A SANADIN GROUP COMPLETE HAUSA NOVEL

A SANADIN GROUP COMPLETE HAUSA NOVEL

Manal kuwa aranar k’arfe Tara aka sallamesu daga asibitin likita ya bata shawarwari da ta rage tunani jininta yana hawa sosai,tunda suka je gida,Manal ta kule a d’aki in banda kuka babu abinda ta keyi,Mallama Rabi ko kallon inda d’akin yake bata yi ba ballantana akai ga ta rarrashi Manal dan gani take duk abinda ya faru ita ta janyowa kanta,daddare su Mustapha suka hallara a gidan dan su tatauna yanda za ‘ayi a samu Yusuf a tambayeshi sakin Manal yayi ko kuwa, Abduljabbar da Babangida suka yanke shawara suje ranar Asabar su sameshi da haka suka ringa maida zance inda suka ringa cewa matsawar Auren Manal mutuwa yayi,lailai Manal zata ci ubanta a hanunsu,da haka suka yiwa Mallama Rabi sallama suka nufi gidajensu.
[10/14, 6:56 PM] Sadnaf: ???? S????N????DIN GROUP

Written by

???????? SADNAF????

PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_  *P.M.L*

#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com

A short novel based on true life story

Page 60_65

Wanan shafin naki ne ke kadai Auntyna ( AUNTY SIS????) thanks for your love and support

Ban manta dake ba Meenahtraj Fck novels ina mik’a sakon gaisuwata gareki

kuna raina

Aseeya Nasser
Saudat idrees muhd
Shamsiyya shamsudeen
Momyn sultan kd
Mrs marafa
Ayush
Bilkisu

IN FACT INA YINKU ‘YAN ZAUREN BIEBIE ISAH KUNA BURGENI IRIN TOTALLY

WISH YOU SPEED RECOVERY MY FATY AZLAND GET WELL SOON DEAR

Wata biyu kenan da tafiyar Yusuf abuja bai k’ara waiwayar Kano ba,waya kawai yake bugowa Hajiyarsa ta had’a shi da yaransa ,Hajiya Munawwara tayi mishi fad’an har ta gaji, Yusuf kuwa yana sane yak’i zuwa duk wanan lokacin,so yake zuciyarsa ta k’ara sanyi kafin ya dawo,Dan har lokacin ya kasa manta abinda Manal tayi mishi,duk da kewarta da Santa dake addabarsa haka ya d’aure,yana San ganinsu Hanif amma haka ya d’aure yak’i zuwa Dan gani yake In yazo ya gansu zasu iya karya mishi zuciya ya maida Manal,shi kuwa ba yanzu yake so ya mayar da Manal ba yafiso sai Manal ta shiga hankalinta tasan mai take yi tukuna zai maidata,Dan ya Dad’e da yafe mata bayan dogon tunanin da yayi yagane shaid’an ma ya bada tashi gudunmawar wajen dulmiyar da Manal,amma Idan ba haka ba babu abinda zai sa ya maidata.

B’angaren Manal kuwa tunda ga lokacin da yayanta Babangida yaje gidan Yusuf ya dawo yace gidan a kulle yake, Mustapha ya kirashi awaya Yusuf ya basu hak’uri da zai zo da kansa amma ba yanzu ba,Manal ta shiga cikin tashin hankali da damuwa ,bata da aikin da ya wuce kuka bata barcin dare Sam,kullum tana kan sallaya tana kuka tana Neman yafiyar Allah,tabi ta rame tayi baki,ga kewan yaranta dake damunta,haka kawai in tana zaune sai ta ringa jiyo muryar Su Hanif,tasha yunk’urin taje gidansu Yusuf taga su Hanif dan tasan babu inda Yusuf zai kai yaran da ya wuce nan,amma kunya kan hanata zuwa Dan gani take kamar Yusuf ya gaya wa Hajiyarsa abinda ta aikata,Mallama Rabi tun tana share ta tana nuna mata halin ko in kula har ta dawo ita ce ke mata naseeha,tana rarashinta akan ta kwantar da Hankalinta watak’ila ita kuma tata jarrabtar kenan.

B’angaren su Haneef kuwa kullum sai sun sa Hajiya Munawarra agaba suna damunta akan ta kaisu wajen momynsu da daddynsu,Hajiya Munawarra ta kanyi musu karya tace tafiya suka yi sun kusa dawowa,babu irin kayan wasan da bata siyo musu Dan ta deb’e musu kewa,tun Suna murna idan ta siya musu har ya kai ya kawo ma idan ta siya musu,watsi suke yi dashi suyi ta kuka su dai akai su wajen Momy da daddy,Taufiqa ma tafi d’agawa Hajiya Munawarra hankali Dan bakin gate take zuwa ta tsaya tayi ta kuka ita dai akai ta wajen momyn ta,har yajin cin abinci suka ringa yi su alalai sai an kaisu wajen momynsu,Hajiya Munawarra ganin duk wayo da dabararta ya kare yaran sun botsare mata ne yasa ta kira Yusuf ta rufe shi da fad’a akan idan bazai maida Manal d’akinta ba to yazo ya kwashe yayansa ita ta gaji,Yusuf hakuri ya ringa bata yana ayyuka ne suka mishi yawa shiyasa bai zo ba Tuntuni amma yana nan zuwa tayi hakuri,tsaki Hajiya munawarra tayi tace kar ma ya dawo in ta gaji kwashe yaran zata yi ta kai wa uwarsu.

Yau ma suna su Hanif na zaune da littafinsu abaje a gabansu sunyi cirko cirko,Taufiqa ta had’a kai da gwiwa kana ganinsu sai ka d’auka marayune,Dan duk irin kiriniya da yara kan yi duk basa yi sunyi wani sanyi,Hajiya Munawarra tana zaune akan kujera tausayinsu duk yabi ya rufeta,Hanif ahankali ya d’ago bayan ya gama karanta Home work d’in da aka bashi dan Sam bai iya ba,Hajiya Munawarra ma ba iya wa tayi ba Dan ita bata yi boko ba iya Arabic tayi,kwana biyu suna shan dukan fad’uwar da suke a home work,ba kuma iya wane basu yi ba,suna bukatar akara musu bayani Dan ana d’an twisting questions d’in,Hanif da yarone shi mai d’an karan wayyo,rashin ganin mahaifiyarsa na mutuk’ar damunsa Dan gwara ma Mahaifinsa yana kiransu awaya wani tunani ne ya fad’o masa arai ya d’ago yace wa Hajiya Munawarra

“hajiya ko dai Momyn mu mutuwa tayi kuke b’oye mana” Ku fad’a mana gaskiya idan mutuwa tayi mu hak’ura Dan kowane mai rai dole ya mutu,dole mu yarda da kaddara mai kyau ko Mara kyau,Dan Mallaminmu yace kowane bawa arayuwa sai Allah Ya jarrabceshi ya gwada imaninsa ya ga inzai iya cinye jarrabawar da ya masa, mun gaji da b’oye b’oyen da kuke mana,jikina yana gayamin momyna tana cikin matsanacin Hali Hajiya Ku fad’a mana gaskiya inda mahaifiyar mu take,”hanif yace yana fashewa da kuka,ai kamar zuga su Saleem yayi tuni suma suka fashe da kuka,Hajiya munawarra mutuwar zaune tayi da taji maganar dake fitowa daga bakin Hanif dan bata tab’a sanin Hanif yasan Kalmar mutuwa ba ballantana akai ga yasan kaddara mai kyau ko Mara kyau,lalai wayon Hanif ya wuce tunaninta,d’aurewa tayi tace, “Ku daina kuka Momynku bata mutu ba,Ku shirya anjima na kai Ku wajenta Dan nima nagaji da ganinku awanan halin,”cak suka tsayar da kukan da suke, suka d’ago da sauri suna kallonta,Taufiqa mik’ewa tayi da sauri taje ta dafa cinyarta tana ” Hajiya dagaske zaki kaimu muga Momy”? Gyad’a kai Hajiya Munawarra tayi ahankali tausayinsu na k’ara rufeta,wani mugun ihu taufiqa tayi ta fara tsallen murna,su Hanif kuwa suka tafi da gudu suka rungume Hajiya Munawarra,Hajiya munawarra hawayen da take b’oyewa ne ya hau zubo mata Dan rabon data gansu cikin farinciki haka tun lokacin da suke zuwa daga gidansu gaisheta,d’akinsu suka nufa da gudu suna bari suje su shirya,Hajiya munawarra girgiza kai tayi ta fara kwashe litattafan da suka baje a tsakiyar palon,d’akinta ta nufa Dan ta shirya Dan in bata shirya yanzu ba tasan halinsu haka zasu sata agaba su takura mata har sai ta shirya.

Driver ne ya kaisu har k’ofar gidansu Manal,Su Hanif suka duro daga motar da gudu, suka shiga cikin gidan suna kwalla wa Manal kira,Manal dake zaune akarkashin bishiya hanunta rik’e da Qurani tana karantawa kamar a mafarki taji muryar su Hanif suna “Momy Momy” daskarewa tayi azaune,ta k’ara baje kunnawa da idanuwa tana jiran taga dagaske ne muryar Su Hanif take jiyowa,wucewarsu tagani da gudu sun shige palonsu,farinciki da murna ne yasa ta kasa tashi hawayen farinciki ya hau zubo mata,Hajiya Munawarrra ce ta k’araso inda take a zaune adai dai lokacin da su Hanif suka k’ara fitowa daga Palon suna waige waige da alama Ita suke nema,idansu ne ya sauka akanta tana zaune akan darduma tana ta hawaye da gudu suka nufi wajenta suke zube ajikinta,ita kuwa ta rungumesu tana fashewa da kuka,suma kukan suka fashe dashi suna “Momy shine kika tafi kika barmu” Hajiya Munawarra itama hawayen tausayi ne ya hau zubo mata tana sharewa adai dai lokacin da mallama Rabi ta fito daga palon, Dan barci take muryarsu Hanif ne ya tashe ta daga barci, wani irin farinciki ne ya rufe Mallama Rabi data ga Hajiya Munawarra Dan tasan duk yanda akayi sulhu ne ya kawota ciki ta koma da sauri, ta d’auko katon tabarma ta fito ta shimfid’a tana yiwa Hajiya Munawarra bismillah tazo ta zauna,Hajiya Munawarra wajen tabarmar ta k’arasa ta zaune tana kallon Manal da yayanta dake rungume da juna tsananin tausayinsu ya rufeta,Manal ta bata tausayi dan ayanda ta ganta tasan Manal tana cikin tashin hankali da tunani,Dan tabi ta rame tayi wani zuru zuru kamar ba Manal ‘yar duma duma ‘yar gayu ba,Ruwan da Hajiya Rabi ta ajiye agabanta ne yasa ta d’auke idonta daga kallonsu,suka fara gaisawa da Mallama Rabi,Manal sai a lokacin tasan tare su Hanif suke da Hajiya munawarra Dan idonta ya rufe tana murnar ganin ‘yayanta ahankali ta zame su Taufiqa daga jikinta ta mik’e ta nufi inda suke asanyaye,dan gani take kamar Hajiya Munawarra tasan komai,tsugunawa tayi har kasa ta fara gaisheta,Hajiya Munawarra ta amsa gaisuwarta tana k’ara kallonta,su Hanif k’ara biyo Manal suka yi suka za zauna agefen tabarma,Taufiqa kuwa ta d’ane bayanta,Shiru ne ya biyo baya Dan Mallama Rabi batasan mai yakawo Hajiya Munawarra ba,Hajiya Munawarra ce ta fara magana tana “Manal kiyi hakuri nasan Yusuf bai kyauta miki ba duk da bansan mai ya faru ba,bai kamata ya d’auki irin wanan matakin ba,ya koroki gida ya rabaki da yaranki,Mallama Rabi kuyi hakuri Yusuf bai kyauta ba Sam,Dan wlh babu yanda banyi ba akan yazo su daidaita da matarsa ta koma d’akinta Dan ni nasan duk abinda Manal tayi masa bai dace yayi mata haka ba,Dan nasan Manal bazata yi masa abinda zai b’ata masa rai da gangan tana sane ba,na dade inaso inazo na maidata d’akinta da kaina,zuba mishi ido nayi Dan naga iya gudun ruwansa,wlh ko ni nan rabona Dana sa shi a idona tun da ya kawo min yaran nan wata biyu kenan,bai k’ara waiwaiyarmu ba sai dai ya bugo mana waya,abine ya isheni nace bari dai nazo dakaina Dan yaran nan wlh tausayinsu nake ji kullum sai sunyi min kuka akan na kai su wajen mahaifiyarsu sai kace wasu marayu,duk abinda ya faru bansani ba wlh,nayi nayi ya fad’a min ya k’i,ai shi zaman aure sai da hakuri ballantana an fara Tara zuria,sai dubi yara ayi hakuri,Dan haka Manal kiyi hakuri ki koma d’akinki ko dan farincikin yaranki,Yusuf ya gama nashi mulkin ki barni dashi,”Mallama Rabi ina Neman alfarma ayi hakuri komai ya wuce Dan Allah kar ayi tone tone Dan agarin tone tone sai rai ya ringa b’aci a iska,ayau inaso na maida Manal d’akinta taje ta cigaba da kula da yaranta,Ku manta abinda Yusuf yayi muku Dan Allah”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25Next page

Leave a Reply

Back to top button