Our website is made possible by displaying online advertisements to our visitors. Please consider supporting us by whitelisting our website.
A SANADIN GROUP COMPLETE HAUSA NOVEL

A SANADIN GROUP COMPLETE HAUSA NOVEL

Ad

_____

Manal hawaye ne ya hau zubo mata ta rasa mai zata ce mishi,”Tambayarki nake nace waye yace kidawo gidana alhalin ban ce ki dawo ba”?

Manal da kuka ya Riga yaci k’arfinta d’aurewa tayi tace “Hajiya ce ta dawo dani”,

Yusuf juyowa yayi yana kallonta Dan duk maganar nan da yake yi kau da kansa yayi ce mata yayi “kin fad’awa Hajiyar abinda kika min? Kin fad’a mata yanda kika ci amanata”?

Zuwa wanan lokacin Manal ta d’urkushe tana fashewa da kuka,cikin kuka tace “Ban gaya mata ba Yusuf ina jin kunyar wani yaji abinda na aikata,ina jin kunyar hajiyar tasan yanda na ci amanarka,Dan Allah Yusuf kayi hakuri ka yafemin wlh nayi danasanin abinda na aikata nayi nadama,Dan Allah ka dubi girman Allah ka yafemin ko dan zuriar dake tsakaninmu nayi kuskure abaya bazan sake ba insha Allahu,” tace ta na k’ara fashewa da kuka,kukan da take yi ba k’aramin tab’a zuciyar Yusuf yake ba dan wani irin Santa da tausayinta yaji ya lullub’eshi amma so yake ya koya mata hankali ta k’ara shiga hankalinta,ce mata yayi, “Manal kenan zan iya yafe miki abinda kika min amma bazan tab’a iya goge abinda kika min a zuciyata ba,kin dasa min tsanarki araina,ban tab’a tunanin zaki ci amanata ba Manal,zan yafe miki sabida yarana,amma kuma inaso kisani bazan iya zama dake ke kadai ba zan k’ara aure Dan yanzu haka ma nagama maganar da yarinyar da zan aura,” tunda ya fara magana Manal taji k’irjinta na dukan uku uku,auren da ya ambata ne yasa ta k’irjinta k’ara dukan Tara Tara,sai da ta samu minti goma a durk’ushen tana kuka ta kasa magana,Yusuf kuwa ko motsawa bai yi ba juyar da kansa yayi kukanta na tab’a zuciyarta Manal d’aurewa tayi ta fara magana “Kayi hakuri Yusuf nasan nayi maka ba dai dai ba na yarda ka k’ara auren Indai zaka yafemin,ka dawo da sona zuciyarka karka manta Allahn da ya hallicemu muna mishi laifi mu nemi yafiyarsa ya kuma yafe mana,nasan ba zaka iya manta abinda nayi maka ba amma kayi hak’uri ka yafemin sabida yaran dake tsakaninmu”

Yusuf maganganunta ba k’aramin kashe masa jiki yayi ba tausayinta da kaunarta kawai ke yawo a jikinsa ,shiru yayi bai magana ba Dan bai San mai zai ce matan ba,Manal kuwa ganin tafi minti ashirin a d’urkushe bai ce mata komai ba yasa ta mik’e tace Allah ya huci zuciyarsa,” band’aki ta nufa ta had’a mishi ruwan wanka ta fice daga d’akin,Yusuf bayanta yabi da kallo har tafice ji yake kamar ya rungumeta,tashi yayi yafara cire kayan jikinsa dan yayi wanka.

Manal kuwa tana barin d’akin kitchen ta nufa ta d’ora mishi girki,tana gamawa ta kai mishi har d’aki Dan bai fito Palo ba,yana zaune a kujerar dake d’akin yana Dane Dane a system d’inshi,shigowarta da kamshin abincinta ne yasa ya d’ago yana kallonta cikinsa kuwa ya hau kugin yunwa,ajiye farantin tayi atsakiyar carpet ta bud’e kullolin ta fara zuba mishi abincin,k’aramin centre table ta jawo ta d’ora abincin akai ta zuba mishi lemo da ruwa ta fice daga d’akin Yusuf da sauri ya rufe system d’in ya jawo center table d’in Dan bak’aramin yunwa yake ji ba,inya ce zai yi zuciya da abincinta yasan shi zai cutu,yana kai loma d’aya bakinsa ya lumshe ido dan yayi missing d’in abincinta sosai.

Da yamma wajen k’arfe biyar ya nufi gidansu,Dan barci mai d’an karan dadi ne ya d’aukeshi Wanda ya Dade bai yi ba bayan yaci abincin da manal ta girka masa,a Palo ya tarar da Hajiya Munawarra tana kuwa jin sallamarsa ta d’aura fuska tana amsa sallamar murmushi Yusuf yayi ya d’urkusa ya fara gaisheta dan yasan Fushi take yi dashi,bata amsa ba ta rufe shi da fad’a ta inda take shiga bata nan take fita ba Yusuf hak’uri kawai yake bata yana yayi kuskure bai zai sake ba tayi hak’uri da k’yar ta hak’ura ta fara mishi nasihar da ya ringa hak’uri yana kai zuciyarsa nesa ya rik’e Manal da amana,dan Manal tana da hak’uri ga hankali,ahaka ta ringa mishi naseeha da yazo tafiya,ta had’a kayansu Haneef da abun wasansu ta bashi tace ya kai musu.

Lokacin da ya baro gidansu ana kiraye kirayen sallahr Ishai sai da ya tsaya yayi sallahr ishai a masallaci yayi siye siye a hanya kafin ya k’arasa gida,

A Palo ya Tarar dasu gabad’aya Manal taci kwalliya ba laifi tayi kyau,Su Hanif mik’ewa suka yi suka fara mishi oyoyo suna k’arbar ledojin hanunsa Manal sunkuyar da kanta tayi har ya k’araso ya zauna akujerar dake fuskantar ta,sannu da zuwa tayi mishi ya amsa yana satar kallonta,wani kyau yaga tayi mishi na musamman,ji yake kamar yaje ya rungumeta amma ina ba yanzu ba so yake sai ya nuna mata kuskurenta,hira ya ringa yi dasu Hanif yana Satan kallonta,Su hanif kuwa ice cream d’insu kawai suke sha suna bashi labari,Manal ita dai kanta a sunkuye bata sa musu baki ba,ahaka suka yi ta hira yana Satan kallonta, har lokacin kwanciyarsu yayi, suka nufi d’akinsu,ya mik’e shima ya nufi nashi d’akin,Manal sai da tayi wanka ta feshe kowane lungu da sak’o na jikinta ta saka rigar barcin data San tana Jan hankalinsa ta nufi d’akinsa,akwance ta Tarar dashi yayi rub da ciki,idonsa a lumshe,har ta bud’e k’ofar ta shigo yana jinta bai bud’e idonsa ba,Manal kuwa duk da gabanta fad’uwa yake hakan bai sa ta k’araya ba ta hau kan gadon ta kwanta a gefensa ta zuba shi ido tana kallonsa,wani tsananin so da sh’awarsa taji yana fisgarta,sai ta kai hannu zata tab’a shi sai ta maida hanunta da sauri,Yusuf kuwa duk abinda take yi yana jinta, tunda kamshin turarenta ya ziyarci hancinsa,yaji wani sha’awarta na taso masa,dakewa yayi ya k’i bud’e idonsa,dan Manal ma zata iya gane halin da yake ciki in ya bud’e idonsa,Manal kuwa ganin kai da mayar da hanunta ba shine mafita ba yasa ta d’aure ta kai hanunta jikinsa,Yusuf zame jikinsa yayi da sauri ya matsa yana juya mata baya,Manal hawaye masu zafine suka zubo mata data ga abinda ya mata Yusuf kuwa k’arfin hali kawai yayi,dan bayaso tagane ya hak’ura da wuri,atakaice aranar babu Wanda ya iya barci a cikinsu dan Yusuf Palo ya fito yana ta juye juye,Manal kuwa ganin da tayi ya bar mata d’akin ne yasa taci kuka ta gode Allah,a karshe ta mik’e ta shiga band’akin ta d’aura alawala tazo ta fara nafilfili,tana adduar Allah ya karkato da zuciyar Yusuf wajenta ya sa ya hak’ura da abinda tayi mishi.

Atakaice ahaka Yusuf ya gama weekends d’insa babu abinda ke shiga tsakaninsa da manal da ya wuce gaisuwa,yana cin abincinta duk wani hidima tana mishi,amma babu hirar dake shiga tsakaninsu Manal abin na damunta dan har ranar Monday dazai koma sai data k’ara Neman yafiyarshi yace mata babu komai ya yafe mata.

Yusuf kuwa yana isa Abuja ya samu ogansa ya rok’eshi da ayi mishi transfer ya koma kano,dan yana tsoron abinda ya faru abaya,gwara yajishi a kusa da iyalinsa hankalinsa yafi kwanciya,aikuwa ran laraba aka kirashi akace anyi mishi transfer zuwa kano,Yusuf ba k’aramin farinciki yayi ba,ataikaice ahaka ya tattaro inashi inashi ya dawo kano,Manal tayi mamakin ganinsa ranar alhamis,amma bata nuna mishi ba bakuma ta tambayeshi dalili ba,

Ganin da tayi Monday yaje aiki ya dawo ne yasa ta kasa hak’uri sai da ta tambayeshi dalili,shi kuwa yace mata anyi mishi transfer ya dawo kano da aiki,Manal ba k’aramin farinciki tayi ba Su hanif ma da suka ji abbansu ya daina tafiya farinciki ne ya rufesu suka ringa murna.

Ad

_____

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button