ita wa daddyn Ayman ya tambaya?

Akunyace mujaheed yace nijlah yaya tana daki babu Wanda yasake dubata tinfa dazu’ ya qare maganar a shagwabe.

Dariya husna tayi batace komai ba ta tashi ta Shiga dakin nijlah.

Kwance ta ganta sedai idonta bude yake ta zuba guri daya Ido tana kallo..

Ah ah kanwata kin tashi shine Baki sanar Dani ba’

A hankali nijlah tace’eh aunty na tashi baccin ne yayi Fadi shiyasa Dana tashi nakesan komawa’

Ki koma ina’ Maza tashi muje kici abinci kafin kiyi wanka.

Ba musu nijlah ta tashi suka fito a tare’ mujaheed naganin fitowansu yayi saurin taran husna yace’

Aunty ki kawomin ita nan sai muci tare ita tana ba Ayman kinganshi Shima ya tashi?

Husna taso qin yadda da hakan sedai ganin yadda mijinta ya kafeta da Ido yasata saurin sakin hannun Nijlah tana Nuna Mata kusa da mujaheed’ jeki zauna kici abinci kinji kanwata.

Maqale kafada nijlah tayi tare da turo pink lips dinta.

To menene kuma’husan ta tambaya.

Cike da shagwaba nijlah tace’ ni ni a baki zaki bani’ sabida Shima Dan birni a Baki yake bani’

Zaro Ido husna tayi tana cewa’ wanene Dan birni?

Mujaheed ko sabida koshin dayaji ya somasa sai da ya kware ya Shiga tari yana cewa nijlah wanene haka.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button