A SANADIN GROUP COMPLETE HAUSA NOVEL

A SANADIN GROUP COMPLETE HAUSA NOVEL

Page 50_55

WANAN SHAFIN NAKU NE MASOYANA ABUN ALFAHARINA INA MUTUK’AR JI DAKU,FHAREEDAT SWREERY,HAUWA SARAUTA, MAIMUNA NIGER,ALLAH YA D’AUKA KA KU YA BIYA MUKU BUKATUNKU NA ALHERI????????????????????????????????????????????????????????

BAN MANTA DAKU BA

*AISHA ALI *GARKUWA*
MEELA ADEEL
SHOLINGAYE
MINASH
MAMAN FADEEL
MASHKURATA
AUNTY MAMY
AMNOOR
MARYAM I GITAL

KUNA RAINA SOSAI ALLAH YA BARMU TARE????????????????????????????

Sunkuyar dakai tayi
Hawaye na zubo mata,Mallama Rabi ido dai ta zuba mata bata ce komai ba,har yanzu gani take kamar mafarki take yi, Manal bazata tab’a iya aikata haka ba, Manal d’aurewa tayi tafara magana “Umma kuyi hakuri Kuyi yafemin sharrin shaidan ne babu yanda banso na k’aucewa Hajja Kaltume amma sai da tayi nassara akaina nayi dana sanin biyewa San zuciyata Umma,nayi nadamar abinda na aikata ni kadai nasan mai nake ji a zuciyata Umma,kuyi Hakuri Ku yafemin,ban tab’a aikata zina ba,waya kawai na keyi da wani,Daddyn Hanif ya kamani, Umma nasan nayi laifi na cancanci kuyi min kowane irin hukunci amma Umma kuyimin adalci karku manta kunsan halina Allah ya Riga ya kaddara sai hakan ta faru,” Tunda ta fara magana Mallama Rabi ke kuka tana kallonta jin abinda tace ne yasa ta katse ta tace” babu wata Kaddara Manal San zuciyarki dai ta kai ta Baro ko,idan bera da sata ai daddawa ma nada wari,ina mamakin mutane da zasu yi Abu Dan San zuciyarsu daga baya suzo suna cewa kaddara ce Allah ya Riga ya hukunta hakan zai faru Sam ban yarda da wanan zancen ba dan babu yanda Allah zai jarrabceku ku aikata mumunan Abu da aurenku,domin Allah ma d’aukakin sarki ba azzalumun bawa bane,Kune dai kuka d’orawa kanku masifa da San zuciya,shaidan kuwa yana daga gefe yana kad’a muku ganga, idan ba haka ba Manal ina ke ina huld’a dawani awaya fisbillahi,da iliminki da tunaninki,mai Mijinki ya rage ki dashi,wlh ko a mafarki akace min zakiyi haka karyatawa zanyi,aganina yau ko fad’uwa nayi na mutu,ke xaki zamto tamkar uwa awajensu Aneesa duk wani Abu da kike ganin sunyi ba daidai ba ke zaki musu fad’a ki d’ora su ahanya sai gashi ke da kanki kinyi abinda ko ameera bana jin zata yi abinda kika yi “Sai da suka kai Ukun dare Mallama Rabi na mata fad’a da Naseeha,Manal jikinta ne ya k’ara sanyi nadama da da nasani na kuma rufeta,ji take Dama hanun agogo ya koma baya da ta gyara kuskurenta amma ina aikin gama ya Riga da ya gama,kuka taci ta gode Allah,a k’arshe ta mik’e ta nufi band’aki ta d’aura alwala tazo ta tada sallah,addu’a ta rin ga yi sosai tana Neman yafiyar Allah akan abinda ta aikata,ta ringa rok’on Allah yasa kar Yusuf ya saketa,Allah ya huci zuciyarsa ya yafe mata ko Dan ‘yayanta aranar ko sau d’aya barci bai yi gingin d’aukarta ba har aka kira sallahr asuba tayi sallah tana zaune akan sallaya tana Jan carbi,Mallama Rabi kuwa tsantsar tausayin Manal ne yasa ta ringa share hawaye akai akai.

B’angaren Yusuf ma kuwa ranar barci bai ga idonsa ba Dan idonsa na kan agogo ya kagu garin Allah ya waye, su Hajja Kaltume su iso yaci ubansu,Allah yasan da ace Hajja Kaltume ba matar aure bace baisan wane irin mataki zai d’auka akanta ba Dan itace silar komai,amma duk da haka baya d’aukarta a matar aure Dan a karuwa ya d’auketa sai ya ci ubanta fiye da tunaninta kuma a k’arshe ya had’a ta da ‘yan hisba,kiraye kirayen Sallar asuba da yafara jiyo wane yasa ya mik’e ya nufi band’aki ya d’aura alwala yazo ya tada sallah,sai da ya dade yana addua kafin ya shafa,Dan massalaci yaso zuwa amma sabida yara yafasa zuwa massalacin,bayan ya idar da sallah,Kitchen ya nufa ya d’orawa su Hanif breakfast, daga nan ya wuce d’akinsa,tashinsu yayi da su tashi suyi sallah,suka mik’e gabad’ayansu da adduar tashi daga barci,d’aya bayan d’aya suka ringa shiga band’akin suna d’aura alwala yana zaune a gefen gado yana kallonsu, Haneef ne yaja su sallar,sallah sukeyi cike da nutsuwa kamar wasu manya taufiqa ma tafi bashi mamaki Dan yanda take sallar kamar wata babba bazaka tab’a yarda ‘yar shekara hud’u bace,mamaki bai gama rufeshi ba sai bayan da sukayi sallama yaga dukansu sun koma sun yi sujjadar shukur,lumshe idonsa yayi Hawaye na zubo mishi Dan yasan wanan duk koyarwar Manal ce,Manal tayiwa yaransa tarbiyya sosai da ba ya shak’ar shiga dasu ko ina yaransa suna da ilimi addini sosai da duk wani taro ko gasa idan za’ayi ‘yayansa ne akan gaba,su hukumar makaranta kan zab’a Dan bai zai iya fad’ar sau nawa yaransa kan ciyo gasa ba ta fanin addini,kuma duk Manal ce take jajircewa wajen ganin sunyi karatu sun kuma iya,amma abun mamaki Manal d’ince ta tak’e duk iliminta da saninta ta keta alfarmar da martabar aure,tasan duk abinda take yi haramune ta biye wa San zuciyarta,muryar Hanif ce ta katse matsa tunanin da yake yi,Suratul duha yake karantawa cikin zazzakar muryarsa Su Saleem nabinsa,ahaka ya shagala da kallonsu sai da ya tuna da ya d’ora abinci ya mik’e da sauri ya nufi kitchen, atakaice shi ya shirya Taufiqa da kansa su Hanif kuma suka shirya dakansu,suna cikin breakfast Hindatu ta shigo gidan ta gaishe shi ta fara aikace aikacenta,ganin suna breakfast ne yasa shima ya nufi d’akinsa shima yayi wanka ya shirya dan ya mik’a su makaranta,yana fitowa ya tarar da sun gama breakfast duk sun dau lunch box d’insu suna jiransa,umarni ya musu da su wuce su tafi,bayan sun gama ficewa daga palon ya kalli k’araso

dake mopping yace mata ta shirya kayansu Hanif a cikin akwati kafin ya dawo dan daga yau gidansu zasu koma wajen mahaifiyarshi ,Manal tayi tafiya sai ta dawo suma yaran zasu dawo,Dan haka daga yau kar ta sake zuwa tabari idan Manal ta dawo sai itama ta dawo,Hindatu to tace mishi tana k’ok’arin nufar d’akinsu Hanif Dan tafara had’a musu kayansu,akasan ranta kuma tana tunanin babu wani tafiya da Manal tayi fad’a suka yi da Yusuf dan jiya ai tajiyo ihun Manal da alama kuma dukanta yake.

Yana saukesu a makaranta ya koma gida, awaje yayi parking d’in motarsa ya shiga ciki,har ya kusa shiga palon ya tuna da Ton G juyawa yayi ya nufi boys quarters,a kwance ya samu Ton G yana ta birgima ya rik’e cikinsa yana ta ihu bai ma San Yusuf ya shigo d’akin ba,tsawa Yusuf ya daka mishi,yana “kai mai haka zaka cikawa mutane kunne da ihu,” da sauri Ton g ya mik’e yana rik’e cikinsa Ton g gaishe shi ya fara yi hawaye na zubo mishi,Yusuf bai amsa ba ya k’ara daka mishi wani tsawan yana tambayarshi mai yafaru yake wa mutane ihu, cikin tsananin tsoro da rawar baki Ton G yace ” Alhaji cikina ne yake ciwo wlh yunwa nake ji” Yusuf wani mugun tsaki yayi yace “shi yasa ka cikawa mutane gida da ihu ai kadan ka gani sai yunwa ta kasheka ma tukuna ba ka iya bin matan mutane ba,” kuka Ton G ya k’ara fashewa dashi yana “Dan Allah ka taimaka min wlh yunwa nake ji kamar na mutu” Yusuf tsaki yayi ya bar d’akin, ya nufi b’angarensa wayar ton g ya d’auko da ta Manal ya nufi kitchen ya juye sauran indomie daya dafa wa su Hanif ya koma boys quarter wajen Ton G,
Ton g yana ganinsa da plate a hannu yayi sauri ya gyara zamansa Yusuf kuwa ya zuba mishi wani harara ya ajiye abincin a gefensa yace ” maza kira min wanan dabobbin abokanan nan naka naji ko sun taho” jiki na rawa Ton g ya k’arbi wayar ya kira Bad boy,Yusuf yace yasa a Handsfree ” a Handsfree yasa adai dai lokacin da wayar tafara ringing,d’agawa su Bad boy suka yi da sauri Dan sun Dade suna kiran layin Ton G su ce mishi suna hanya Dan sun ma wuce Kaduna Dan da asuba suka taho,Ton g tambayarsu yayi ko sun taho anan suka ce mishi ai sun Dade da tahowa ko sallar asuba ma basuyi ba suka taho Dan haka yacewa Sugar Mama d’insa ta tanada musu breakfast kafin su iso,to Ton G yace ya kashe wayar yana kyalkyala dariya,Yusuf mamaki ne ya rufeshi daya ga Ton G na dariya ce masa yayi mai yasa yake dariya, Ton g wani dariyar ya k’ara kyalkyalewa dashi yace ” Alhaji dariya nake yi Dan su Bad boy basu San bulala zasu zo su sha ba ,har suna a ajiye musu breakfast,Alhaji Dan Allah ka taimaka min yanda ka cire min hak’oran gaba suma ka cire musu wlh duk sun fini iskanci gwara” maganarsa ce ta mak’ale a fatar bakinsa sakamakon wani bahagon mari da Yusuf ya d’aukeshi da ita, yace “Dan ubanka har kana da sararin da zaka yi dariya,ka daina dariya Dan tare zan k’ara dukanka da abokanan naka,Dan a duniya babu Wanda na tsana sama dakai shege Dan iska” Yusuf k’arbe wayar yayi daga hanunsa yabar d’akin yana zagin Ton g, ton g kuwa yana ganin ya bar d’akin ya janyo plate d’in indomie yafara ci loma uku yayiwa indomie ya cinye,yana gama ci ya fashe da kuka yana ya shiga uku ya lalace yau da kansa ya kawo kansa gidan da za a kashe shi da ransa, Allah ya isa ya ringa jawa Hajja Kaltume yana tsine mata dan ita ta janyo mishi komai dan ita ta ringa zugashi akan yazo.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25Next page

Leave a Reply

Back to top button