Our website is made possible by displaying online advertisements to our visitors. Please consider supporting us by whitelisting our website.
A SANADIN GROUP COMPLETE HAUSA NOVEL

A SANADIN GROUP COMPLETE HAUSA NOVEL

Ad

_____

Manal hannu ta d’ora aka tana zunduma ihu,”karka min haka Yusuf karka rabani da yarana,nayi nadamar abinda nayi,shaidan ne ya sakoni agaba,kayafemin ban kai ga aikata zina ba ka dubi yarana ka yafemin ka yanke min kowane irin hukunci karka sakeni” tsaki Yusuf yayi yace ” kinsan da yaran kika je kina iskanci bazan iya zama dake ba baki dace da zama uwar ‘yayana ba”

Kallon Ton G yayi yace “wanan abokanan naka duk kasansu” dasauri Ton G ya gyad’a kansa, ” to inaso ayau ba gobe ba ka kirasu d’aya bayan d’aya kace ka had’u da ita harija ce,kai kayi mata kad’an tace suma suzo zata biya su kud’i mai kauri,kace dukansu su turo da account number tace zata tura musu kud’in mota,kasan yanda zaka yi su zo gidanan,if not sunanka gawa maza yanzun nan ka kirasu d’aya bayan d’aya ina jinki,Ton G cikin tsananin rawar jiki ya k’arbi wayar shi jiki na rawa ya ringa kiran abokanan nashi one by one,hud’u ya samu awaya d’aya ne bai samu ba ,wayanda ya samu d’in murna suka ringa yi suna gobe zasu taho bara su tura account number d’insu,

Yusuf jin sunce zasu zo gobe ne yasa ya gyad’a kansa yace “yayi kyau saura uwar gayyarku Hajja Kaltume, waro ido Ton G yayi yace “Alhaji matar aurece fa” shut up my Friend karuwa dai, maza bani contact d’inta kafin naci ubanka” jiki na rawa Ton G ya bashi lambar yayi saving,mik’ewa yayi ya ja hanun ton g ya kaishi boys quarter ya watsar dashi yace sai abokananka sun zo zanyi freeing d’inka bani wayarka, mik’a masa wayar Ton G yayi,ya fice daga d’akin,tunda suka yi boys quarters Manal keta birgima tana kuka, gani take gwara taga mutuwarta data ga ranar rabuwarta da Yusuf da yayanta,shigowar Yusuf ne ya sa ta mik’e dak’yar ta nufi wajen Yusuf,cikin tsanani fushi da b’acin rai Yusuf yace “karki sake ki matso kusa dani,before counting of two get out of my house I don’t want to see your face again,Manal Neman zubewa take akasa,Yusuf ya finciko hanunta yayi hanyar gate da ita ya watsar da ita waje ya rufe gate ya koma ciki.
[10/14, 6:56 PM] Sadnaf: πŸ…° SπŸ…°NπŸ…°DIN GROUP

Written by

πŸ’…πŸ’… SADNAFπŸ’ž

PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_  *P.M.L*

#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com

A short novel based on true life story

Page 40-45

WANAN SHAFIN NAKI NE KE KADAI KAWATA TA KAINA,AUNTY KHADY THANKS FOR BEING THERE FOR ME ALLAH YA BAR SO DA KAUNA YA BARMU TARE ILYSVM🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

JINJINAN BAN GIRMA GAREKU MEMBERS D’IN MIEMIE BπŸ‘„ NOVEL 2 COMENT D’INKU NA MUTUK’AR K’ARFAFA MIN GWIWA LOVE YOU GUYS LIKE DIEπŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„

HMM AUNTYNA (AUNTY SISπŸ’ž )
MY EVERYTHING HAVING YOU BY MY SIDE MAKES ME FEEL LIKE A QUEEN I CAN’T REALLY EXPLAINED HOW GRATEFUL I AM MAY ALLAH GRANT YOUR WISHES AND FILL YOUR HEART WITH HAPPINESS

Yusuf d’akinsa ya nufa yana shiga ya zube akan gado dan wani zazzabi zazzabi yaji yana Neman rufeshi,ga ciwon kai mai tsanani kamar kansa ya rab’e gida biyu,hawaye mai zafi ne ya hau zubo mishi Dan shekarar goma sha uku da suka yi aure basu tab’a fad’a da manal tayi yaji ta tafi gida ba,ba atab’a jin Kansu ba,sai gashi Manal tayi abinda yasa bazai iya zama da ita ba, magana ya fara yi shi kadai yana juye juye “Manal y manal y what have I done to deserve this from you,duk k’ok’arin danake akanki Manal ni zaki ciwa amana,mai zance wa ‘yayana in suka dawo Manal kin cuceni bazan k’ara yarda da kowace mace ba mutane nawa ne suka ga sirrina,kin cuceni kin cuci ‘yayana ” kuka Yusuf ke yi sosai kamar mace sai da ya gaji dan kansa ya mik’e dak’yar ya nufi band’aki dan yayi alwala yayi sallah.

Manal kuwa sai data samu minti 30 azube akasa tana kuka ganin ta fara Tarawa kanta jama’a ne yasa ta mik’e da k’yar jiri na d’ibanta ba ko takalmi a k’afarta ahaka taje bakin titi ta samu abun hawa ta nufi gidansu,tunda suka d’au hanyar gidansu ta d’ora hannu aka tana ta kuka Dan bata San mai zata CE a gidansu ba tunda take ko yaji bata tab’a yi tsakaninta da gidansu ziyara ce mahaifiyarta na alfahari da ita Dan har gorantawa kanenta take yi akan su koyi da halinta Dan acikin su biyar mata itace bata tab’a yaji ba,Mallama Rabi takan ce halinta ta d’auko na hakuri,Dan itama har mahaifinsu ya rasu bata tab’a yaji ba,bama wanan ba yanzu mai zata cewa mahaifiyarta ya had’asu da Yusuf,mai zata cewa ‘yayyenta ya had’ata da Yusuf ya dawo da ita gida,baban yayansu Mustapha daya zame musu tamkar uba take tsoro Dan mutun ne shi mai zafin gaske shi ya takawa kanenta birki suke daina zuwa gida da sunan yaji,dan har gidanki zai maidaki ya bawa mijinki hakuri,tashin hankalinta idan yaji labarin abinda ya had’asu da yusuf batasan wane mataki zai d’auka akanta ba wanan abun kunya har ina,idan mahaifiyarta da ‘yan gidansu suka ji abinda tayi,ya zata yi da ranta,yaron da baifi Sa’an Affan autan gidansu ,Affan ma yafi shi cikar ido dan a hoto take ganin girman Ton G,a filli d’an tsamurmuri ne ,maganar mai adaidaita sahu ne ya dawo da ita hankalinta yace mata gasu a layin ,gabanta ne ya hau fad’uwa data ga har sun k’araso layin gidansu,gidansu ta nuna mishi tace su k’arasa Dan ta bashi kud’insa dan babu ko sisi a hanunta,suna isa gidan gabanta ya tsananta fad’uwa ahankali ta sauk’o daga adaidaita sahun tana karanta ” Allahuma ajirni fii musibati wa aklifnin khairin minha,Allah uma lah sahla illa ma ja’altahu sahla wa anta taj alu hazna iza shi’ita sahla”ahankali taji wani nutsuwa ya zo mata gabanta ya rage fad’uwa,ahankali ta tura gate d’in gidan ta shiga.

Gabanta ne yayi wani irin fad’uwa data hango tabarma a shimfid’e a katon tsakar gidan nasu sai yanzu ta tuna duk ran laraba mazan gidansu agidansu suke zuwa suci abincin dare su tatauna matsalolin da ya taso a family da yanda za a magance matsalar,dan ba laifi gidansu na da wanan had’in kan,mata kuma sai duk k’arshen wata suke had’uwa, Hannu ta d’ora aka “tana shikenan tawa ta k’are yau su yaya sai sun kasheni ,Affan ta hango ya fito daga Palo yayo hanyar gate,ahankali itama ta fara takawa tana nufar palon,Affan kuwa hangota da yayi ne yasa ya k’ara sauri ya tado ta,Maganar ya ke k’ok’arin yi yaga Fuskar Manal a kumbure,sallati yayi da k’arfi yana ja da baya,yace ” Aunty Lafiya kuwa mai ya sameki”? Ce mishi tayi yaje waje ya sallami mai adaidaita sahu yana waje, ta rab’e ta gefenshi ta wuce,Affan bin bayanta yayi da kallo,yaga Ashe ma babu takalmi a k’afarta da gudu yayi waje dan ya sallami mai adaidaita sahun ya dawo yaji mai ya samu Manal.

Manal kuwa a k’ofar Palo ta tsaya tana jiyo buruntun Mallama Rabi da ‘yar aikinta Raliya dake tayata aikace aikace da alama girkin da su ‘yayyenta zasu ci anjima take yi,ahankali ta wuce d’akinsu tana zuwa ta zube akasa tana kuka, Affan kuwa yana dawowa ganin bai ganta a Palo ba yasa ya nufi kitchen da Sauri dan ya d’auka tana wajen,yana ganin bata kitchen d’in yace ” Umma ina Aunty Manal d’in”? Mallama Rabi a mamakince ta ajiye cokalin hanunta tace ” wacce Manal d’in”? ” Aunty Manal mana yanzu nan ta shigo inaga ba lafiya ba dan baki ga fuskarta ba a kukumbure” “subhanallahi mai ya sameta tana ina”? Mallama Rabi tace tana yin hanyar waje,Affan yabi bayanta,d’akinsu suka nufa suna d’aga labulen suka hangota a kwance a kasa tana ta kuka,da sauri Mallama Rabi ta k’arasa inda take ita da Affan tana Sallati,” Manal lafiya kuwa mai yafaru? mai ya sameki? Mai ya kumbura miki jiki haka ?ina yaran? Manal kuka kawai take ta kasa magana,hankalin Mallama Rabi ba k’aramin tashi yayi ba tambayar duniyar nan babu Wanda bata yiwa Manal ba,amma kememe Manal tak’i magana sai kuka take kamar zata shide,Mallama Rabi ranta taji ya fara b’aci tace “ke Manal kin d’auka ke yarinya ce inata tambayarki mai yafaru kin k’i kiyimin magana sai kuka kikeyi,to shikrnan karki fad’a min idan yayanki ya zo Mustapha ai kya gaya mishi,ni nasan yanzu suna hanya sun kusa k’arasowa idan ma yaji kika yo wlh maidaki zai yi a Daren nan,Abinda baki yi da kuruciyarki ba sai yanzu da yaranki har uku zaki yi,Mijinki ma da ba ya gari ta ina ma kuka yi fada ke kika sani bari dai yayan naku ya k’araso In ni kin k’i gayamin ai dole k’i fad’a mishi,mik’ewa tayi tabar d’akin tana ta fad’a,Affan kuwa tausayin Manal yagama rufeshi duk da baisan abinda ya faru take kuka ba,rarrashinta ya ringayi da ta daina kukan haka kar kanta yayi ciwo,kiraye kirayen sallah magriba da Affan yaji ne yasa yayi waje,Manal dak’yar ta mik’e ta nufi band’aki dan tayi alwala ji take kamar ta gudu tabar gidan,tunda taji ance ‘yayyenta na hanya.

Ad

_____

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button