BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL

BABBAN YARO BOOK 2 COMPLETE NOVEL


Kullum Mimi sai ta kirani a waya tana min magiya kan naje gidan ta wai na taya ta zama kafin ya dawo wataran sai na zage ta sannan muke dai-dai tawa da ita. Wataran ma kin d’aukar wayar nake yi.


Yau watan Amjadu Uku a chana Wanda yayi dai-dai da watanin auran su da Mimi komai yayi masa yanda yake so, don haka sai ya fara shirye-shiryen dawowa gida.

Lokacin kuma Mimi tana fama da Matsalar ciwon ciki matsananci Dr Mujahid shine tsaye a kanta scanning anyi mata sau biyar kullum Abu guda yake nunawa Cikin Mimi na zaune a bayan mahaifa Mujahid ya tsorata mutuka duk scanning din da zai sanya ayi mata zai nuna masa twins amma ko gurin wanne kwanciyar daban, daya cikin mahaifa daya a waje Innalillahi wa’innailahi raji’un.

Duk wannan fad’in tashin da muke yi Sam bai sani ba domin Mujahid yace kar Wanda ya fada masa, Ni kad’ai ya fadawa abunda yake faruwa nima tare da gargadin kar in fadawa kowa saboda kwanciyar hankalin su duk da haka granny tayi mugun tada hankalin ta, saboda ta Dora wa cikin Mimi son duniya.

Tuni na tare a gidan Mimi kusan wata guda kenan muke cikin wannan tashin hankali Mimi ta fige tayi wata shegiyar rama sai uban haske gashi bata cin abunci sai nayi da gaske sannan take ciki ko kuma taga raina ya b’aci kullum da daddare ta dinga murkususu kenan Cikin ta, kuka nake yi sosai ina mata addu’a.

Ganin halin da take ciki yana kara yin gaba, ya sanya Dr tununin Sanar wa da Amjadu dole kome yake yi ya aje ya dawo gida domin duba halin da gidan yake ciki, Duk da cewa kullum yana kiran waya safe da dare amma kira da ban zuwa daban, Dr yana ganin dole ayi mata aiki shine za’a samu maslaha. To ko da ya kira Amjadu din a waya ya fad’a masa abunda yake faruwa bai wani nuna damuwar sa ba yace.” Insha Allah yana kan hanya.

Zaman mu guri guda da Mujahid ya sanya wata matsananciyar soyayya ta shiga tsakanin mu, gani nake yanzu nake soyayya Mujahid ya cika mutum mai kyawun hali da tausayi tabbas duk macan da ta aure shi tayi dace da miji na saki jikina sosai dashi, domin shine yake kaini makaranta cikin motar shi kullum, siyayya kuwa babu irin wacce baya min, har yaron shi sai da ya kawo min ya yini a gurini
Grnay tayi ta tsokanar sa, sai dai yayi dariya kawai.

Ina dawo wa daga makaranta granny take fada min yau Mai gidan zai dawo domin yayi waya bayan futa ta yace.” Yana jirgi, shikkenan na nemi nutsuwata na rasa domin Sam bana kaunar abunda zai sake hada ni dashi, tunanin hada kaya na nafara yi domun ina gudun cin mutumcin da zai yi min a gidan shi….

20/11/2019
[11/21, 10:38 AM] BintuUmarAbbale: BABBAN YARO

MALLAKAR_ BINTA UMAR

LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA SAI TA CI SHI

58

Mimi na sanya tayi wanka ta gyara jikinta tsaf! Nima nayi wanka ban yi wata kwalliya ba, na sanya atamfar mu ta anko Candy mu, ina kokarin zama kusa da ita tace.” Asma’u ya kamata a shirya masa abunci ko.”? Kallonta nayi na minti biyu kana nace”Kina da tabbacin zai ci abincin idan ka shirya masa nifa bana son wulakanci domin yanzu ma na had’a kayana tsaf! Zan tafi inda nafi wayo.”
Marairaice fuska tayi tace”Don Allah kar ki tafi yau kinji ki bari na warware tukkuna.” Tsaki naja tare da fad’in “Kinsan inuwarmu bata had’uwa guri guda dashi, bana son abun bata rai.” Tace” Ki rabu dashi don Allah duk abunda zai miki.”
Shiru nayi kawai, Granny ta futo daga d’akinta da carbi a hannunta ta idar da sallahr la’asar, ta kalli Mimi sai ta saki dariya tana zama kan kujera tace.” Wato da kika ji Mijin ki na kan hanya kinyi wanka tsaf har da kwalliyar fuska.” Dariya nayi kadan nace”Dole tayi kar taje ki kwace mata gakinan kin rambad’a kwalli har da sabuwar atamfa.” Granny tace”Sai kiyi kuma komai abunki bazan baki kwallina ba.”
Dariya nayi nace”Ni ba kwalli nake so ba ki bani lallai me ja irin na k’afafunki.”
Kallon k’afar tata tayi tace.” Yana gidana nima Iyami ce ta kawo min daga garinsu, duk sanda zata zo gidanan zan ce ta Zo miki dashi.”
Nace”Yawwa granny ko yanzu ma a kira ta a waya ai tana da waya ko?”?
Granny tace”Tana da waya to wai ke meye kika damu da kunshi sai kace wata me miji, ki bari mu masu miji muyi.”
Dariya ta bani sosai nake yi nace”Ni ko nake da miji a hannu kin San shi don kullum yana zuwa gaishe k………….Kafin in karasa ya shigo parlor tuni k’amshin turaran sa, ya mamaye parlor. Yana sanya da Riga shart fara tas tana da gaje ran hannu, wando jikinsa jins ne blue ya sanya fencing cap (hana sallah) idanunsa sake da bakin glass wuyan shi wata siririyar sark’e ce silver sai shek’i take, hakama a gogon hannun Shi, shi kanshi blet din da yayi amfani dashi abun kallo ne kafin kazo kan takalmin k’afar shi, booth mai igiyoyi blue colour in da kasan bature haka ya koma.
Duk zancan da Asma’u suke da granny a kunne shi.
Fuskarsa murtuk! Ya tsaya bakin kofa, yana karb’ar wayoyin shi daga hannun Rambo

Granny ta washe baki tana fad’in”Oyoyo angon karni ya dawo sannu da zuwa angon Aishatu sannu da zuwa.”! Mik’ewa tayi karasa bakin kofar sai washe baki take, fuskarsa ya saki kad’an ganin kakar tashi ya rungomta jikinsa hade da sumbatar goshin ta yana fadin”Granny na same Ku lafiya.”? A sake tace.” Lafiya ba lafiya gaskiya amma shige ka huta tukkuna.”
Hannunta ya rik’o suka k’araso parlor, ina kallon Mimi ta yunk’ura ta mike tsaye ta nufi inda suke, sakin Granny yayi ya kamo ta ya rungume ta hadda lumshe ido! Kauda kaina nayi da sauri ina da na sanin zama na a gurin.
Fuskar ta ya d’ago da hannunshi yace.” Momyna haka kika koma.”!? Mimi ta fara k’walla, saurin rungume ta yayi yana Dan dukan bayan ta kad’an cikin sigar rarrashi yace.” Sorry baby na ya taso ki a gaba kiyi hakuri insa Allahu zaki warware.”
Kungunta ya riko har suka k’araso tsakiyar parlor.
Ya kalleni a d’age. Nima na kalle shi babu yabo babu fallasa.
Wuce wa yake kokarin yi, granny tace “Zaka wuce baku gaisa da Asma’u ba, yarinya hazika kuma jajurtacciya ta tsaya kan matarka sosai, gaskiya samun me zumuncin ta sai an tona.”

Babu yabo babu fallasa tace.” Granny na ganta ai ni da ita waye zai fara gaida wani ko banza na girme ta nesa ba kusa ba, bayan haka kuma a gidana take dole ta girmama ni.”
Tsaki granny Taja tana fadin”kai dad’i na da kai kenan,son girma kowa ai da irin tashi fahimtar ko kaga ka wuce bata gaishe ka ba.”

Fuskata na saki don kar in kunya ta granny nace”Sannu da zuwa ka dawo Lafiya. “? A fakaice ya kalle ta, yayi saurin dauke kansa, jin muryar ta ya tayar masa da abubuwa da dama, yana tafiya yace.” Lafiya k’alau na dawo.”
Bedroom d’insa ya shige da Mimi rungume a jikin sa.
Wanka ya shiga ya futo Mimi na kwance kan bed ya kalleta cike da tausayi ya dawo da matsananciyar sha’awa babu hali domin akwai rashin imani ya kusanci Mimi duba da halin da take ciki.
Sabbin kaya ya sanya ya shirya tsaf dashi kana ya zauna kusa da ita.
Mik’ewa tayi zaune cikin kasala, shi kuma ya tsira mata idonsa.
A hankali yace.” Momy kin rame sosai laulayi ya sanya ki a gaba ko.” ? Mimi tace.” In laulayi ne kadai da sauk’i kullum da daddare fa bana iya bacci ciwon ciki, Dr Mujahid ne a tsaye a kaina sai Asma’u, domun ta dalilinsa take zaune a gidanan tunda shi ya tursasa ta, yana da kirki wallahi, kusan kullum sai ya shigo ya duba ni.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60Next page

Leave a Reply

Back to top button