A SANADIN GROUP COMPLETE HAUSA NOVEL
Hindatu har Palo tayiwa bad boy,dan auta, Dee Boy da Badest one iso,suka zauna suna kalle kalle,tsugunawa tayi dan ta zuba musu lemon bad boy yayi sauri ya k’arbe lemon dan gani yake tana b’ata musu lokaci dan ba k’aramin yunwa da kishi ruwa suke ji ba, lemon ya k’afa abakinsa yafara sha,su dee boy na ganin haka suma suka susungumi lemon suka k’afa kai,Hindatu kuwa hakan da tagani ne yasa ta mik’e tayi hanyar d’akin Manal,ta na d’aga labulen d’akin Yusuf yace tace musu Hajiyar tana zuwa,Hindatu fitowa tayi ta fad’a musu ta fice waje, dan autan kalle kalle ya fara yi yana ” Kai guys da alama matar nan fa mijinta mai kud’i ne kunga dukiya kuwa,” dee boy ne ya k’arbe zancen,yana “kai dalla zauna tukuna ni yunwa nake ji wallahi, wai ina ton g d’in ne dan iska yasan mun k’araso yaki fitowa,” Bad boy tsaki yayi yace shege bari na kirashi, Yusuf yana ganin kiran bad boy ya fito daga d’akin hard’e hannayensa yayi yana kallonsu,’yan kuci kucin yara ne dan basu fi 21/22 ba har gwara Ton g akansu, duk sun shagala suna kalle kalle basu lura da Yusuf dake kallonsu ba,Yusuf cikin ya koma ya d’auko dorinar ya b’oye abayansa ya nufi inda,suke gyaran muryar da yayi ne yasa suka juyo gabad’aya suna kallon Yusuf a tare suka mik’e gabansu na fad’uwa dan Yusuf irin giant dinan ne ga tsayi,in ba saninsa kayi ba tunani zaka yi soldier ne,d’aura fuska Yusuf yayi yace musu ” Lafiya wa kuke nema”? Wani irin murd’awa cikinsu yayi jikinsu ya d’au rawa,dan Ba k’aramin tsoron Yusuf suka ji ya rufesu ba,wani mugun tsawa Yusuf ya daka musu yana” nace uban me kuke yi a gidana wa kuke nema”? Tuni suka zube akasa suka fara kinkina wanan ya kalli wanan,wanan ya kalli wanan,Yusuf cikin tsananin fushi ya k’arasa inda suke yace ” tunda bazaku yi magana ba bari na ci ubanku zaku bud’e baki kuyi magana,zaro dorinar yayi daga bayansa ya fara lapta musu ihu suka suna Neman taimako in wani ya mik’e yana k’ok’arin guduwa sai Yusuf ya kamoshi dukansu kawai Yusuf yake yi kamar an aiko shi sai da yayi musu jinajina dan autan har fitsari ya saki a wando ya koma gefe yana sauke ajiyar zuciya,Su Bad boy kuwa sabida tsabar wahala sun ma kasa kuka,cikin murtuk’ewar Fuska Yusuf yace ” zaku gayamin abinda kuka zo nema a gidana ko kuwa”? Da sauri suka had’a baki suka fara ce mishi abokinsu Ton G ne yace suzo,tambaya Yusuf ya wurga musu yace ” waye ton g mai yace kuzo kuyi
Zare ido suka fara yi suna kallon juna dan basu San mai zasu cewa Yusuf ya kawo su gidan ba,Yusuf ganin babu mai shirin magana a cikinsu ne yasa yace ” tunda ba zakuyi magana ba bari na ci ubanku zakuyi magana ne dorinar ya d’auka ya k’ara rufesu da duka suka ringa ihu suna zasu fad’a.
Maneji pls ya kusa karewa
[10/14, 6:56 PM] Sadnaf: ???? S????N????DIN GROUP
Written by
???????? SADNAF????
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_ *P.M.L*
#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
A short novel based on true life story
Page 55_60
Ajiye dorinar Yusuf yayi yace " ina jinku mai kuka zo nema a gidana"?,
dan auta da sauri ya d’aga hannunsa Dan baya so ya k’ara dukansu da dorinar,”Alhaji kayi hakuri wlh wani abokinmu ne yace muzo ana Neman ‘yan aiki,” da sauri su bad boy suka hau girgiza kai suna ” aiki muka zo nema wlh” murmushi Yusuf yayi yace ” yanzu dai aiki kuka zo nema ko” kallon juna suka yi suna tsoron Murmushin da Yusuf yayi,ko dai ya gano abinda ya kawo sune,In kuwa hakane sun shiga uku Dan da alama shine mai gidan,Yusuf mik’ewa yayi ya fita waje ya kullo k’ofar palon ya nufi boys quarters Bad boy da sauri ya mik’e ya kalli dee boy yana ” Mun shiga uku Mun lalace muna zaman zaman mu Ton G ya janyo mana masifa inaga fa mai gidan ne ” D badest one da yafisu shan laftar dorina cewa yayi “ina ga fa kama ton g yayi da matarsa mu dai munga ta kanmu yau,Dan Auta dai ba magana sai sauke ajiyar zuciya yake, shiru suka yi da suka ji ana k’ok’arin bud’e k’ofar,Yusuf ne ya shigo yana ingiza keyar ton g har gabansu ya kai Ton g, Yusuf yace ” Wanan shine abokin naku”? Cikin tsananin tsoro suka fara gyad’a kai Yusuf kallon Ton G yayi da ya ringa bin su Bad boy da kallo yace ” wayanan sune ‘yan group d’in ” SEX NIGHT CLUB da kuke turawa juna hoto da videon Matan da suke Muamalla daku” da sauri Ton g yace “sune Alhaji amma saura mutum d’aya Aliyos shine Wanda Baka samu a waya ba,” Su bad boy tuni cikinsu ya d’uru ruwa dasu ka ga Ton g da zub’abb’un hak’ora guda biyu,ga Shatin dorina a koina na jikinsa Yusuf juyawa yayi ya kallesu yace ” ina shi Aliyos d’in yake “? Dee boy ne yayi sauri yace “ya koma Lagos da zama ranka ya dade”,girgiza kai Yusuf yayi yace “dakyau zan muku tambayoyi inaso Ku fad’amin gaskiya idan ba haka ba kunga wanan ” ya nuna Ton g ” to wlh zan Muku fin abinda na masa matsawar kuka min karya shi hak’ora biyu na cire mishi Ku gabad’aya zan cire muku, kafin nan duk ku mik’o min wayoyinku cikin rawar jiki da tsananin tsoro suka ciro wayoyinsu suka mik’a mishi, irin Tambayoyin da Yusuf yayi wa Ton g irin shi ya ringa musu suka ringa bashi amsa daki daki,suma dai Hajja Kaltumen ce ta zama silar lalacewar su,girgiza kai Yusuf yayi yace “Ku yanzu abinda kuka ringa yiwa matan mutane idan Ku aka nemi matanku Ku,zaku ji dadi,girgiza kai suka yi da sauri suna bazasu ji dadi ba,”, To meyesa kuka zabi irin wanan rayuwar mai tarin zunubi,shiru suka yi babu Wanda ya iya bud’a baki yayi magana,kiran Hajja Kaltume da yaringa shigowa wayar Manal ne ya katse masa maganar da yake, mik’ewa yayi yace Ku tashi dukanku mu tafi wajen leader d’inku tana can a hotel tana jiran tsinane irinku,zan d’auki mumunan mataki akanta Dan itace SANADIN LALCEWARKU,ITACE SILAR JEFA MATATA ACIKIN MASIFA DA BALAI”Ku wuce mu tafi,da sauri suka yi waje, Dan suma zasu so Hajja Kaltume ta samu nata rabon bulalar,d’uruwa suka yi cikin motan Yusuf yajasu suka nufi k&tsuit hotel,tafiyar minti goma sha biyar ne ya kaisu hotel d’in, Umarni ya musu da su sauk’a,su biyo shi abaya kuma kar Wanda yayi yu
nkurin gudu wa a cikinsu,duk Wanda ya kuskura yace zai gudu tsaf zai harbeshi, tsoro ne ya kara rufesu suna bazasu gudu ba, dorinar da ya ajiye abayan motarsa ya d’auko ya rufe motar ,yayi gaba su Ton g na binsa abaya,Yusuf bai sha wahalar gane d’akin da Hajja Kaltume ta kama ba,text ya mata da wayar Manal da ta zo ta bud’e k’ofar suna waje.
Hajja Kaltume dake kwance tayi rashe rashe akan gado daga ita sai wani gajaren bak’in skinny,sai breziya dake jikinta,juyi kawai take yi tana tand’a baki kamar wacce take shan alewa( ‘yar iska kawai????????) shigowar text message ne yasa ta mik’e da k’yar Dan Tumbine da ita kamar mai ciki,tana gama karanta message d’in da aka turo mata ta mik’e tana wani juyi,Tumbinta duk ya zazzago kasa kamar mai ciki,bud’e k’ofar tayi ta juya tana tafiya tana juya duwawu,Yusuf kuwa dama ya saita dorinar hannunsa ya rik’e ta da kyau yana ganin an bud’e k’ofa ya ce su Ton g su shiga,da sauri suka shige shima yabisu a baya ya rufe k’ofar da mukulli,Hajja Kaltume duk batasan abinda ake ba juya duwawu kawai take dan ta ja hankalin wanda Manal ta had’ata dashi,magana take tana “kun kyauta da kuka shanyani ai,sai Ku shigo daga d’aki “,tana dab da shiga d’akin taji saukar dorina ko ta ina, Yusuf da iya k’arfinsa yake zabga mata dorinar dan ganinta da yayi ba kaya ba k’aramin k’ara hasala shi yayi ba,duwawunta da cinyoyinta ya ringa kaiwa duka, Hajja Kaltume kuwa sai tsalle take tana ihu,su ton g dake gefe a tsaye dariya suka kwashe dashi da suka ga yanda Hajja Kaltume take tsalle tumbinta na tsalle,cikin minti goma Yusuf ya chanjawa Hajja Kaltume kamanin,dan bayan ya zane mata duwawunta da cinyarta fuskarta kawai ya koma ya ringa lafta,Hajja Kaltume kuwa sabida tsananin azaba kasa ma ihu tayi ta zube akasa tana birgima, sai da Yusuf ya gaji dan kansa ya wurgar da dorinar hannunsa ya zauna akan kujera yana maida numfashi,Su ton g tuni suka gimtsa dariyar da suke amma dayake Bad boy yana da rabon shan wata bulalar kasa daina dariyar yayi,dan Hajja Kaltume yanda ta ringa tsalle,tumbinta na tsalle ne ya masifar bashi dariya,Yusuf mik’ewa yayi a fusace yad’auki dorinar da ya wular ya nufi inda suke,ihu suka ringa yi suna bashi hakuri amma ina Yusuf ya Riga da ya zuciya sai da ya musu lilis ya koma gefe yana sauke ajiyar zuciya,Hajja Kaltume kuwa sai da ta samu minti 30 tana birgima tana kuka dan ba k’aramin azaba tasha ba d’agowa tayi da k’yar ta kai kallonta kan su Ton G da suka yi tsururu suna kallonta mamaki ne ya rufeta data gansu a waje d’aya d’aurewa tayi tace cikin kuka “Ton G,Dee boy,bad boy,D badest one,dan auta mai kuke yi anan,mai ya had’aku da wanan azzalumin kuka kawo shi gurina”? Shiru suka yi suka kasa magana dan gani suke suna k’wak’waran motsi Yusuf zai rufesu da duka,Yusuf cikin tsananin kiyayya da tsana yace “inaga har yanzu Baki daku ba dan da kin daku bazaki samu bakin magana ba” mik’ewa yayi ya nufi wajenta,Hajja Kaltume tasa ihu ta mik’e da k’yar tafara zagaya palon, tana “kasan wa kake duka kuwa kasan kuwa ni matar aurece,wlh sai ka yi dana sanin dukana shege azzalumi, mai had’ina dakai mai nayi maka da zaka min irin wanan dukan” duk maganar nan da take yi zagaye palon take tana kuka, murmushin takaici Yusuf yayi ya kalli Ton g yace ka gaya mata ko ni waye, Ku fad’a mata komai dan ni bazan iya magana da kazama karuwa ba,dan wanan shaidaniyar bata da banbanci da karuwa da ake biya a kwanta da ita,wanan ‘yar iskar tsohuwar da ahaife ta haifeku ita take biya ankwanta da ita wai nan da sunan matar aure wa’iya zubillahi,” maza gaya mata ko ni waye, kafin na mik’a Ku offishin Hisba dan wanan shaidaniyar matar sai na kaita Hisba,Ton G cikin rawar baki da tsoro ya fara bawa Hajja Kaltume labarin Yusuf Mijin Manal ne,ya kwashe komai ya fad’awa Hajja Kaltume a k’arshe ya bud’e mata wawulonsa yana “Hajiya kinga mai kika janyo min na rasa hakorina biyu nayi dana sanin biye miki”,Hajja Kaltume tunda Ton G yafara magana jikinta ya hau rawa,tsananin tsoro ya rufeta, zubewa tayi akasa tana ” Kayimin rai bawan Allah ka rufamin asiri nayi kuskure bazan sake ba”