A SANADIN GROUP COMPLETE HAUSA NOVEL
“Manal kinsan yau abinda yasa kika ga banida kuzari,wlh badan kar na k’wareki ba da bazan iya tab’uka komai ba,wani abune ya tsaya min arai Manal tun shekaran jiya abun ya kasa barin raina,”
Manal itama cikin tsananin damuwa da fad’uwar gaba tace “Daddyn Hanif mai yake damunka haka? mai kasa aranka ka kasa mantawa?
“Manal wlh wani tashin hankali na gani shekaranjiya matar oganmu nagani ta fito daga hotel d’in da naje siyan abinci,yaron da ta ruk’o hanunsa wlh ahaife zata haife shi,Manal ban yarda da abinda Nagani ba sai Dana mari kaina na murza idona dan in gaskata abinda nagani,Manal sabida tashin hankalin Dana shiga wlh sai dana je gurin receptionist na bata kud’i na roketa ta fad’a min mai matan nan tazo yi a hotel ita da yaron dana ga sun fita yanzu,Manal wlh amsar da receptionist d’in ta bani sai da numfashi na ya d’auke na wucin gadi,wai Ashe shekarar ta biyu kenan tana zuwa hotel d’in ita da yaron,wani sa’in su kwana wani Sa’in su tafi,
Manal hankalina ya tashi tausayin oga musa ya rufeni yana can yana nemawa matar nan kud’i ita da yayanta,ita ta nan ta na cin amanarsa,Manal ya zanyi idan ni mata ta tayiwa haka,Manal Oga Musa karki so kiga yanda yake rawar jiki jummaa tayi ya tafi gida,wlh tun ran alhamis zaki ga ya fara siye siye Wanda zai kai gida,har tsokanarsa na tab’a yi nace duk da ya tsufa yana rawar jiki zai tafi gida, Manal murmushi yayi yace min idan bai yi wa iyalinsa ba wa zai yiwa,bashi da sama dasu, Dan su yake nema,sune farincikinsa,Manal washegari Dana je office naga suna waya da ita wlh sai da hawaye ya zubo min Dan bai San mai matarsa take aikatawa ba,mai yasa zata masa wanan cin amanar mai ya rageta dashi,idan sha’awa ne da ita mai yasa bata nemi ya saketa ba sai dai ta ringa cin amanarsa,Manal idan ni mace tayi wa haka zan iya had’iyar zuciya na mutu”
,Manal tunda yafara magana jikinta ke rawa duk sanyin Ac sai da ta jike da gumi,ganin Yusuf na magana kamar ba a hayyacinsa yake ba yasa ta janyo shi ta rungume shi tana ” daddyn Hanif ka kwantar da hankalinka ka daina hara rowa da matarka ce tayi ma haka ya zakayi Dan matarka ma bazata tab’a yi maka haka ba” d’agota yayi da sauri yana girgiza kai yace “Manal nasan bazaki tab’a min haka ba,ko a mafarki bazaki tab’a cin amanata ba,na yarda dake koda wani ne yazo ya fad’amin bazan tab’a yarda dashi ba,abinda yasa kika ji ina cewa da matata ce ya zanyi shine,ina sa kaina a amatsayinsa ne dani aka yiwa haka ya zanyi”
Manal da jikinta tsabar rawa da fad’uwar gaba Dan gani take kamar asirinta na hanyar tonuwa d’aurewa tayi tace Daddyn Yusuf yanzu idan matarka kace misali tayi maka hakan ya zakayi”?
Runtse idonsa yayi da k’arfi ya damko kafad’unta yace ” wlh kasheta zanyi,in ban kasheta ba zan nakasa ta,in ban nakasata ba,zan mata mugun dukan,idan ban mata mugun duka ba wlh tallahi sai na k’ona gabanta inkuma saketa,kuma har duniya ta nad’e ina tsine mata,” da ace ana ganin zuciya da Yusuf yaga yanda zuciyar Manal ke lugude,da ya kasa kunne da ya ji yanda cikinta ke hautsinewa,da ya k’ura mata ido da ya hango tsantsar tashin hankali a idonta,aranar barci bai ga idonta ba Dan tana tunanin da Yusuf ya San mai take aikata wa ya zata yi,a tsorace take matuka,Dan idan Yusuf zai iya shiga wanan tashin hankalin akan wata taci amanar mijinta,ina ga ace ita ya kama tana cin amanarsa,abun ta sa aranta har ya gama weekends d’insa aranar Monday da zai koma da safe ya zaunar da ita ya rik’e hanunta yace “Manal ki kwantar da hankalinki ki cire abunan a ranki nasan dole ki damu Dan kinsan matsayin matar auren da take aikata zina da aurenta,amma ba komai Oga Yusuf bashi da hakkinsa wataran sai asirinta ya tonu insha Allah”
Manal hawaye kawai take sharewa Dan ita tasan halin da take ciki tinda ga lokacin da ya bata labari,ajiyar zuciya ya sauke ya d’ago fuskarta ya share mata hawaye ya kira sunanta cikin sanyin murya”Manal Dan Allah in tambayeki karki b’oye min ko kiji kunyata Dan Allah,Manal shin in bana nan kina jin sha’awa?”
Shiru Manal tayi tana kallonsa Dan bata San mai zata ce mishi ba,
Ganin tana kallonshi ne yasa ya mik’ar da ita ya zaunar da ita akan cinyarsa yace “Manal Dan Allah ki fad’amin Dan bana so na ringa cutarki,kina hakuri,idan kina sha’awa nasan abinda zan yi,Dan ni nasan Oga musa watakila baya gamsar da matarsa yanda ya kamata shi yasa take cin amanarsa
Girgiza kai tayi da sauri tace mishi bata sha’awa har sai ya dawo,ba rok’onta ya k’ara yi da ta fad’a masa gaskiya tace mishi ba tayi har sai ya dawo,ahaka ya musu sallama ya tafi,Manal kuwa jikinta sai da yayi sanyi, in ta rufe ido,Yusuf kawai take gani lokacin da ya shiga tashin hankali akan wata ta ci amanar mijinta.
Sai da Manal tayi sati bata kula Titi ba Dan ta sha alwashin ta tuba ta daina tun kafin asirinta ya tonu,amma dayake Hajja Kaltume shu’uma ce ita da titi sai da suka San yanda suka yi suka kuma maidata ruwa.
Ton g shirun da yaji ne yasa yace “yana ji kinyi shiru”
Da sauri Manal ta fara girgiza kai tana ” kayi hakuri bazan iya aikata zina da aurena ba,wanan ma abunda muke yin bansan mai yasa nake biyewa San zuciyata ba,bazan iya cin amanar mijina ba pls let cut this relationship, tsoron Allah ya shigeni,mu tuba mu daina,Wanda yake da aure Allah in ya aikata zina jifansa zaayi tayi har ya mutu,”
Ton g lashe lebb’e yayi yace inkin San wani ai baki San wani ba Allah sai na d’ana,
Kwantar da murya yayi zai fara tsarata tayi sauri ta kashe wayar, Dan har ga Allah so take ta watsar da kazamiyar rayuwanan tun kafin asirinta ya tonu Yusuf yasan mai take yi,Dan ya masifar yarda da ita, ko kiranta aka yi awaya baya gigin d’agawa ballantana akai ga ya hau mata bincike awaya,ansha turo mata texes wayarta na hanunsa bai tab’a bud’ewa ba.
Ton G ba irin Kiran da bai yiwa Manal ba amma Sam tak’i d’agawa,haka ma Hajja kaltume ke zuba mata kira amma bata d’auka ba Dan indai ta d’auka tasan zasu maidata ruwane.
Hajja kaltume ashar ta dura da ta ji abinda Ton g yace mata cewa tayi” Tj ai bata isa ba wlh sai ka d’ana ai ni burina arayuwa inga na samu partner in crime,partner ma mai wa’azi inta San wata tabbas bata San wata ba bari na gaya maka abinda zaka yi,nidai banjiyo abinda take ce mishi ba Dan k’asa tayi da murya,murmushi Ton g yayi yace shi yasa kike burgeni hajiya kina da kai hakan za’ayi.
A daren ranar ton g kiran Manal kawai yake,da Manal taga ba hak’ura zai yi da kiranta ba d’agawa tayi a fusace zata masa masifa ya kwantar da murya yafara magana “Manal tunda kika min nasiha jikina yayi sanyi nima na tuba na daina”,washe baki manal tayi tace yauwa ko kai fa ,alfarma d’aya nake nema agurinki Manal”
“Ina jinka”
Dan Allah zanzo kano mu gaisa kawai,ba wani Abu ne zai kawo ni ba wlh kawai so nake na ganki a zahiri,”
“Aa tijjani ni banasan naganka Dan Allah kabarni haka na rik’e aurena ka manta da ka tab’a magana dani, Dan Allah Dan banga amfanin had’uwarmu ba,
Tuni logic d’in da Hajje kaltume ta koya masa ya fad’o mata kuka ya fara yi yana tsarata da wlh ya tuba badan suyi wani abun yake San ganinta ba,tsarata kawai yake,Abunka da mace kwakwalwar kifi gareta tuni ta tsaru ta d’auka iya gaisawar zasu yi tace mishi ta amince yazo su gaisa amma ya sani daga waje zai tsaya ta lek’o su gaisa,ce mata yayi ya yarda da haka suka yi sallama yace mata gobe zai d’auko hanya tunda ran laraba ne kafin mijinta ya dawo.