A SANADIN GROUP COMPLETE HAUSA NOVEL
Wani mugun
tsawa ya daka mata yace ta shige taje ta sa riga tun kafin yazo ya k’ara mata wani dukan dan ganinta da yake ba kaya wani irin zafi Zuciyarsa ke masa a guje ta shige d’aki taje tasa kayan ta fito ta kuma zubewa agaban Yusuf tana ” “bawan Allah kayi min rai karka tona min asiri wlh sharrin shaidan ne” Yusuf wani irin bak’in ciki ne ya rufe shi yace dan Allah baki ji kunya ba da kika ce sharrin shaidan ne,ai kema kanki shaidaniya ce,dan Allah dubi yaran da kika lalata kika d’orasu akan hanyar halaka, A haife kin haifesu,da aurenki kike aikata zina,kika bud’e grp kika janyo mata salihai kika dulmiyar dasu da aurensu da yayansu,anya ke ba jahila bace dan jahilai kadai ne za su iya abinda kika yi,
Dan kinyi Abu kamar jahilan farko wanda basu da ilmi da tsoron Allah
Ki tuna fa Allah madaukakin sarki a cikin AlQur’ani mai girma yana cewa
Wa man ya’asil laha wa rasulahu fakad dalla dalalan mubeenah
(Dukkan wanda ya saba ma Allah da manzonshi hakika yana cikin bata mabayyani)
Ke kam abinda kuka jefa kanki a ciki yafi karfin b’ata ya koma hallaka bayyanan na.
Haba kina musulma ‘yar musulmai amma kina aikata masha’a irin wannan alhalin Allah da kanshi ya fad’a cikin AlQur’ani mai girma cewar
Wa Qullil mu’uminati yagdubna min absarihinna wa yahfazna furujahun
(Allah yace ma Annabin rahma ka gaya ma matan mummunai su kulle idanuwansu daga kallon abun ki su kuma kiyaye farjinsu daga daga abinda Allah ya haramta) (zinace zinace)
Wallahi Ku sani gabad’ayanku kun aikata babban zunubi,ke kina da aure kina aikata zina,Ku kuma kuna Neman matan aure kuna aikata zina dasu,yanzu fa zaku iya cewa wannan kaddara ce Allah ya d’ora muku ,to bari kuji na fad’a muku wanan ba kaddara bace da Allah ya dora maku, face kaddarar da kuka dora ma kanku saboda shagala da dunia, rashin tsoron Allah da kuma gangar shaidan dake gaya maku karya. Saboda Allah da kanshi ya fada a cikin AlQur’ani mai girma inda yake cewa.
Innallaha laa yazlimuu misqalaa zarra
(lallai Allah baya zaluntar Dan Adam daidai da gwargwadon kwayar zarra)
Kunga kenan babu yadda zaayi Allah ya zalunceku ta hanyar dora maku zina da aurenku,zinarma kazama da yayan cikinku.
Alhalin da kashi a cikin AlQurani ya fadi da kanshi cewa..
Wala taqrabuz ziinah..innahu khana fahishatan
(kada Ku kusanci zina,sbd ta kasance alfasha ce)
Ku yanzu ko hukuncin da Allah ya tanadar ma mazinata baya daga maku hankali wanda ku hukuncinku kisa ne ta hanyar jefewa a matsayinku na matan aure su kuma samarin ga abinda Allah yace a kansu
Azzani wazza niyatu fajliduu kulli waheedin mihhumaa mi’atee jaldha
(Da mazinaci namiji da mazinaciya mace dukkansu hukuncinsu bulala dari ne)
Mune nan zamu kiraku da kaddara saboda kaddara ce Allah ya doro mana ta aurenku tunda mudin ba mazinata bane ba kuma mushirikai bane
Amma Allah ya hadamu da fasikan mata mazinata masu zina da yayan cikinsu,zinarma da ta ido ta baki data farji duk kun hada kuna yi..wa’iyazu billah
Wannan wace irin masifa ce. Muna salihan maza Allah ya hadamu da matan banza.
Wannan mummunar kaddara ce Allah ya dora mana. Allah kuma ya bamu ikon cinyeta.
Azzani la yankihuu illa zaniyatan au mushrikatan wazzaniyatu la tankihuha illa zanin ai mushrik,fa hurumma zalika alal mu’uminin
(Mazinaci namiji baya aure sai mazicinayi mace ko mushrika,haka kuma mazinaciya mace bata aure sai mazinaci namiji ko mushriki,hakika Allah ya haramta hakan akan mummunai)
Yanzu ke hajia Kaltume kinsan iyakar zunuban da kika dauka kuwa a dunia,kin zama hangar shedan,kina bin yaran mata da manyan mata kina lalata masu rayuwa,kina koya masu zina,kina bata kananun yara maza ta hanyar koya masu mummmunar dabia ta zinace zinace, kina bata rayuwar aure (babbar sunna ta maaikinmu) kina wulakanta daraja da martabar aure,kina koya ma matan a al-umma ha’intar aure alhalin babu abinda mazajensu suma gaza dasu,ke koda sun gaza ki sani zina haramun ce kuma babu inda aka halatta komin tsananin condition kuwa
Hajia Kaltume ki sani ga abinda Allah ke fada akan irinku nan
Innallazina yuhibbunah an tashi’aal fahishata fil lazina amanu lahuum azabunn aleemun fid dunia wal akhira,wallahu ya’alamu wa antuum laa ta’alamuun
(Hakika wadanda suke son yada alfahasha ta (zinace zinace) a cikin mutanen da sukayi imani, lallai suna da zunubi mai tarin yawa a dunia da lahira. Allah masani ne akan abinda baku sani ba)
Dan Haka Ku tuba Ku nemi yafiyar Allah tun mutuwa bai riskeku a cikin irin wanan halin da kuka jefa kanku a ciki ba,yanzu mijinki kina ganin kinyi masa adalci,yanzu idan na tona miki asiri na yad’aki a gidan duniya na nemo mijinki na fad’a masa abinda kike aikata wa zakiji dadi,?” Da sauri Hajja Kaltume ta girgiza kai tana kuka dan tunda Yusuf yafara magana taji wani tsoron Allah na shi garta bata tab’a nadamar abinda take aikatawa ba sai yau
.Yusuf magana ya cigaba da yi yana
Ina ma ana yiwa mazinata hukuncin tun a gidan duniya kafin su mutu,da an rage zinace zinace a duniya,Allah ubangiji ya shiryeku idan kuna da rabon shiriya, Ku sani duniya ba gidan zama bane,Ku farka tun da wuri,dan kun shagala da yawa, naseeha Yusuf ya ringa musu sosai,Hajja Kaltume dasu ton g suka ringa kuka,suna nadamar abinda suka aikata,Yusuf sim card d’in wayarsu ton g ya cicire ya mik’a musu yace musu tafiya zai yi da wayarsu bazai iya basu ba,zai basu kud’i su siyi wani wayar, kallon Hajja Kaltume yayi data d’urkushe tana ta kuka yace ” kiyi k’ok’ari ki nemi yafiyar mijinki dan kin cutar dashi,kin ci amanarsa ko da kin tuba kin nemi yafiyar Allah kindaina abinda kike yi,matsawar baki nemi yafiyar mijinki ba Allah bazai yafemiki ba har sai kin nemi yafiyar mijinki,a k’arshe ina baki shawara ki rufe wanan grp d’in da kika bud’e idan ba haka ba,duk wacce ta cigaba da iskanci asanadiyarki kina da zunubi babba,kallonsu Ton g yayi yace ” Ku kuma kun maida zina ado,kun maida zina abun burgewa,kuje ku sab’i Allah kuzo kuma kuna fad’a kuna turawa junanku hotona da videon abinda kuka aikata,karku manta kowane gabb’a na jikinmu zai yi shaida ranar Lahira ina jiye muku zaman wuya,ina jiye muku daren hisabi daren da bawa ya kan yi kuka,daren da mata zata ga mijinta ta ringa b’uya akan Hisabi,daren da d’a zai ga ubansa ya ringa b’uya akan hisabi, daren da ‘ya taga uwarta ta ringa b’uya akan Hisabi,Allah ya ganar daku gaskiya,ina mai Baku shawara kuje Ku nemi duk mazajen da kuka aikata zina da matansu Ku nemi yafiyar su,daga haka ya fice daga d’akin yace Wani acikinsu ya biyo shi ya basu kud’in wayar,gabad’aya Yusuf ya d’auresu da jijjiyoyin jikinsu an rasa mai tashi a cikinsu ya bishi, kuka suke sosai suna tsinewa Hajja Kaltume dan duk itace silar jefasu a cikin wanan masifar,yanzu dagaske suma sai an nemi matansu,yanzu dagaske suma in suka haifi ‘yaya sai an neme su,( Sadnaf kuwa tace wanan dole ne ai duk abinda kayiwa d’an wani sai anyi maka)
Yusuf kuwa yana barin hotel d’in bai zame ko ina ba sai gida, yana zuwa sallah yayi ya had’a kayansa dan ayau yake so ya koma Abuja, yana dab da ficewa daga d’akin idonsa ya sauka akan wayarsu bad boy da ya k’arba koma wa yayi ya zauna a gefen gado,ya d’auki wayarsu ya shiga gallery aikuwa hotuna da videon manal da yake kyautata zaton duk abokanan Ton g suna dashi awayarsu su yagani kaca kaca,gogewa ya fara yi hawaye na zubo mishi dan Manal ta cuceshi matuk’a da ta tura sirrinsa mutane wajen shidda suka gani ganin goge hotunan duk b’ata lokacine,yasa ya sun gume wayoyin ya fita waje,ya bud’e rijiyar dake kai ruwa saman tank ya jefa wayoyin a ciki,ya koma d’aki ya d’auki jakar kayansa ya fita waje ya hau mota ya d’au hanyar Abuja.