A SANADIN GROUP COMPLETE HAUSA NOVEL

A SANADIN GROUP COMPLETE HAUSA NOVEL

Yusuf yana barin wajen Ton G akwatin kayansu Hanif ya kinkima yayi waje,abayan boot yasa akwatin ya koma ciki yacewa Hindatu ta jirashi ya dawo akwai aikin da zai sata kafin ta tafi, daga haka ya juya ya koma cikin motarsa ya d’au hanyar gidansu dake Lameedo cresent,tafiyar ‘yan mintuna ne ya kaishi gidan,awaje yayi parking ya kwankwasa gate d’in,maigadi ne ya leko dan yaga waye ganin Yusuf ne yasa ya bud’e k’ofar cikin rawar jiki ya na mishi sannu zuwa,amsawa Yusuf yayi yana shigewa ciki,Tamfatsetsen gida ne daya amsa sunansa gida dan Mahaifin Yusuf shahararren mai kud’i ne na bugawa a jarida, duk da kud’in mahaifinsa hakan bai sa ya dogara da kud’in mahaifinsa ba duk da shi kadai ne namiji,Neman na kansa yake tukuru,babu irin fad’an da Mahaifinsa baiyi ba akan ya ajiye aikin da yake yi yazo ya rik’e mishi wasu companies d’insa Yusuf yak’i dan yafi so shima ya Tara nasa yasan zafin nema.

A katon Palo dake saman gidan ya samu mahaifiyarsa a zaune da wasu mata a zaune dagani mabukata ne dakanzo Neman taimako wajenta,sallamar da yayi ne ya katse mata maganar da take yi,ta juyo tana amsa sallamar cikin tsananin mamakin ganinsa dan tasan yau alhamis,duk ranar sunday yake zuwa gaisheta,da sauri matan nan suka mik’e suka yi waje,Hajiya Munawara tace ” aa Yusuf yau Kaine a gari lafiya kuwa naga yau alhamis ba weekends ba”? Murmushi Yusuf yayi yana cire Takalmin k’afarsa tsugunawa yayi har kasa yana gaisheta, amsawa Hajiya Munawara tayi tana nazarin fuskarsa dan taga idonsa a d’an kumbure ” Lafiya kuwa Yusuf na ganka haka? Yaushse ka dawo”? Hajiya Munawara tace tana k’ara nazarin fuskarsa.

Sunkuyar da kai Yusuf yayi yana tunanin abinda zai gaya mata dan gaskiya bazai iya gaya mata gaskiyar abinda ya faru ba,kirkirar murmushi yayi yace
“Ba komai hajiya kawai zuwa nayi jiya ayyuka suka dan ragu shine nace bari nazo kawai”

Hajiya Munawarra kallonsa kawai take yi dan bata yarda da abinda yace ba tana dai tunanin wani abun yake b’oye mata cewa tayi ” lailai ka kyauta yasu Manal d’in ya yaran”

Tofa nan gizo ke sak’ar dan Yusuf bai San mai zai ce mata ba dan Hajiyarsa na masifar San Manal, indai zai zo ya gaisheta sai tayi mishi naseeha da ya rik’e manal dakyau dan dabi’un Manal na mutuk’ar burgeta,most especially ta fanin addini,dan idan su Hanif suka zo gaisheta har wani murna take yi idan taga yanda suke karatun Qurani,d’aurewa yayi yace ” Hajiya Abinda ya kawoni kenan mun samu sabani da Manal tana gidansu shi yasa na kawo kayan su Hanif su zauna anan kafin komai ya daidata,” tunda yafara magana Hajiya Munawarra ta saki baki tana kallonsa cikin tsananin mamaki tace ” mai kace kunsamu sabani da Manal tana gidansu kasan mai kake cewa kuwa”? Shiru Yusuf yayi ya k’ara sunkuyar dakansa ” ina tambayarka Mai ha had’aka da Manal d’in da har ka kasa hakuri sai da ka koreta gidansu,shekara goma sha uku da aure,da yara uku babu kunya babu tsoron Allah ka kora Manal gidansu mai tayi maka haka”?

“Hajiya kiyi Hakuri bazan iya fad’a miki abinda ya faru ba,kema kinsan tunda na aureta hakan bata tab’a faruwa ba Laifiin da ta min ya wuce tunanin mutum bazan iya hakuri na cigaba da zama da ita ba tana gidansu”

Yusuf yace yana mai kau da kansa dan ji yake kamar yanzu abun ya faru

“Yusuf kenan nima ban matsa ma lailai sai ka fad’amin abinda ya had’aka da Manal ba amma aganina duk abinda zata yi maka bai kamata ka koreta gidansu ba hakuri ya kamata kayi ko dan yaranta,yanzu aganinka korata da kayi gida shine mafita, duk da bansan mai ya had’aku ba Manal bata cancanci haka daga wajenka ba yarinya mai hankali da tunani, hak’uri zaka yi dan aure ya gaji haka dole wataran ku samu sabani dan haka Nima bana bukatar naji mai ya had’aku a matsayina na mahaifiyarka ina mai baka hakuri,ka k’ara hakuri ka dubi yaranka ka tausaya musu kaje Ku daidaita ta koma d’akinta”

Shiru Yusuf yayi dan Sam bazai iya maida Manal d’akinta ba yanzu ko da zai maidata ba yanzu ba “Hajiya dan Allah kiyi hakuri ban tab’a bijire miki ba bana fatan kuma na bijire miki zan mayar da Manal d’akinta ba yanzu ba,sai ta kara hankali tayi nadamar abinda tayi min ai yaran nawa na duba shi yasa ban saketa ba ,amma badan haka ba Manal abinda tayi min ya cancanci in saketa,kawai alfarma d’aya nake nema awajenki dan Allah su Hanif su zauna awajenki suringa zuwa makaranta daga nan,duk weekends zan ringa zuwa ina d’aukarsu”

Hajiya Munawarra zuba mishi ido tayi tana mamakin maganganunsa can kasan zuciyarta kuma tana tunanin mai ya had’asu haka,tasan Yusuf na masifar San Manal,lailai tunda Yusuf ya iya d’aukar irin wanan matakin abinda Manal tayi mishi ba k’aramin abu bane, amma zata so tasan mai ya had’asu haka ganin ko da ta matsa mishi ba gaya mata zai yi ba yasa tace “to shikenan dafatan dai bazaka d’au tsawon lokaci ba,dan gwara Ku daidaita tun wuri in ba haka ba dakaina zan maidata d’akinta dan yara ya kamata ma ka duba,” Yusuf bai tab’a tunanin komai zai zo mishi da sauki haka ba,murmushi yayi yace “Insha Allahu Hajiya ni zan tafi dan Allah 12:30 nayi kisa driver ya d’auko Taufiqa ya jira su Haneef ma kawai sai su taho gabad’aya dan ni daga nan Abuja zan wuce, Hajiya Munawarra cewa tayi ” babu matsala kaci abinci kuwa”? Girgiza mata kai yayi yace “Naci” Hajiya Munawarra cewa tayi “ban yarda kaci abinci ba wuce dinning ka zuba abinci kaci”,Yusuf yunwar yake ji amma sabida yanasan yaci ubansu Ton G yace mata dagaske a koshe yake,agurguje ya mata sallama ya tafi dan yana tunanin zuwa yanzu yaci ace abokanan Ton G sun k’araso

Ai kuwa yana shiga motar yaga misscalls d’insu rututu,Hajja Kaltume ma ta mishi 10 misscall,da sauri ya duba wayar Manal yaga misscalls d’in Hajja Kaltume, harda text message,bud’ewa yayi ya karanta

Momyn Hanif ina ta kiranki tundazu baki d’auka ba na kira ma layin ton g bai d’aga ba wane irin soyayya kuka sha haka kuka kasa d’aga wayar nafi minti arbain da sauka a kano,Ina k&tsuit hotel ki turomin lambarsa dan Allah ina jiranki

Murmushi jin dadi Yusuf yayi dan komai na tafiya mishi dai dai abokanan Ton G sun k’araso lokaci d’aya da Hajja Kaltume, reply yayi mata da

kiyi hakuri banji bane,barci mai nauyi ne ya d’aukemu wlh jiya bamu samu barci ba kice har kin iso,ki fad’amin room number da kike na kawo shi da kai na dan nafad’a miki boy d’in nawa d’an madara ne

Hajja Kaltume datayi rashe rashe akan gado tana kwankwad’an maganin mata text d’in na shiga wayarta ta saki murmushi ta mayar da reply kamar haka

Momyn Hanif bakida dama,duk kinsa na zaku naga Wanan Boy d’in naki, ina room 13 down floor,dan kinsan yafi ko ina girma,dubu d’ari da hamsin na kama d’akin dan tunda naji kince aje bota ne bai dace in kama mana k’aramin guri ba ,dan Allah kiyi sauri ki kawo min shi a gwiwa nake dan ko barcin kirki ban yi ba sabida dokin ganinsa

Yusuf reply ya mata yana dariyar mugunta

an gama Hajiya admin yanzu zanyi wanka na d’aukoshi sai kin gamu

A guje ya ja motar ya nufi gida dan ya bawa Ton G wayar ya kira su Bad boy yaji suna ina,yana isa gidan ko parking bai gama yi ba ya fito daga motar aguje,ya nufi boys quarter, Ton G agigice ya tashi daya ga yanda Yusuf ya fad’o d’akin mik’a mishi wayar yayi yana haki yace “maza kira ‘yan iskan abokanan nan naka naji ko sun k’araso kiran daya shigo wayar ne ya ya katse masa maganarsa Bad boy ke kiran Ton G dasauri Yusuf ya d’aga yasa a Handsfree,wani gundumemen ashar bad boy yayi yace ” dan ubanka ina ka ajiye waya tun dazu muna kiranka,kasan mun kusa awa d’aya da isowa kuwa,kabarmu a shanye a bakin titi ga yunwa dan wulakanci ana ta kiranka baka d’auka ba dalla Mallam turo mana address,”dariyar mugunta da ya tahowa Ton G ya had’iye Yusuf kuwa ya ja da baya yayi kasa da murya ya fara yiwa Ton G kwatance ya fad’a musu, yana gama gaya mishi ya kashe wayar,kasa dai had’iye dariyar yayi sai da yayi,Yusuf k’arbe wayar daga Hanunsa ya zuba mishi mugun harara ya fice da sauri,d’akinsa ya nufa ya canja kayansa zuwa 3 quarter da armless,ya d’auko wata sharb’ebiyar dorina ya ajiye agefen gado,fito wa yayi daga d’akin, Hindatu dake zaune a Palo yace wa zata shigo mishi da wasu,ta d’auko musu lemo da ruwa tamkar dai jiya in ta ajiye ta juya ta tafi gida,to tace mishi ya koma d’aki yana zaro wasu dorinar,bayan minti goma sha biyar sai ga Bad boy na kira da sauri Yusuf ya d’aga Bad boy yace ” gamu nan a bakin gate d’in gidan” katse wayar Yusuf yayi yafito Palo,yacewa Hindatu suna waje taje ta shigo dasu, ya juya ya koma d’akin,yafara had’a sharba sharba dorinar ya had’esu waje d’aya ya d’aure.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25Next page

Leave a Reply

Back to top button