A SANADIN GROUP COMPLETE HAUSA NOVEL

A SANADIN GROUP COMPLETE HAUSA NOVEL

Wajen dining ta nufa ta zuba abincin ta fara ci,ringing d’in wayarta ta jiyo daga d’aki ta k’wallawa Hindatu kira tace ta d’auko mata wayarta a d’aki,da sauri Hindatu ta d’auko mata wayar a lokacin har ya katse,cewa Hindatu ta yi taje ta gyara mata d’akinta adai dai lokacin da kiran ya kara shigowa wayar,murmushi tayi da taga Titi ne yake kiranta lumshe ido tayi ta d’aga wayar Ton G,kuwa yace “babe ko ba ki tashi bane”

K’ara lumshe ido tayi tana murmushi Dan muryarsa har ya saukar mata da kasala cewa tayi,”ban d’ade da tashi daga barci ba yanzu haka ma breakfast nake”

Dariyan ‘yan duniya Ton G yayi yace ” how was your night hope jiya kinyi mafarkina Dan Ni jiya mafarkinki kawai na ringa yi dan assshhhhh kai baby bazaki gane ba you are sweet,”

Manal tsigar jikinta taji yafara tashi,sha’awa yafara taso mata,kasa magana tayi sabida irin muryar da yayi mata amfani dashi,

“Babe kinyi shiru ko kin fara hawa network ne arhhhh” yace da muryar karuwai (Dan malafar uba)????,

Manal shiru tayi ta kasa magana Dan ya jefata a cikin wani hali,

“Babe talk to me mana kinsan voice d’inki na tsumani ssssss yace kamar Wanda yaci abinci mai yaji( Dan kan uwa kawai)????????

Manal magana tafara k’ok’arin yi taji kira na shigowa dubawa tayi taga Daddyn Hanif ke kira da sauri tace mishi tana zuwa mijinta na kiranta zata kirashi ta katse wayar ta d’aga wayar,Yusuf da ransa a mutuk’ar b’ace yake Dan ya mata miss call wajen goma sha bata ‘daga ba,sai gashi ya kirata yaji call waiting,sallama tayi mishi amadadin ya amsa yace

“meyesa nake kiranki baki d’auka ba?

Manal cewa tayi
” Gashi na d’auka yaushe ka kirani ban d’aga ba”,dan ita bata ma San ya kirata ba, cikin tsananin b’acin rai yace “ki duba wayarki kiga Misscall nawa na miki” ya kashe wayar,da sauri ta duba misscall taga ashe tun 6:30 ya ke kiranta,ya mata miss call har goma sha d’aya,tunanin karyar da Zata mishi ta fara yi,kiransa ya sake shigowa wayar,d’agawa tayi yace “guda nawa kika gani”?

” Daddyn Hanif wlh barci nake lokacin da ka kirani banji ba wlh”

“Barci barci fa kikace Manal” k’irjinta ne yafara dukan uku uku Dan indai ya kirata da Manal to ransa yakai kololuwar wurin b’aci, ” yaushe kika fara komawa barci idan kin idar da sallar asuba”

Manal rasa amsar da zata bashi tayi Dan bata komawa barci in tayi sallar asuba,tun a gida,shi yasa ma in yayi tafiya yake kiranta awuraren lokacin kafin yatafi aiki,haka zasu ringa waya daga 6:30 har zuwa lokacin da yara zasu tafi makaranta ta had’asu awaya su gaisa daga nan suyi sallama,Dan babu laifi Yusuf is a caring Husband indai yana da sarari awajen aiki sun tayin waya da ita kenan,Kame kame ta fara yi tana k’ok’arin lalubo amsar da zata bashi Dan bata iya karya ba,katseta yayi yafara magana rai a b’ace

” Manal Wai mai yake damunki ne? kwana biyu bana gane miki Sam,kin chanja ba kamar yanda kike ba,yanzu yaushe rabon Dana ga kiranki a wayata da sunan ke kika kirani?yaushe rabon Dana ga misscall d’inki awayata? Ina kiraki awaya Allah Allah kawai kike in ajiye wayar,a watsapp ma ina miki magana kafin ki kulani kiban amsa sai ansamu awa d’aya ko biyu alhalin kina online Manal what have come over you,?ko laifi nayi miki kike min haka,banso nayi miki magana ba amma abun na damuna manal,caring d’in dakike nuna min duk kin daina,yanzu in ba ni na kiraki ba bazaki tab’a kirana ba,in ni nakiraki sai kin kawo min excuse din dazai sa muyi sallama,texes d’in da kike turomin suke deb’e min kewa in ina wajen aiki duk kin daina,what change you like this Manal in laifi nayi miki ki fad’amin na baki hakuri,yanzu duba kigani,bakiji muryata ba har 11:30 baki kirani ba,kuma ni na kiraki baki d’aga ba,hasali kina can kina waya ba ki damu ba,Manal ina nan ne zuciyata tana wajenki da yarana,wlh duk abinda nake kuna raina,ba asan raina kuka yi nesa dani ba,badan halak d’ina nake nema ba,babu abinda zai nesanta ni daku, Dan Allah idan laifi nayi miki, ko wani ke zugaki kiyi hakuri ki dawo yanda kike, Dan canjawar da kikayi ba gani bane kawai har da yarana,sani ne baki yi ba Hanif ya gayamin Last week dazan kaisu gidan Hajiya,yanzu kamar Hanif ma yasan kin canja musu,yaringa cemin in baki hakuri in laifi suka miki,kin daina musu home work Hindatu ke musu,kin daina koya musu karatun Qurani Haba Manal this is not you”

Tunda yafara magana hawaye ya hau zubo mata Dan tabbas ta canja ba haka take ba,Yusuf Nada hakuri,to mai yasa takewa Mijinta uban yayanta haka,mai yasa ta zabi group akan farincikin Mijinta da yayanta,yanzu jiya Manal daddare kafin barci ya d’auketa sai da ta ce mata “Momy yanzu kin daina sona,bakya min wanka bakya min kwalliya,bakya koya min Home work d’ina Daddy yafi sona idan ya dawo,yana min wanka ya ce in kawo littafina ya koya min home work d’ina Momy mai nayi miki kika daina sona ” a lokacin tsaki tayi tace mata ta tafi ta bata guri bata San surutu,ta cigaba da kallon videon dake d’aga mata hankali.

Magana ta fara yi tana kuka “Kayi Hakuri Daddyn Hanif nayi maka laifi insha Allahu zan gyara,na gane kuskure na,zan cigaba da nuna caring d’ina insha Allahu kwanaki nan ne bansan mai yake damuna ba,” cikin kulawa Yusuf yace “mai yake damunki Mom Hanif menene matsalarki har akwai abinda yake damunki da zaki kasa fad’amin share your problems with me am your husband, I would try my possible best to solve it pls dear ki fad’amin abinda yake damunki karki b’oyemin komai,

Manal tsintar kanta tayi da sharara mugun karya Dan Mahaifiyarta Nada matsalar ido,za ayi mata aiki satin da za a shiga cewa tayi
” Daddy Hanif wlh bawani abu ke damuna ba kamar aikin da zaayi wa Mama ran Thursday, am scared I don’t want to loss her she is the only one we have left,”tace tana fashewa da kuka
Da sauri Yusuf yace ” Haba Mom Hanif akan wanan kika d’agawa kanki hankali kika d’aga mana,insha Allahu za ayi aikin successfully ai yanar daya rufe mata ido za a cire mata,babu abinda zai faru pls ki kwantar da hankalinki kinji addua ya kamata muyi na Allah yasa ayi aikin cikin Nassara kinji”

Gyad’a kanta tayi kamar yana kallanta tace “insha Allahu zan ringa adduar”

“Yauwa Mom Hanif ko kefa,In baki kwantar da hankalinki ba fa zan dawo ayau”,da sauri tace “aa wlh zan kwantar insha Allahu, murmushi yayi yace ” zan turo miki 200k ki je ki mata shopping anjima idan su Hanif sun dawo su rakaki,kuce ina gaisheta ina dawo zanje ingaisheta” hawaye ne ya hau zubo mata Dan tausayin Yusuf,yana masifar Santa yana k’ok’arin yaga ya faranta mata rai,sai gashi tana nan tana cin amanarsa da yaron da bai fi shi da komai ba,yaron da bai fi ace Dan aikensa bane, ji tayi guiltiness na damunta,d’aurewa tayi ta had’iye kukan da ya taho mata ta mishi godiya tayi mishi adduar ahaka ya mata sallama yace zai kirata anjima,yana kashe wayar ta fashe da kuka Dan ji tayi ta rasa mai ke mata dadi,wai wane irin rayuwa ta jefa kanta a ciki,halayen da ba nata ba duk ta ara ta yafa,ba iya aurenta halin da ta jefa kanta ya shafa ba har da Ibadan ta,wai yau itace tayi sallar asuba sha biyu saura, yaushe rabon da tayi lazumi in tayi sallah?yaushe rabon da ta d’auko Qurani ta karanta,sallar kanta ba a nutse take yinta ba,hasali tana sallah tana tunanin group video na fad’o mata arai,wanan wane irin balai ne,yanzu ???? S????N????DIN group duk ta koma haka,yanzu menene mafita,
Kiran wayar daya shigo wayarta ne ya katse mata tunanin da take, ganin Titi ke kiranta ne yasa taja tsaki Dan haka kawai taji bata San jin muryarsa,sai da ya mata misscall biyar ya hak’ura,kiran Hajja Kaltume ne ya shigo wayarta shima k’in d’agawa tayi Dan gani take duk itace silar jefata a cikin wanan halin,tunanin ta ringayi na ta tuba ta rabu dasu gabad’aya ta dawo da farinciki gidanta,ahaka Manal ta ringa sake sake,aranar taci alwashin kula da yaranta,da ganta ta shiga kitchen ta dafa wa yaranta abincin da suke so ta dawo ta zauna a Palo ta kira Yusuf awaya suka fara hira,hakan kuwa ba k’aramin farantawa Yusuf rai yayi ba,sai labari yake bata tana dariya,ahaka su Hanif suka dawo suka sameta sallama sukayi,suka durk’usa suna gaisheta,amsawa tayi tana mik’awa Hanif wayar,k’arba yayi yafara gaishe da Yusuf,ta d’auki Taufiqa ta d’orata a cinya,tana cire mata uniform,Taufiqa da rabon da taga Manal ta mata haka sakin baki tayi tana kallonta,Salem da Hanif suma ita suke kallo mamaki ya gaza b’oyuwa a fuskarsu,Dan sun saba sai Saturday Sunday take basu wanan kulawar,Manal kuwa duk tasan kallon da suke mata,wani irin zafi taji a zuciyarta tana danasanin abinda tayi,d’aya bayan d’aya suka gaisa da Yusuf,ya musu sallama yace suci abinci zai k’ara kiransu insun dawo daga islamiyya,Manal Hanif take kallo daya sunkuyar dakai yana Murza hanusa Dan jinsa yayi a takure ya saba da rashin kulawarta agaresu,Manal sauke Taufiqa tayi daga cinyarta ta ruk’o hanun Hanif tace

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25Next page

Leave a Reply

Back to top button