Our website is made possible by displaying online advertisements to our visitors. Please consider supporting us by whitelisting our website.
A SANADIN GROUP COMPLETE HAUSA NOVEL

A SANADIN GROUP COMPLETE HAUSA NOVEL

Ad

_____

” Manal ina can ina neman kud’i sabida ke,kina nan kina can amanata mai na rageki dashi,”?Ashe bin maza kike bansani ba,? Ashe idan bana nan maza kike kawowa gidana? Ashe bani kadai nake tarraya dake ba kina da Wanda yake tarraya dake idan bana nan?

Girgiza kai Manal tafara yi da sauri tana kuka,Yusuf juyawa yayi ya d’auko wayar ya shiga watsapp d’inta chatting d’in ita da titi ya k’ara bi ya karanta,ya bud’e videon data tura mishi playing yayi yafara kallo k’irjinsa kamar ya fad’o kasa,Manal kuwa runtse idonta tayi da k’arfi Dan ihun banza da ta ringa yi da sunan kuka dadi ne ya doki kunenta ji take dama kasa ta tsage ta shige,dama mafarki take yi,

Yusuf wayar sub’ucewa yayi daga hanunsa,sabida rawar da jikinsa ke yi,wajen Manal ya nufa a fusace ya rufeta da duka,Manal ihu kawai take yi,amma ina ran maza ya b’aci tuni jini ya b’alle a hancinta,ya kumbura mata baki,da naushi,Dan dukanta yake kamar namiji ya samu yake duka ball kawai yake da ita, Hindatun dake palon a zaune tunda tafara jiyo kukan Manal hankalinta ya tashi ji take kamar ta shiga d’akin,Ganin Taufiqa ta fashe da kuka tana Neman shiga d’akin ne yasa ta rukota Dan tasan duk yanda aka yi ba lafiya ba ahaka su Hanif suka zo suka samesu,Hanif ihun Momynsa da yaringa jiyowa daga d’akinta ne yasa ya nufi d’akin da gudu Salem ya rufa mishi baya,suna shiga d’akin Hanif yace “dadddy” adai dai lokacin da Yusuf ya shak’e Manal yana Neman kai ta lahira,juyowa yayi yana kallon Hanif,durk’usawa Hanif yayi yace “Daddy kayi hakuri ka daina dukan momy,” yace hawaye na zubo mishi,ahankali ya cika Manal,ya zube akasa hawaye masu zafi na zubo mishi,fad’ar abinda yake ji b’ata bakine Dan ji yake dama ya mutu,Manal kuwa yana sakinta zubewa tayi akasa tana maida numfashi,Hanif da Saleem kuka suke sosai Dan daga Manal har Yusuf d’in kuka suke jini kawai ke fita daga jikinsu Dan manal hancinta tsiyayr da jini yake sosai,Yusuf kuma kansa ke zubda jini Dan ba k’aramin gwara kansa yaringa yi da bango ba,

“Manal kin ci amanata bazan tab’a yafe miki abinda kika yimin ba,na tsaneki bazan iya zama dake ba bana San in bud’i ido naganki kin cuceni,abinda baki tab’a yimin ba kinyiwa wani namiji,

Kiran da ya shigo wayar manal ne ya katse masa maganar da yake,da sauri ya mik’e ya d’auko wayar,Manal kuwa ta gwalle ido tana kallonshi,Yusuf ganin titi ke kiranta ne yasa yayi sauri ya d’auki wayar ya Dana ya sa a handsfree, “Hot milk tun dazu na iso kano Dan Allah ki turomin address d’in ayau nake so na koma”

Kashe wayar Yusuf yayi ya kalli su Hanif dake d’urkushe suna kuka yace sufita waje,suna fita ya nufi wajen Manal da tayi suman zaune Dan tasan yau Yusuf sai ya kasheta Yusuf mik’a mata wayar yayi,yace “gashi nan ki kirashi ki mishi kwatance wlh idan kika yi magana da muryar kuka sai na kasheki,”

Manal girgiza kai tafara yi tana bashi hakuri tsawan daya d’aka mata ne yasa ta k’arbi wayar adai dai lokacin da kira ya k’ara shigowa wayar,”ki daidaita nutsuwarki karki bari ya gane kina kuka ki d’aga wayar nan wlh inkika yi anything stupid zakiyi mamakin matakin da zan d’auka akanki,” Yusuf yace yana tsareta da ido cikin rawar jiki Manal ta d’aga wayar ta daidaita nutsuwarta ta fara mishi kwatance muryarta na rawa, Dan kiris ya rage ta fashe da kuka,”

Ton g cewa yayi in the next five minute zai k’araso ya kashe wayar yana dariyar mugunta ya d’auko hodar da zai bada mata yasa a aljihunsa yana sokuwa “ai yau sai na d’ana wallahi”

Yusuf k’arbe wayar yayi daga hanunta ya mik’e ya cire rigarsa yasa wata armless da 3qtr ya zauna a gefen gado yana jiran zuwan Ton G,Manal kuwa kallonsa kawai take gabanta na fad’uwa Dan bata San mai yasa ya canja kayan jikinsa ba,aikuwa minti biyar da wayar sai ga ton g na kira,d’aga wayar yayi,Ton G yace “Hot Milk gani abakin gate” kashe wayar yayi,yayi hanyar waje, Manal ta mik’e da sauri tabi bayansa juyowa yayi ya mata wani mugun kallo yace “ooo biyoni kika yi kiga kwartan naki ki kwantar da hankalinki har d’akinki zan kawo miki shi Dan dama kuringa da kun saba hot milk iso zan mishi” Manal wani irin kuka ne ya k’wace mata data ji mai yace zata yi magana ya fice daga d’akin.

Yusuf a Palo ya Tarar da su Hanif da Hindatu sunyi cirko cirko suna ganinsa suka mik’e a tare,Hindatu ya kalla yafara mata magana,”kije waje ki shigo dawani,kice masa hajiya tace ya shigo daga ciki,kifita dasu Hanif su jiraki awaje, karki ce injini kice inji hajiya,inkin kawo shi har Palon nan ki d’auko masa lemo da ruwa,inkin kawo mishi ki zuba mishi,sai ki shiga d’akin Maman Hanif daga nan kifito kice masa tace tana zuwa,sai kifita waje ki tafi gidanku dasu Hanif anjima zan zo in d’aukesu kinji mai nace ko” dasauri Hindatu ta girgiza kanta ta rik’e hanun taufiqa suka yi waje,Yusuf ya koma d’akin Manal yana jifanta da mugun kallon tsana sai kuka take yi.

Ton G yana tsaye abakin gate sai karewa gidan kallo yake,Hindatu tsugunawa tayi tana gaishe shi su Hanif suma duk’awa suka yi suna gaishe shi,wani murmushi yayi da gefen baki yana amsawa Dan arayuwa yana so yaga an tsugunna an gaishe shi,kamar yanda Yusuf ya gaya mata haka tayi,bayan ta ajiye mishi lemo da ruwa ta shiga d’akin Manal,Yusuf na ganinta ya mik’e ya tambayeta ta bashi lemon,ce mishi tayi eee,yace to tafi gida zai zo d’aukansu Hanif,ta kulle mishi gate d’in,to tace tabar d’akin, Manal kuwa hankalinta ba k’aramin tashi yayi ba Dan bata San mai Yusuf yake so yayiwa Ton G ba Dan taga ya d’auko wuk’a da wata sharb’ebiyar dorina mai baki hud’u,ganin yayi hanyar waje ne yasa ta mik’e dagudu ta ruko rigarsa tana “kayi min rai Yusuf karka yi kisan kai karka yi abinda zai sa kazo kana nadama,wlh babu abinda ya tab’a shiga tsakanina dashi,ban tab’a ganinsa ba wlh waya kawai muke yi” kallon da yake mata ne yasa ta cika mishi Riga da sauri,ya fice daga d’akin.

Ton g kuwa yana daga zaune a Palo ya bararraje kamar a palonsa yake, bin ko ina yake da kallo yana kiyasta irin dukiyar da akashe a gidan,

Sai k’urbar lemo yake yana hararo irin hutawar da zai yi a jikin Manal, Dan da dukan alamu ba sai ya bad’a mata hoda ba,tunda ta kori yaranta da ‘yar aikinta su bar gidan,Dan su ji dadin shanawa,murmushi ya ringa yi shi kadai,yana lashe lebb’e sai kace tsohon maye,

Exotic mai sanyin dake ajiye agabansa ya k’ara d’agawa yana tultulawa a k’ofi,ya k’afa baki zai sha yaji sauk’ar dorina ko ta ina,wurgi yayi da k’ofin hanunsa yafara ihu,Yusuf kuwa tsula mishi dorinar kawai yake,Manal kuwa cikin tsananin tashin hankali tayo waje da ta jiyo ihun Ton G,wajen Yusuf ta nufa da gudu da zumar ta rik’e mishi hannu dan zuwa wanan lokacin,Yusuf ya kwantar dashi akasa yana ta tsulla mishi dorinar,A fusace ya fusge hanunsa daga ruk’on da Manal tayi mishi ya tsula mata itama,wani irin gantsarewa tayi,tayi hanyar waje da gudu Dan dorinar ta gigita ta,da alamu ba ordinary dorina bace har da barkono ajiki,Dan Ton G har fitsari ya saki awando.
[10/14, 6:56 PM] Sadnaf: 🅰 S🅰N🅰DIN GROUP

Written by

💅💅 SADNAF💞

PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_  *P.M.L*

#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com

Ad

_____

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button