A SANADIN GROUP COMPLETE HAUSA NOVEL

A SANADIN GROUP COMPLETE HAUSA NOVEL

Yusuf kuwa da taimakon adduar da ya ringayi ya samu kansa ya lafa mishi,ahankali ya mik’e daga kwancen da yake,ya d’auki wayarsa ya duba miss call d’in baban yaya yagani,dan da sunan da yayi saving number Mustapha kenan,ajiye wayar yayi yana tunanin mai zai ce mishi in ya tambayeshi mai ya had’a shi da Manal,Har ga Allah yana jin kunya da nauyinsu, bazai iya fad’a musu abinda Manal tayi masa ba dan yasan Manal ma bazata iya fad’a ba,yanzu kuma idan bai fad’a musu ba suka bashi hakuri suka ce Manal ta dawo fa,Sam bazai iya zama da Manal ba, dan babu wacce ya tsana kamar ta,ahaka ya ringa tunane tunane ganin bashine mafita a gareshi ba yasa ya mik’e ya chanja kayan jikinsa ya d’auki hanyar gidansu Hindatu dan ya d’auko su Hanif kasancewar babu nisa sosai tsakanin gidansu Da gidansu Hindatun ne yasa ya tafi a k’afa,yana zuwa ya aika a kira Hindatu,minti biyu da aikawa sai gashi ta fito hanunta rik’e da Hanun Taufiqa tana ta sauke ajiyar zuciya da alama kuka tayi,tana ganin Yusuf ta saki hanun Hindatu ta tafi da gudu ta rungumeshi shima rungumetan yayi ya d’aga ta sama ya juya baya dan kar Hindatu taga hawayen dake zubo mishi,ahaka su Hanif suka fito suka same shi,yayi gaba suka bishi a baya, still lokacin hawaye na zubo mishi dan yana mugun tausayin yayansa,tun a hanya taufiqa ta fara tambayarsa “ina Momy”? Kamar had’in baki Saleem da Hanif ma suka hau tambayarshi,Yusuf kasa magana yayi dan Indai yayi magana sai ya fallasa kansa,a haka suka k’arasa gidan suna zuwa Palo ya sauke Taufiqa Su ka nufi d’akin Manal da gudu suna ” MoMy mun dawo” Yusuf kuwa yayi hanyar d’akinsa da sauri yana share hawaye.
[10/14, 6:56 PM] Sadnaf: ???? S????N????DIN GROUP

Written by

???????? SADNAF????

PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_  *P.M.L*

#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com

A short novel based on true life story

Page 45-50

WANAN SHAFIN NAKI NE KE KADAI FIRDAUSI SODANGI THANKS FOR YOUR LOVE AND SUPPORT????????????????????????????????????

Su Mustapha na isa asibitin b’angaren emergency akayi dasu,sai kai da kawowa suke hankalinsu gabad’aya a tashe,Affan har da kuka, bayan minti 30 da aka shigar da su wata nurse ta fito daga d’akin tace musu Mallama Rabi ta farka yanzu haka ma idonta biyu,d’ayar kuma tashin hankalin da buguwar zuciya ne yasa tayi dogon suma nan da awa biyu zata farka, ajiyar zuciya suka ringa saukewa d’aya bayan d’aya suna godewa Allah,Mustapha ne yayi saurin cewa zasu iya shiga suka mahaifiyar tasu,Nurse d’in girgiza musu kai tayi tace ba yanzu ba su bari nan da anjima sai su shiga.

Babangida ce mata tayi to babu matsala,tana tafiya ya kalli Mustapha yace mishi mai zai hana ya k’ara kiran Yusuf awaya sabida gwara yasan Manal tana asibiti ga kuma halin da take ciki,Mustapha ce mishi yayi bazai iya kiransa ba yana jin nauyi da kunyar abinda Manal tayi watak’ila ma ya saketa sani ne basu yi ba tunda ba kowane Namiji ne zai ga matarsa taci amanarsa ba bai saketa ba,cikin karayar zuciya Abdullahi yace,ai Manal tace a iya waya take muamalla da wani bata kai ga cin amanarsa ba,wani mugun kallo Mustapha ya mishi,yace mishi yasani ko karya Manal d’in Take yi kamata Yusuf yayi dawani,idan ma ta waya ne ai taci amanarsa, shi bai tab’a tunanin Manal zata yi haka ba da hankalinta da tunaninta,da iliminta,ahaka suka cigaba da maida zance inda a k’arshe suka yanke Babangida zaije gidan Yusuf da kansa ya gaya mishi duk abinda ya faru,ya kuma fad’a musu ya saketa ne ko bai saketa ba.

Yusuf kuwa yana shiga d’akinsa ya zauna a gefen gado yana tunanin abinda zai cewa yaransa in sun tambayeshi ina mamansu,Taufiqa ce ta shigo d’akin kamar an jefota su Hanif suka biyo bayanta,d’aura fuska yayi yana kallonsu,take Hanif da Saleem suka juya suka koma Taufiqa kuwa da yake bata da wayo cewa tayi ” Daddy ina Momy ban ganta a d’akinta ba”? Kau da kansa yayi yace ” Tayi Tafiya”? Taufiqa uban yan tambaya wani tambayar take shirin k’ara jefo mishi ya daka mata tsawa yace ta tafi ta d’auko Home work d’inta ya koya mata,aguje tabar d’akin tana kuka,share hawayen daya zubo mishi yayi dan idan ba haka yayi musu ba ahaka zasu sa shi agaba suna mishi tambayoyi shi kuwa tausayinsu zai iya sa yayi kuka agabansu, mik’ewa ya fita Palo,suna zaune su uku sunyi jungum jungum litattafansu a baje agabansu,kowane da pencil a hanunsa amma ba rubutu suke ba,tausayin Taufiqa ne ya rufeshi da yaga yanda hawaye ke zubo mata tana gogewa,sai kace wasu marayu,wai bama mutuwa Mahaifiyarsu tayi ba ,rabuwa kawai su kayi na kwana d’aya suka shiga wanan halin,ina ga mutuwa tayi,(lailai uwa dadi gareta in ka rasa uwa ka rasa wani b’angare na rayuwarka Allah ya jikan iyayenmu mata da suka Riga mu gidan gaskiya,wayanda kuma suke rayye Allah ya ara musu tsawon rai,wayanda kaddara tasa suka rabu da mazajensu Allah ubangiji ya daidata su,Dan kowane d’a zai so ya taso agaban mahaifiyarsa,da mahaifinsa)

K’arasawa yayi inda suke azaune ya zauna a kusa da Taufiqa,ya d’agata ya d’aurata akan cinyarsa ya goge mata hawayen fuskarta yace ” Ku kwantar da hankalinku Momynku tayi Tafiya zata dawo nan da kwana biyar tace in ce muku in zata dawo zata taho muku da abinda kukeso” Allah sarki yara tuni suka hau murna suna tsalle,Yusuf shi kuma farincikin da yaga suna yi yasa yaji sanyi a zuciyarsa,Hanif dayake yafisu wayo cewa yayi a kira musu Mommy awaya, Yusuf da wayo ya share maganar Yusuf yace su Matso da Home work d’insu ya koya musu,ahaka ya koya musu Home work d’insu yana jansu da wasa,k’arfe Tara nayi yace su tafi d’akinsa su kwanta,da Kansa ya d’auki Taufiqa ya kaita d’akinsa sai daya tabbatar barci ya d’aukesu ya tofesu da addua ya sungumi wayarsa ,da ta Ton G da ta Manal yayi waje,a doguwar kujera ya zauna ya bud’e wayar Manal data ya kuna ya bud’e watsapp d’inta aikuwa nan da nan messages suka fara shigowa rututu, sai da ya bari messages sun gama shigowa ya fara bud’ewa d’aya bayan d’aya,group d’in Manyan mata hark’a oneyafara bud’ewa ahankali yafari bin chatting d’insu yana karantawa tsantsar Batsa kawai ake yi a group d’in,videos da yaga an tuturo da yawa ya gwada bud’e guda d’aya abinda yagani ne yayi mutuk’ar girgiza shi,da Sauri ya rufe videon yana sallati,mamakin abinda ya gani ne ya rufeshi yafara magana shi kadai “yanzu acikin irin wanan grp d’in manal take subhanallahi astagfurullah astagafrullah” abinda Yususf yayi ta Nana tawa kenan.

Idonsa ne ya sauka akan group d’in MANYAN MATA HARK’A ZALLA kara nanata sunan grp d’in yayi a fili, ya bud’e group d’in, messages sun fi k’arfin dubu d’aya ahankali yafara bin chatting d’insu yana karantawa,a irin hirar da suke ne yasa ya gane a grp d’in ake had’a matan aure da samari,sabida akwai wacce tace ita Baby boy d’inta bashida zafi yanzu jiya sau biyu kawai yayi mata allura duk uban kud’in nan da take kashe masa Hajja kaltume ta taimaka ta had’a ta da wani kafin mijinta ya dawo, girgiza kai Yusuf ya ringa yi hawaye na zubo mishi,wannan wane irin masifa ne ,wanan wane irin balai ne,matan aure ke aikata zina da aurensu,su ka kuma fito suna fada ya zame musu tamkar abun burgewa,bama su d’auka zunubi suke aikatawa ba,”innalillahi wa inna ilahi rajiun,mu kuma tamu jarrabtar kenan, muna can muna Neman halal matan mu na nan nacin amanarmu,”bude grp d’in yayi Dan yaga adadin members d’in dake grp d’in, su ashirin ne cif cif admin guda d’aya ganin Hajja Kaltume ce grp admin d’in ne yasa ya tuna maganar Ton G,da sauri ya rufe grp d’in, aikuwa sai ga messages d’in Hajja kaltume na shigowa ,bud’ewa yayi yafara karanta abinda tace,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25Next page

Leave a Reply

Back to top button