A SANADIN GROUP COMPLETE HAUSA NOVEL

A SANADIN GROUP COMPLETE HAUSA NOVEL

Mallama Rabi itama alwala tayi tazo ta tada sallah,tana sallah tana tunanin abinda ya samu Manal hankalinta ya kasa kwanciya sallah dai tayi amma ba anutse ba,tana idarwa ta koma Palo ta zauna tana Jan carbi idonta akan k’ofa dan ta matsu su mustapha su shigo su tambayeta abinda ya faru.

Ana idar da sallar magriba su Mallam Mustapha suka shigo gidan kamar had’in baki Mustapha babangida( mabiyinshi) Abduljabbar Abdullahi da Affan auta,a tabarmar dake shimfid’e a tsakar gida suka zazauna,Affan ya shiga ciki yagaya wa Mallama Rabi su yaya Mustapha sun k’araso,da saurinta ta mik’e tayi waje,suna ganinta suka hau gaisheta,amsawa tayi tana tambayarsu ya iyali,bayan gaishe gaishe da suka yi,Ta hau kora musu jawabi da Manal tazo gida tana ta kuka babu irin tambayar da bata mata ba amma tak’i magana,had’a baki suka yi wajen cewa Manal d’in,Dan sun San duk a gidan itace bata tab’a kawo karar mijinta tayo yaji ba,Mustapha kuwa cewa yayi” tunda kika ga tak’i magana kinsan bata da gaskiya watak’ila laifi tayiwa mijinta ta korota gida,’Mallama Rabi cewa tayi in kuwa hakane da taji kunya abinda ba tayi a da ba sai yanzu zata yi da yayanta da komai ,Affan maza jeka ka kirata kace mata tazo inji yayanku,” Manal tunda tajiyo maganganunsu a tsakar gida hankalinta ya tashi,gabanta fad’uwa ya ringayi dan bata San wane mataki yaya Mustapha zai d’auka akanta ba,ahaka Affan ya shigo ya sameta yace taje inji yaya Mustapha, ya juya ya bar d’akin,Manal hannu ta d’ora aka tana ta shiga uku ta lalace dama da yanda zata iya guduwa da ta gudu tabar gidan dan karshenta yaya Mustapha yace zai maidata gidanta tasan kuwa asirinta yana dab da tonuwa,muryarsa ta jiyo yana ko bazata zo bane,tayi sauri tayi waje,dukansu suna zaune sun zuba mata ido yaya Mustapha fa kuwa ya d’aura fuska alamar babu wasa tuni taji yan hanjin cikinta ya kad’a ta zube akasa,tana gaishe su cikin muryar kuka, ” mai yafaru kika zo gida kina kuka ko kema yajin kika yo kamar yanda kanenki ke yi? Shine tambayar da Mustapha ya jefata dashi,kasa magana tayi jikinta na rawa ta fashe da kuka,wani mugun tsawa Mustapha ya daka mata yace “ba tambayarki nake ba mai ya faru” shiru tayi still ba amsa,Abdullahi ne yaja tsaki yace ” wai kin d’auka ke yarinya ce, dalla ki bud’e baki kiyiwa mutane magana kin wani samu agaba kina kuka” Babangida dayake yafisu sanyi cewa yayi ” Ku bita ahankali dan Allah muji mai ya faru ai bata tab’a zuwa gida da sunan yaji ba,Manal bud’e baki kiyi mana magana mai ya faru” ai kamar zugata yayi ta k’are volume d’in kukanta,Mallama Rabi da hankalinta ya gama tashi da taga irin kukan da Manal take,cewa tayi,” tunda kuka ji ta kasa magana inaga an saketa” had’a baki suka yi wajen cewa ” saki saki fa kikace” to tayi magana mana idan ba sakinta akayi ba” Mallama Rabi tace tana kallon Manal, Wani mugun tsawa Mustapha ya daka mata yace “zaki yi magana ko sai na kwada miki mari”? Kuka Manal ta fashe dashi tana cusa hijabinta a bakinta,Babangida tausayinta ne ya rufeshi yace ” Manal fad’a kuka yi da Yusuf d’in yace ki dawo gida”? Da sauri Manal ta gyad’a kanta,Mustapha a zuciye yace ” ke kuma dayake bakida hankali sai kika taho gida baki bashi hakuri ba,yanzu da su Aneesa ne suka yi haka sai fa ki musu fad’a sokuwa kawai da yaranki da komai kika taho gida wai kinyi fad’a da miji,to mai ya had’aku fad’a mai kika yi mishi”? nan fa gizo ke sakar dan manal kasa magana tayi sai kuka take kamar ranta zai fita, babu irin tambayar da basu mata ba dan har takalmi Mustapha ya jefeta dashi amma tak’i magana,Mallama Rabi girgiza kai tayi tace tunda kuka ga tak’i magana lailai bata da gaskiya,Mustapha kira mana Yusuf d’in muji mai tayi mishi ya korota gida,

Cak manal ta tsayar da kukan da take,ta zubawa wayar dake hanun Mustapha ido,yana fara ringing gabanta ya hau fad’uwa fitsari mai zafi na Neman zubo mata dan a Handsfree yasa.

Yusuf na kwance dafe da kansa a lokacin sai sallati yake dan kansa ma kamar ba ajikinsa ba,ko bud’e ido ba iya yi,yanaji wayarsa na ringing amma ya kasa tashi ya d’auka,sai da aka mishi Miss call biyar bai iya d’agawa ba,adduoi ya yafara yi Dan gani yake kamar mutuwa zai yi,ga tunanin su Hanif da yake yi,yana so ya gansu a gefensa ko ya d’anji sanyi a ransa.

Mustapha d’agowa yayi yace “bai d’aga ba tunda kuka ga haka lailai abinda Manal tayi mishi ba k’aramin abune,” Abduljabbar da rashin d’aga wayar ya masifar b’ata mishi rai a zuciye ya fara magana yana ” to dan Manal ta b’ata mishi rai sai yak’i d’aga waya wanan ai wulak’anci ne ya korota gida sanan mu kirashi ya k’i d’agawa,” Manal kuwa ajiyar zuciya ta ringa saukewa da ta ga Yusuf bai d’aga ba,can kasan zuciyarta kuma tana tunanin irin fushin da Yusuf yayi da ita idan har zai iya ganin wayar Mustapha yayanta yak’i d’agawa lailai tsanar da ya mata ba k’adan bane yanzu tana ji tana gani,zata rabu da Yusuf,kuka ta fashe dashi tana “innalillahi wa inna ilahi rajiun,wayyo Allahna na janyowa kaina ???? S????N????DIN GROUP, Hajja Kaltume kin cuceni kinsa mijina ya tsaneni,Ton G Allah ya isa tsakanina dakai,wayyo Allahna ina zansa kaina ya zan iya rayuwa babu mijina da ‘yayana” su Mustapha sakin baki suka yi suna kallonta,Mallama Rabi ta sulmiyo daga kan kujera tana kallonta Manal kuwa duk batasan a fili tayi maganar ba, Mustapha da maganganun da tayi sun masifar d’aure masa kai d’aurewa yayi yace ” kiyi mana bayani wacce hajja Kaltume?,waye ton g ?wane irin cuta kika yiwa mijinki? Kinsamu a duhu ki fito damu haske, Manal a mugun firgice ta ja da baya dan bata tab’a tunanin a fili tayi maganar ba, Mallama Rabi kuwa suman zaune tayi maganganun Manal na mata yawo a kunne,macece ita mai zurfin tunani ahankali ta had’e duk maganar da Manal tayi tasamu amsar da takeso dan ta tabbatar da amsar tace cikin karayar zuciya”Manal muamalla kike da wani bayan da aurenki”? Ba Manal ba duk wayanda suke Palon sai da gabansu ya fad’i dan sun girgiza da jin abinda Mallama Rabin tace, Manal jikinta ne ya d’auki mugun rawa,ta zaro ido tana kallon Mallama Rabi,Mustapha yanayin Manal da ya gani ne yasa yafara gaskata maganar Mallama Rabi wani mugun tsawa ya d’aka mata yace ” Manal yanzu da aurenki kike muamalla da wani awaje, innalillahi wa inna ilahi rajiun,Manal kuwa da ta ga bata da option kuka ta fashe dashi tana “wlh Sharrin shaidan ne ba halina bane,dan Allah Ku fahimceni ban tab’a aikata zina da aurena ba wlh Allah duk abinda nake yi a iya waya ne,Ku taimaka min kar na rasa raina inasan mijina” Mallama Rabi wani irin kukan kura tayi tayi kan Manal ta rufeta da duka tana kuka tana ” kin cucemu kin cuci kanki,idan aka ce min zakiyi haka karya tawa zanyi,kinsan mai kika yi kuwa,na Shiga uku ni Rabi mai zan gani haka,Manal ina iliminki da yayanki da komai,kike muamalla da wani namijin a waje, Mustapha zuba mata ido kawai yayi jikinsa na rawa su Babangida kuwa sabida shock d’in abinda ta fad’a sun kasa koda kwakwaran motsi, Mallama Rabi gajiya tayi da dukanta ta koma gefe tana kuka,Mustapha kuwa da zuciyarsa kamar ta fad’o kasa wani irin yunkurawa yayi ya cakumo Manal ya hau dukanta su babangida da Abdullahi ganin ta daina motsi ne kwata kwata yasa suka mik’e da gudu suka rik’e Mustapha, Affan yayi kanta da gudu yana jijjigata, d’agowa yayi yana “shikenan kun kasheta,Aunty Manal ki tashi dan Allah”, Babangida shima jijjigata ya fara yi yaga bata motsi,Mallama Rabi kuwa ganin da tayi da gaske bata motsi ne yasa tayi kanta da gudu,itama tana jijjigata,hankali a tashe tace Affan ya deb’o ruwa,affan a guje ya deb’o ruwan ya kwara mata nan ma bata motsa ba,Mallama Rabi zubewa tayi akasa a sume,Mustapha kanta yayi da gudu shima yana jijigata,ganin itama bata motsi ne yasa ya kinkimeta yayi waje, Abduljabbar ya kinkimi Manal yabi bayansa a mota suka zubesu suka nufi asibiti,tashin hankali iya tashin hankali sun ganshi aranar.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25Next page

Leave a Reply

Back to top button