A SANADIN GROUP COMPLETE HAUSA NOVEL

A SANADIN GROUP COMPLETE HAUSA NOVEL

Sai da suka samu wata biyu
zaman nasu bai canja zani ba dan har yanzu Yusuf yana kan bakansa na sai Manal ta shiga hankalinta zai fara sakin jiki da ita,duk da yana takuruwa,baya iya barci,sai ya sha maganin barci,haka zai ta kallon manal yana had’iyar yawu,Manal kuwa bata fasa zuwa d’akinsa ba duk da fitowa yake yayi kwanciyarsa a palo, Manal kuwa tayi kukan tayi adduar har ta gaji,ganin ta gaji da binshi ne yasa itama tadaina zuwa d’akinsa iya kacinta tayi mishi duk wani Abu data San hakkinta ne tayi mishi, Yusuf tuni ya fara shan jinin jikinsa da yaga Manal itama ta tattara shi ta watsar,ta rungumo yaranta,duk dare tana d’akinsu yana jiyo hirarsu,shima ahankali abun yafara damunsa,yazo in suna hira dasu Hanif sai yaringa sa musu baki,Manal tuni taji wani farinciki ya rufeta dan tasan Yusuf ya fara saukowa,hakan data gani ne yasa ta dage ta ringa kwalliya da zata ringa Jan hankalinsa,kwalliyar da zata yi da safe kafin ya fita daban,Wanda ,zata yi da rana daban,na dare kuwa yafi kowane dan gayu take sosai Yusuf ya ringa had’iyar yawu,

Yusuf kuwa hankalinsa yanzu kullum a tashe yake dan Manal tana rikirkita masa lissafi,in yaje office baya iya tab’uka komai in banda tunanin Manal da yake ga wani masifaffan sha’awa dake sa shi ciwon Mara,duk dare,ganin in dai ya biyewa zuciyarsa shi zai cutu ne yasa bayan ya koma gida sun mishi sannu da zuwa kamar yanda suka saba,ya wuce d’akinsa dan yasan Manal sai ta shigo d’akinsa ta had’a mishi ruwan wankan,yana zama agefen gado ta shigo da shigarta da ya k’ara dagula mishi lissafi,ta nufi band’akin dan ta had’a mishi ruwan wanka,ai bai yi wata wata ba ya bita band’akin,ya janyota ya fara aika mata da sakoni,

AYAU NAGANE CEWA MATA DA MIJI SAI DAI ALLAH,IN KACE ZAKA SHIGA TSAKANINS MATA DA MIJI ZA’A BARKA DA SHAN KUNYA,ALLAH YA K’ARA HAD’A KANMU DA MAZAJENMU,YA KAU DA FITINA A TSAKANINMU AMEEN

aranar Sam babu Wanda yayi barci a cikinsu,Yusuf ji yake kamar ya maida Manal cikinsa,wani Santa na ratsa zuciyarsa,Manal ma amfani ta k’ara yi da opportunity d’in ta k’ara Neman yafiyarsa suka ringa yiwa junansu alkawaririka,washegari su hanif ma Kansu sun San iyayensu suna cikin farinciki.

WAIWAYE

Hajja kaltume tunda Yusuf ya bar d’akin take ta kuka kamar ranta zai fita dan ayoyin da Yusuf yaja mata ba k’aramin d’aga mata hankali yayi ba,yanzu ko da ta tuba ta daina kenan,duk wanda yayi zina ta silar ta sai ta samu kamoshi ta ina zata fara neman yafiyar mijinta,mazajen da ta Nema da aurenta ‘yan kananan yara bazasu lissafu ba dan har da abokanan ‘yayanta nema take,idan mutuwa ta d’auketa a irin wanan halin mai zata ce wa Allah, wani irin tsoron Allah taji yana shigarta,ta kuma rushewa da kuma,su Ton g kuwa haushinta da tsanarta suka ringa ji suna dura mata zagi,bad boy kuwa ji yake kamar ya rufeta da duka dan sai da aka kai ruwa rana kafin ya yarda ta fara aikata zina dashi,Allah ne yasan adadin mutanen da Hajja Kaltume tasa suke aikata zina da aurensu,Allah ne yasan samari nawa ta ringa had’awa da mata aure dan ko shi ta had’a shi da matan aure sun kusa shidda, d badest one da wa’azin da Yusuf yayi musu ba k’aramin tasiri yayi a zuciyarsa ba wani mugun tsawa ya dakawa Hajja kaltume yana ta rufe musu baki ta cika musu kunne da kukan munafirci,Shi dai Allah ya isa tsakaninsu da ita bazasu tab’a yafe mata ba,Ton g kuwa wawulon bakinsa ya tab’a ya fashewa da kuka,shima yana tsinewa Hajja kaltume, atakaice ahaka suka baro hotel d’in,bayan sun kwashe duk kud’in hajja Kaltumen suka d’au hanyar abuja,suna wuce Kaduna kad’an,wata katuwar tirela ta k’aro da motarsu,atake Bad boy,da d baddest one rai yayi halinsa,ton g,dan auta,da dee boy kuwa mugun rauni suka ji,inda sai da aka danganasu da asibiti,ahanyarsu ta zuwa asibiti,dee boy shima ya amsa Kiran mahallici,Ton g da dan auta, kuwa bama su San inda kansu yake ba sabida mumunan raunin da suka ji

Hajja kaltume kuwa,tayi kuka tayi nadama,tayi Dana sani ta rasa inda zata sa ranta, bata iya komawa ba aranar sai washegari dan kwana tayi kanta na mata ciwo sabida kukan data kwana tana yi,washegari da sassafe,taje bank dake kusa da hotel d’in ta ciri kud’i dan su ton g sun tatiketa ba ta da ko sisi,

K’arfe biyu ta isa abuja ta nufi gidanta,gabad’aya ta rasa mai ke mata dadi,dan har yanzu nasihar Da yusuf ya mata yana mata yawo a kunne,ahaka ta shiga gida tana mai shan alwashin daina abinda take yi ta fara Neman yafiyar ubangiji,turus tayi a lokacin da ta hango mijinta da ‘yayanta a zaune a Palo,hawaye na ta zubowa Alhaji sa’adu,yayanta ma dagani sunci kuka sun gode Allah,gabanta wani irin yanke wa yayi ya fad’a jakar hanunta ya sub’ale daga hanunta jikinta ne ya fara rawa dan tunda ta auri Alhaji sa’adu bata tab’a ganinsa a irin wanan halin ba,’yaranta zuba mata ido suka yi gabad’aya suna kallonta sai hawaye ke fita a
idonsu,d’aurewa tayi ta k’arasa inda suke Alhaji sa’adu kuwa ya mik’e yabar palon ,baban d’anta Abba ne ya mik’e da sauri yana “Hajiya mai muka miki zaki mana haka?,Hajiya da wane idon kike so mutane su ringa kallonmu? Mai Abbanmu ya miki da zaki yi masa haka,mai yasa kika zabi irin wanan wulak’antaciyar rayuwar Hajiya da yayanki da komai kika ringa aikata zina Hajiya kinyi mana adalci kenan”? Tunda ya fara magana Hajja kaltume ta rik’e zuciyarta dan ji take kamar ya fad’o d’aurewa tayi tace mai kake nufi Abba ban fa gane mai kake cewa ba”, a fusace Abba ya d’auki wayarsa dake ajiye akan kujera yace ” ga abinda nake nufi Hajiya k’arbi ki gani,” jikin Hajja kaltume ne ya d’au rawa ta k’arbi wayar,ware ido tayi tana kallon videon,itace a kwance a d’akinta itada Aliyos abokanan ton g suna aikata zina akan gadonta,take ta tuna ranar,bayan sun gama watsewarsu da Aliyos,ta bashi dubu hamsin, Aliyos ya wurgo mata kud’in yace ta bashi dubu d’ari kud’in yake bukata dubu hamsin ya mishi kad’an,ashar ta liliyo mishi,tace idan ba zai k’arba ba ya ajiye mata kud’in ta bazata iya k’ara mishi ko sisi ba,Aliyos murmushi yayi mata a lokacin yace wlh idan bata k’ara mishi ba zai tona mata asiri duniya tasan abinda take yi,tsaki tayi a lokacin,ta mik’e ta wurgar masa da kayansa waje, tace ya fice ya bar mata gida tun kafin tasa masu gadi su mishi shegen duka,Ashe dagaske yake zai tona mata asiri video yayi mata ya watsa a duniya,hannu ta d’ora aka bayan ta gama tunani ta zube akasa ta fara kuka,tana ta shiga uku ta lalace,’yayanta wani irin kallon tsana suka ringa binta dashi,yayanta mata kuwa sai kuka suke dan videon ya watsu a ko ina,asanadiyarta har auren ‘yarta fadeela ya mutu,sakamakon videon da mijinta yagani,kukan suke suna ta cucesu,ahaka Alhaji sa’adu ya fito daga d’akinsa ya nufi inda Hajja kaltume take akwance tana birgima ya wurga mata takardan saki yace “Na sakeki saki Uku bazan tab’a yafe miki abinda kika min ba ko da yafe miki shine zai sa ki shiga aljana,haka zata tsine miki har na koma ga mahallicina,” sarkewa yayi ya fara tari suka yi kanshi gabad’aya, kafin kace me ya zube a kasa yana aman jini,Abba kinkimarsa yayi hanyar waje dashi da gudu suka bi bayansa,Hajja Kaltume kasa kuka tayi dan gani take kamar mafarki take,atakaice Hajja kaltume taga masifa a rayuwarta dan yayanta korarta suka yi sakamakon mahaifinsu b’arin jikinsa ya mutu,Hajja kaltume tayi kukan tayi nadama har yaza mana bata iya gani sosai,wani irin kuraje ne suka fito mata a jiki,da private part d’inta bata iya zama Sam ,iyayenta ma kyamarta suke dan duk sunji labarin abinda ta aikata,duk wani Abu data mallaka ya kare a zuwa asibiti,intaje wajen yayanta babu mai sauraranta,babu yanda bata yi ba akan taga Alhaji sa’adu ta nemi yafiyarsa dan burinta bai wuce ta nemi yafiyarsa kafin ta mutu ba,amma ta kasa ganinsa dan masu gadin gidan korota suke yi,hak’ura tayi da zuwa gidan,ta koma gidansu ta kulle kanta a d’aki tana Neman yafiyar Allah.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25Next page

Leave a Reply

Back to top button