A SANADIN GROUP COMPLETE HAUSA NOVEL

A SANADIN GROUP COMPLETE HAUSA NOVEL

*ABUJA*

Yusuf ne a zaune ya had’a kai da gwiwa bai dad’e da waya da Manal ba,k’arfe takwas na safe lokacin,haka kawai yaji yana sha’awar tafiya kano yaga su Manal Dan jiya kawai yayi tunanin ya kamata ya ringa zuwa ganinsu akai akai,ba sai Friday Saturday Sunday ba,Dan gani yake ma Manal al kunya take mishi data ce mishi bata sha’awa in baya nan gwara ya ringa Dan zuwa in ya samu sarari,ganin bashida wasu ayyuka aranar ne yasa ya fara shiryawa dan tafiya kano,har ya d’auko waya zai kira Manal ya fasa Dan so yake kawai yayi suprising d’inta,yana fitowa ya nufi wajen motarsa ya tayar ya d’au hanyar kano.

Ton G

K’arfe goma ya shirya ya taho kano shima suna ta waya da Manal,Dan ita har ga Allah ta cire shi aranta Dan ya dage sai ya ganta ne da babu abinda zai k’ara had’ata dashi.

IDAN BAKA DA HAKKIN MUTUM

*RANA DUBU TA BARAWO RANA D'AYA TAK TA MAI KAYA*

Wuraren k’arfe d’aya na rana Yusuf ya iso kano,ad’an nesa da gidan yayi parking yashiga cikin gidan,Hindatu ya samu a Palo ita kadai,hannu ya aza a lebb’enshi alamar kar tayi magana,maida gaisuwarta tayi,tana kallonsa ce mata yayi yana k’asa da murya ina “Momyn Hanif”? Hindatu ce mishi tayi ta tafi ta d’auko taufiqa daga makaranta Dan 12:30 aka tashinsu,Dan tun jiya ta shirya komawa irin rayuwar da take yi ada a gidanta,ta hanyar kula da yaranta da kanta babu yanda Hindatu bata yi ba akan tabari ta d’auko ta Manal tak’i,

Murmushin jin dadi Yusuf yayi Dan yaji dadi da bata nan zai ji dadin suprising d’inta,cewa hindatu yayi karta sake tace mata ya dawo,ya nufi d’akinta rage kayan jikinsa yayi, Dan ya gaji,ya kwanta akan gado yana murmushi shi kad’ai Dan ya hango irin tsallen murnar da Manal zata yi inta ganshi,wayarta dake side bed yana chargy ne yafara ringing, bai ko motsa ba yace ” Ashe ma barin wayarta tayi a gida,ganin ana kira babu kak’autawa ne yasa ya d’aga wayar, ji yayi ance “hot milk ina hanya nakusa k’arasowa pls send me the address” dif yaji an kashe wayar,wayar subucewa yayi daga hanunsa kirjinsa yayi wani irin bugawa,jiki na rawa ya d’auki wayar ya duba yaga titi ne ya kira,message ne ya k’ara shigowa wayarta,bud’ewa yayi yaga titi ne ya turo mata tex Dan Allah ki turo min address d’in ayau nakeso na koma na kusa fa Dan na ma wuce ‘yan kura

Yusuf ji yayi kamar da guduma ake buga masa kai,k’irjinsa kuwa kamar mutane sabain ne suke caka masa wuka, ahankali yafara bin messages d’in wayar yana karantawa sai da yagama Dana inbox ya shiga sent item shima reply d’in da Manal tayi wa titi rututu yagani,watsapp d’inta ya bud’e dan yaga message d’in da Titi yace su had’u a watsapp ya sumar da ita,charting d’insu yafara karantawa,da videos d’in da suke turawa juna,hotunan da Manal take d’auka na k’irjinta da kasanta ta turawa Titi ya ringa gani,numfashin Yusuf ne yafara sama da sauri da sauri,bugun k’irjinsa ya k’aru sakin wayar yayi ya dafe kansa dake barazanar tsagewa ya k’urawa hoton cinyar manal ido.

Manal suna shigowa gida haka kawai taji gabanta yayi wani irin fad’uwa, addua tayi a zuciyarta,gabanta ya k’ara fad’uwa da ta tuna Ton G yace mata zai zo,haka kawai jikinta ke gaya mata watak’ila ba ita gaisawar zasu yi ba,so yake ya yaudareta,d’akinta ta nufa dasauri Dan ta cire sim d’inta sabida in ya kira kar ya sameta,tana tura k’ofar suka had’a ido da Yusuf da ya koma mata tamkar zaki,da sauri ta kalli gabansa taga wayarta a yashe akasa,Zubewa tayi akasa ta d’ora hannu aka Dan sam kamar an k’wada mata sandar mantuwa bata goge komai awayarta ba.
[10/14, 6:56 PM] Sadnaf: ???? S????N????DIN GROUP

Written by

???????? SADNAF????

PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_  *P.M.L*

#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com

A short novel based on true life story

Wanan shafin naki ne ke kadai kawata kanwata ta kaina Salma b,I love you so very much from the bottom of my hrt ,may Allah shower his blessing upon you,you are indeed more than a friend love you❤❤❤❤❤❤❤❤❤

Page 30- 35

Cikinta wani irin murd’awa ya ringa yi,jikinta in banda rawa babu abinda yake yi,Yusuf zuba mata ido kawai yayi yana kallonta kamar mutum mutumi,idonsa jajazur kamar babu digon fari a idansa,sai da ya dau tsawon minti biyar yana kallonta,Manal kuwa take ta tuna abinda yace mata,”wlh idan mata ta ce taci amanata sai na kasheta,
idan ban kasheta ba sai na nakasa ta,

idan ban nakasata ba sai na mata mugun duka,

Idan ban mata mugun duka ba wlh tallahi sai na k’ona gabanta na kuma saketa ,

Har duniya ta nad’e ina tsine mata,

Kuka ta fashe dashi Dan tana ta shiga uku ta lalace Dan tasan acikin irin hukuncin da Yusuf ya zayyano zai yiwa matarsa in ita ta ci amanarsa tasan dole yayi mata d’aya ita kowane hukunci yayi mata kar ya saketa,Yusuf kallonta kawai yake bakinsa sai rawa yake kowace jijjiya ta jikinsa a tashe fuskarsa tayi jajjawur,Manal had’e Hannayenta tayi alamar rok’o tace “Daddyn Hanif ka yimin kowace irin hukunci Dan Allah karka sakeni,wlh sharrin shaidan ne ban tab’a aikata zina da aurenka akaina ba,Dan Allah Daddyn Hanif kayi min kowane hukunci karka sakeni karka rabani da ‘yayana” maganar da take ne ya mak’ale afatar bakinta sakamakon wani irin mari da Yusuf yayiwa kansa ya buga kansa a bango take kansa yafara jini,wani irin rawa bakinsa ya ringa yi ya nuna Manal da yatsa yace cikin karaji,

“Manal ki tasheni daga mugun mafarkin danake,

Manal kizo ki taimakeni kice min mafarki nake yi Manal d’ita bazata tab’a cin amanata ba

“Manal d’ita mai tsoron Allah ce bazata tab’a min haka ba

” Manal ki taso kice min wanan hotunan da nake gani ba naki bane,Manal ki karyata idanuna ba hoton sirrina naga kin turawa wani ba Manallllll taso nace kafin in samu tab’in hankali,

Yusuf yace yana bubuga kansa

Zuwa wanan lokacin Manal ta saki fitsari a zaune Dan tunda take bata tab’a ganin Yusuf awanan halin ba ayanda take ganinsa yanzu kamar ba a hayyacinsa yake ba,tashin hankalintan bai wuce kansa dake ta zubar da jini ba,kuma ahaka ya cigaba da bubuga kansa,wani irin kuka ta fashe dashi,tana “Daddyn Hanif kayi hakuri ka yafemin ???? S????N????DIN Group na shiga wanan tashin hankalin wallahi ba halina bane,”

Cak Yusuf ya tsayar da buga kansa da yake ya juyo yana kallonta,hanjin cikin Manal ne yayi wani irin Hautsinawa Dan Yusuf hancinsa har jini yake,Yusuf wani irin durowa yayi ya nufi inda take,Manal tsabar tsorata da tayi zubewa tayi akasa a sume,Yusuf da idonsa ya Riga ya rufe wani mugun bugu ya mata Manal ta mik’e a firgice,tana sallati,Yusuf shak’eta yayi ya had’ata da bango yafara magana yana k’ink’ina dan idan ransa ya b’aci har k’ink’ina yake,

“Manal ki min bayani abinda nagani awayarki,ki tasheni daga barcin da ya d’aukeni,Manal kimin bayani kwakwalwata ta daina aiki na kasa gaskata abinda idona ya ganemin,sirrina sirrina Manal,kike turawa wani,Manal kalmomin da baki tab’a min amatsayin mijin aurenki naga kin turawa wani,zuciyata ta kasa gaskata Manal zata iya cin amanata,manal ki tasheni daga barcin da ya d’aukeni,I know am dreaming,”Yusuf yace yana girgiza ta da k’arfi,Manal kuka ta fashe dashi tafara ” Yusuf kayi hakuri sharrin shaidan ne wlh ba halina bane”

Yusuf ja da baya yayi yana kallonta hawaye ya b’alle a fuskarsa girgiza kai ya fara yi yana “Manal mai na miki kika ci amanata?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25Next page

Leave a Reply

Back to top button