YAR SADAKA Page 31 to 40

Hmmmm Nasir Kenan Ni wallahi kuna Bani mamaki Idan kuna Kiran nijlah da yarinya’
Yarinyace mana mashkur inba yarintaba meze sa ta riqayin wannan abubuwan daka lissafa..
Babu Wani yarinta’ yarinyar datasan Kishi Har tana cewa banyimata adalciba kodan ita banasanta shiyasa Zan auro wata.
Kai mashkur nijlah Ke gayama haka’ wallahi kuwa nasir’ Ni kaina Saida nayi mamakinta’ Nasir kasan nasaba waya da Yasmeen a Duk lokacin dazan kwanta to Ashe Dai nijlah ba bacci takeba’ labe kawai take mana Sai yanzu take gayamin Duk abinda Taji inayi a waya,, inda Allah yasoni ba Wani abun tashin hankali Taji ba Dan bazata Iya tsaida Ido Taji komai ba..
Dariya Nasir yayi Yana cewa kaima Dai Baka kyautaba tinda kayi aure Ai saika Dena wayan dare.
Kai tafi can wanne irin sure yarinyar da Ko wasa nayimata Bata Iya ganewa..
Shidai Nasir Banda dariya Babu abinda yake’ Saida yayi me isarsa kafin yace’ yanzu Dai yaushene daurin auren?
Ranar asabar ne.
Kai abokina Baka da kirki shine Baka gayamin ba Sai yanzu ‘ kayi hakuri Nasir yanzu ma Bana gayama Dan kazobane nagama ne sabida Hankalinka ya kwanta..
To shikenan tinda Dai kuna lafiya alhamdulillah’ yanzu Dai ga Bello saiku gaisa’ mashkur Na dariya yace to bashi wayan…
Bayan sun gaisa Bello ya riqa yimasa dariya Yana cewa’ Aida ka Koro mana ita’ amarya da kashin kwance…
Zaro Ido mashkur yayi Yana cewa kai Nasir an Iya gulma shine harya gayama?
Bello Na dariya yace ba ruwan Nasir Nida kunnena naji’ nan Dai suka jima Suna waya kafin suyimasa Allah yasan alkairi sukayi sallama..
Lallabawa yayi ya Tashi da niyyan fita a Dakin nijlah ta farka..
Dasauri ya miqe tsaye Yana rufe baki Aiko tana ganinshi ta Tashi da gudu ta fada jikinshi tana cewa’
Nidai Allah saika tafi Dani nagaji da Zama Ni daya kama mayya kawai ka mayar Dani gurin kaka Nina fasa Zama da kai’ nijlah ta fada tana qara maqalqaleshi.
Hannu yasa ya dago fuskanta Yana kallanta cikin nutsuwa kafin ya Bude baki a hankali yace’
Nijlah waime kikeyi haka kokina haukane’ Ni kike Gaya wadannan maganganun Ashe baki da kunya’?
Murguda masa baki tayi tana cewa’ Daga fadar gaskiya saika Kamani da fada sabida kaga Bani da kowa’ Ko an gayama nibansan kishiba’ bansan ciwan kwatan Abu a hannuna ba dahar Zaka fara gayamin haka” shikenan Sai ayimin kishiya ban ajiye yaro Ko guda ba..
Ranshi a bace yayi Kanta Yana cewa’Ke nijlah nikike gayama haka yafada Yana nuna kanshi?
Eh haka nace nijlah ta fada cike da rashin kunya..
Lallai kuwa Yau Zan koyamiki hankali tinda baki dashi’ nijlah Ni Kika dubi tsabar idona kike gayama haka..
Jinjiga nijlah ta riqayi tana huci sedai wannan Karan Bata Iya bashi amsaba
???????? *’YAR SADAKA..*????????
*STORY & WRITING BY…*
*BY*
*MOMN SULTAN*
*DEDICATED TO…..*
*MMN AMATULLAH*
*SPECIAL GIFT TO…*
*ZARA…..*
6⃣0⃣&6⃣1⃣
Tinda mashkur ya fita nijlah ta Hada kai da gwiwa tana rera kuka’ harga Allah batasan menene Kishi ba sedai ta taba ganin wata Mata a kauyensu Wanda za’ayima kishiya ta riqa kuka tana zagin mijin ta Kuma San Mata dayawa Basa San kishiya shiyasa itama yanzu da za’ayi Mata take wannan abun..
Toni Koda kishiyar Zemin Ai gwara ya Samu me hankali Dan gaskiya Idan ya auro wannan matar kasheni zatayi’ kuka ta qara saki Na tausayin Kanta tare da Jin kewar kaka, ahaka bacci ya dauketa Bata bi takan takeaway daya kawomata ba..
Tuqi yake Yana tinanin tare da nazari sosai akan nijlah Babu Hakka wannan yarinyar ba qaramin wayo garetaba sedai Bata da kunya’ Duba da yadda ta nake Magana tana mayarmin mtsss Yaja tsaki’ Yana cewa kodan ba laifinta bane tinda kishiya za’ayimata, Sai kuma yayi murmushi Wanda ya bayyanar da hakoransa Yana cewa sufa Mata Basu kankanta indai aharkan Kishi ne,,yanzu da haqqina na amsa da tinin tana gadon asibiti Amma dayake harkar kishine gashinan ta Iya rashin kunya da kukan banza..
Da tunani barkatai harya isa gidan jabeer’ Yana zuwa ya kirashi a waya ya shaidamasa Yana kofa su fito’
Fitowa jabeer yayi Yana cewa ango kasha kamshi kayi hakuri Mun tasoka,,kasan bansan Saban gidaba shiyasa Naga kazo kawai mu tafi tare zefi sauqi da muyita waya.
Hakane Nima yanzu Na shirya inasan fita Naga kiranka’ Dan da tinima Na tafi wannan yarinyar ta tsareni da rigimarta.
Dariya jabeer yayi Yana cewa kajika wacce yarinya Kuma da Dai uwar gida kace zanfi ganewa’
Murmushi mashkur yayi Yana cewa kaga tana Ina muje itama tayi nata aikin Dan wallahi nijlah tace bazatayi karatun arna ba.
Dariya jabeer yayi Yana cewa kai Dan Allah’ Amma Ko indai hakane zata bamu matsala.
Indai nijlah ce zakaga abinda nake gayama’ to ai shikenan indai Khadija ce nasan zata gyamaka ita’ to Allah yasa cewar mashkur cikin sanyin murya tare da kwantar da kanshi jikin Mota Yana tinani..
Dafashi jabeer yayi Yana cewa kaga abokina kada ka Zama Rago,Kabi komai a hankali nasan yarinyar zata nutsu,,kai wallahi Idan nijlah ta girma saita kere Yasmeen sabida tana da qira me kyau gashi tin yanzu tafara nunamaka soyayya harfa Dan fari ka qara abokina.
Murmushi mashkur yayi sabida yasan Duk kilewan da nijlah zatayi bazata taba kaiwa Yasmeen ba Dan Yasmeen karshece gurin Iya kalamai masu sanyi da kwantar da Hankali” abokina bakace komai ba?
Muje kawai mashkur ya fada Yana yatsina fuska.
Ok Baka yadda da Magana Naba ko,,wallahi mashkur nijlah ta hadu Idan kaduba yadda qugunta ya zauna jikinta saikace dasamata Shi akayi gata kyankyawa sannan ka Duba yadda qirjinta yafara cika tin ba….
Cike da tsawa mashkur yace’ kaga jabeer ya isa haka’ matatace kake qarewa kallo haka gaskiya banaso Idan Zaka kirata muje to Idan Kuma bazakaje ba shikenan Saina nemi wata mafitan yaqare maganar cikin fishi ba bacin Rai tare da zallar kishi..
Dariya jabeer yayi ya tafi Yana cewa Allah yabaka hakuri angon yasmeen..
Shiko mashkur haushine ya cikamashi zuciya jiyake kama ya kama jabeer yayita Duka sabida Kalle masa nijlah dayayi,, ahaka jabeer yaje ya Kira Khadija suka qaraso jikin motan.
Suna zuwa hajiya Khadija ta gaisheda mashkur’ haka mashkur ya amsa fuska ba yabo ba fallasa suka Shiga motan mashkur ita Kuma hajiya Khadija ta Shiga nata motan sabida zata dauko nijlah su tafi…
Tinda mashkur ya fita nijlah Ke kuka Har suka dawo.
Dasauri mashkur yaqarasa inda take ya janyota jikinshi Yana sharemata hawayen fuskanta’ nijlah meyasa kikesan Sani cikin damuwa kiduba abincinki kofa ci bakiyi ba’ meyasa kikemin irin haka? Why nijlah..
Maimakon nijlah tayi Shiru Saima fadawa jikin mashkur tayi taqara sakin kuka tana cewa’ indai kana damuwa da kukana meyasa bazaka fasa auren wancan muguwan ba,, itane fa ta dakeni Dukan da Ko kaka Bata tabayimin Shiba,, Kuma Baka ramamin ba..
Kanta ya shafa Yana Magana a hankali’ haba nijlah ta kintaba ganin inda miji ya Shiga fadan Mata Idan sunayi’ Kuma Ai Nace kada taqara dukanki..
Janye jikinta tayi tana cewa nidai Allah ita ba matanka bace aidai nice matarka,, dariya yayi ya juna inda yabar jabeer da hajiya Khadija yadan Sosa kai Yana cewa Bismillah ku zauna..
Ke Kuma Shiga ciki ki dauko hijabi kizo inasan Magana dake GA Kuma aunty nan Na kawomiki.
Nijlah Bata musaba ta Shiga daki da gudu tana murna ta dauko mayafinta ta yafa’