A SANADIN GROUP COMPLETE HAUSA NOVEL

A SANADIN GROUP COMPLETE HAUSA NOVEL

[10/14, 6:55 PM] Sadnaf: ???? S????N????DIN GROUP????????

Written by

???????? SADNAF????

PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_  *P.M.L*

#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com

A short story based on true life story

Page 1_5

Manal a zaune take akan dining table ita da Mijinta da yaranta Uku,suna cin Abinci,hankalinta na kan Daddyn Hanif dake cin abincinsa hankalinsa kwance,yanda ma yake cin abincin kasan ba k’aramin dadi abinci yake mishi ba,d’agowa Daddyn Hanif yayi suka had’a ido,suka sakarwa da juna murmushi cewa yayi ” aa Momin Hanif kallon yanda nake loma kike ko,?” Murmushi tayi tace “ko d’aya mai ka gani,”? Loma ya kai bakinsa yace kallona kike mana tunda zu Dan ke ba abincin kike ci ba sosai,karma kiga laifina Dan abincin yayi dadi sosai dole nayi loma” Daddyn Hanif yace yana k’ara kai loman abinci bakinsa” Hanif d’an shekara takwas dariya ya kwashe dashi yace “daddy kar dai ka k’ware kamar ranan, ” kanensa Salem da taufiqa suma dariyar suka yi suna kallon daddyn nasu Dan indai zai ci abinci sai yayi santi, Dan Manal ta iya girki sosai ba laifi,ahaka suka gama cin abincin suna zolayar juna, su Hanif suka tashi suka nufi Palo,suka bar Manal da Yusif a zaune akan dining, sai da Yusif ya tabbatar da yaran sun gama ficewa ya matsa kusa da Manal yace

“Mom Hanif wanan girkin yafi na koyaushe dadi,idan na dawo dole na biya,badan ina so naje nayiwa Hajiya sallama ba, da babu abinda zai fitar dani.”

tunda ya fara magana take ta zuba murmushi, tace “karka damu daddyn Hanif kayi sauri kaje ka dawo,ina nan na maka tanadi na musamman, Manal tace tana kashe masa ido d’aya murmushin jin d’adi yayi yace ” Allah Mom Hanif”

“Allah kuwa kai da zaka yi tafiya gobe kasan dole in tanade ka” janyo ta yayi ya rungumeta yace ” bari nayi sauri naje na dawo I can’t wait” tare suka mik’e suka nufi Palo, Hanif da Salem na zaune akan kujera suna Home work d’insu,Taufiqa na zaune akasan carpet tana kallo,Yusif wajen su Salem ya nufa ya duba home work d’in da suke yi,ganin sun iya home work d’in ne yasa ya mik’a musu suka cigaba,ya nufi wajen Taufiqa da ta mayar da hankalinta kan kallon da take yi,tsuguna wa yayi a gabanta yace “baby ke kinyi home work d’inki ne”?

” Nayi Home work d’ina daddy,tun jiya momy ta koya min”

Murmushi yayi yace “da kyau babyna mai zan taho miki dashi”?

Da sauri Hanif ya ajiye pencil d’in hanunsa ya nufi inda suke yana ” daddy zan raka ka gidan hajiyan” shima Saleem rigima yasa yana zai raka shi,adai dai lokacin da Manal ta fito daga d’akinta hanunta d’auke da wani viva bag,

“Daddyn Hanif lafiya naga sun sa ka agaba”?

Manal tace tana mik’a mishi ledar hanunta tana ya kaiwa Hajiyarsa yace tana gaisheta,k’arbar ledar yayi yana ” ki rabani da yaran nan naki sun dage sai sun rakani,”

“Daddyn Hanif ka tafi dasu mana Dan Allah na samu ma nayi barci” Manal tace tana mik’ar da Taufiqa,

“To shikenan kuzo mu tafi,Yusif yace yana yin hanyar waje,Hanif da Salem da sauri suka d’auko takalminsu suka bishi da gudu suna murna,Manal d’akin ta nufa ta d’auko wa Taufiqa Hijabinta ta sa mata,ta rik’e hanunta suka yi waje.

Gaban motar ta bud’e ta sa Taufiqa aciki,Dan su Hanif suna zaune abaya,rufe k’ofar motar tayi ta lek’ar da kanta tace ” Daddyn Hanif sai kun dawo Ku gaishe min da hajiyar,” amadadin ya bata amsa K’ane mata ido yayi ya faki idon su Saleem ya hura mata kiss,murmushi tayi itama ta mishi blowing Kiss ta ja da baya,yaja motar su Hanif na mata bye bye,tana tsaye har sai da suka bar harabar gidan,ta koma ciki tana murmushi.

Manal da Yusif shekararsu goma sha uku da aure,aure suka yi na soyayya,Inda Allah ya azurta su da yara uku,Hanif shine first born,yana da shekara 8,Salem shine second born yana da 6,sai Taufiqa da take da shekara 4,Yusuf d’an chanji ne yana aiki anan Abuja,duk weekends yake zuwa gida,ran Monday ya koma da sassafe, akwai soyayya mai k’arfi atsakaninsa da Manal duk da dadewar da suka yi da aure hakan bai sa sun rage San da suke wa junansu ba,Dan idan ba saninsu kayi ba,tunani zaka yi basu dade da aure ba Dan yanda suke Ji da juna kamar basu dade da aure ba, Yusuf burinsa a rayuwa bai wuce yaga ya farantawa Manal da ‘yayanta ba,duk da yana da kud’i hakan bai sa yayi amfani da wanan damar yayi kula kule ‘yan mata ba,inda Manal itama nata b’angaren hakane,tana masifar San mijinta sabida yana k’ok’arin faranta mata babu abinda ta nema ta rasa a rayuwarta,sai dai ta godewa Allah,Manal na da Ilimin addinin dai dai gwargwado,yaranta sun taso da tarbiyya da ilimin addinin kwarai da gaske,dan tayi tsayuwar daka wajen koyawa yaranta ilimin addini,shi yasa duk inda yaran suka shiga sai an yaba irin tarbiyar da mahaifiyarsu ta musu,hakan kuwa ba k’aramin farantawa Yusif rai yake ba,shi yasa ya ke k’ara Santa a zuciyarsa.

Tana shiga ciki,ta Dan yi aikace aikacenta duk da tana da ‘yar aiki wanan bai sa ta sakarwa ‘yar aikinta komai ba,bedroom d’in Yusif ta shiga ta k’ara gyarawa ta turara d’akin ta fito,Palo ta koma ta zauna akan kujera ganin bata aikin komai ne yasa ta janyo wayarta ta bud’e data ta hau Watsapp,sai da ta bari messages sun gama shigowa ta bud’e family group d’insu mai suna ZURIA D’AYA duk Wanda ke cikin grp d’in ‘yan uwanta ne Dan Familynsu na da yawa,shi yasa suka bud’e grp Dan su sada zumunci,Sallama tayi kamar yanda ta saba,sai adduoi da fatan alheri da tayi posting,aikuwa nan da nan,suka fara Zolayarta,kamar yanda suma suka saba,ahaka ta biye musu,sai da ta ga abun nasu ba mai karewa bane,ta rufe grp d’in ta bud’e d’aya group d’in na matan aure mai suna MU KARU DA JUNA ta fara ka karanta chatting d’insu tana murmushi dan gabad’aya group d’in matan aure ne a ciki,basu da hirar da ya wuce,Sx da kayan Matan da zasu sha dan su rikita oga,bata fi sati biyu da shiga group d’in ba,Dan a grp biyu kawai take Dana Familynsu,da wanan na mukaru da juna d’in,shima ta silar cousin d’inta Ummi ta shiga grp d’in,Sallama kawai take yi,tayi ta karanta chatting d’insu bata tab’a tofa baki a maganar da suke ba sai dai ta tura Smiley ???? in Abu ya bata dariya,tana cikin karanta chatting d’insu taga an turo wani link MANYAN MATA HARK’A 1 wacce ta turo link d’in tace Wanda yake da sha’awa ya shiga group ne na Manyan Mata

Haka kawai taji tana sha’awar shiga group d’in,ta kuwa yi joining,abun mamaki tana joining bai fi mutane biyu ne suka yi joining ba,taga wata Hajja Kaltume tace zata yi revoking grp d’in bata San mutane da yawa,Manal ita dai bata ce komai ba,taringa karanta chatting d’insu,yan grp d’in hirar su kawai suke suna wani irin zaurancen da ba ganewa take ba,bud’e group d’in tayi dan taga members nawa ne a cikin grp din 40 of 256 tagani,indicating su arbain ne a group d’in,group admin kuwa guda d’aya wanan Hajja kaltumen,rufewa tayi ta cigaba da karanta chatting d’in da suke yi,wata Maman Aisha ce a group d’in tayi wani irin batsa, Manal tayi sauri tayi a’ uziyya dan Sam batsar da tayi ya mata nauyi a baki,ai kamar jira sauran members d’in group din suke,nan suka Bark’e da hirar batsa,Manal tuni taji hankalinta ya tashi da taga yanda suke batsa,typing ta fara yi da sauri na waazi da kuma suji tsoron Allah akan harshenmu da hannayen mu zasu yi shaida aranar gobe kiyama akan abunda ka aikata,tana cikin typing, d’in wanan Hajja kaltumen ta turo wani video,gani tayi members d’in group sun fara murna mai turo

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25Next page

Leave a Reply

Back to top button