BABU SO HAUSA NOVEL

BAJININA BACE COMPLETE HAUSA NOVEL

Wani abin mamaki tun kafin Baffa ya sanarwa kowa haihuwa Muhammad yafara sanarwa haihuwar Wanda a yanzun yake shekara ta uku amatakin karatuntasa Wanda yakeyi Kuma zab’in Baffansa yayin da ak’asan ransa Kuma yasha alwashin bayan ya gama zaije yayi na soja wanda shine zab’i da ra’ayinsa amma yanzun kam zab’in mahaifinsa yabi yake Wanda ya zabar masa.

Hakanan ya tsinci kansa da wani irin farin cikin kasancewar ganin Baffansa cikin tsantsar farin ciki, haka ma Inna ana fad’a mata haihuwar da kanta ta taso abinda bata tab’a yiba wato kwana agidan Baffa wannan karon cewa tayi ita zata kula da maijegon da’yarta wannan karramawa ta Inna ya k’ara mata kima da mutunci a wajen iyayen Amina.

Ranan suna kuwa Saida Muhammad ya yabaro makaranta yazo suna yasha fad’a wajen Baffa domin a lokacin suna shirin jarrabawane, a lokacin murmushi yayi yace kasa daurewa ne.

Tunda yai arba da kyakykyawar yarinyar yaji ta masifar shiga ransa shikenan Kuma ya tare a d’akin domin kullum ya fito daga b’anga rensa yana d’akin Ammey kamar yadda itama Baffa yasashi fad’a mata har zuwa sanda yakoma makaranta dakewar MARAYAM kamar yadda taci sunanta wanda take Ammey tace sunan mahaifiyar malam ne hakan kuwa yayiwa malam dad’i kulawa ta musamman yake bawa yarinyar kullum sai ankai Masa ita ya tofeta da addu o in tsari

Sailuba kuwa

Takuce maman islam
بسم الله الرحمن الر حيم
______________________

FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION

FCWA

{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________
BA JINANA BACE
2021

            NA 

HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI

MAMAN ISLAM

Page 12

Haka rayuwa taci gaba da tafiya, yayin da Sailuba sukayi amanna da malaman tsubbu wani lokacin suyi sara kan gab’a wani lokacin kuma sai b’ata lokaci da nesan ta kai da mahalicci.

Wata rana Sailuba takaima k’awarta haj. Zakiyya ziyara anan ne take cewa “k’awata ni kuwa me zai hana ki karb’i Maryam?”

Wani d’an iskan kallo ta watsa mata tace “amma k’awata basiranki ya gude ne ko?kirasa yar da zakice na karb’a na raina da hannayena masu albarka”

“Hum k’awata kenan inbaki saniba ki sani rainon wannan yar shine zai baki duk wani abu da kike nema kuma ta hakane zaki cimma burinki akanta sannan zokiji” tajawo tayi mata rad’a, bushewa sukayi da dariya suka tafa sun jima suna kulle kullensu kafin su sallami juna.

Haka Maryam taci gabada samun kulawa daga ta ko wane fanni kamar yadda Nanne ta buk’ata haka dole Ammey ta cire kunya take kula da yarinyar ta domin ta kula abokiyar zamanta ba irin wannan matan bane da suke son jan d’an wani jikinsu.

Sai dai abinda yai masifar d’aga hankalin Amina shine sanda Maryam ta isa yaye kawai tace ita Maryam takeso abata tunda ita an tabbatar da bazata k’ara haihuwa ba, ita kuma Amina yanzune ma ta soma Kuma babu wanda yasan iyaka ci sai Allah dan Allah ya rok’ar mata ita ta temaka tayi mata wannan sadaukarwar.

Wani irin masifaffen tashin hankali ne yakawowa ziciyarta farmaki take tafashe da wani fitinannen kuka mai mugun k’arfi wanda yasa duk suka maida hankalinsu kanta yayin da Baffa yake dubanta da masifar mamaki Sailuba kuwa wani b’oyayyen murmushi take saki azahiri Kuma hawayene yake ta rige rigen fitowa daga idanunta ta bala in kalar tausayi ta taso ta durk’usa agabanta tareda rik’o hannayenta tana wani irin kuka mai cin rai tace.

“Dan girman Allah badan halina ba dan soyayyar da kikewa annabinmu muhammadur rasulillah (S A W) ki taimaka kiyimin wannan sadaukarwar na miki alk’awarin Maryam bazata tab’a sanin zafin cewa bata tareda mahaifiyar taba zan rik’eta da gaskiya da Amana zan kula da ita fiye da yadda bakiyi tunaniba kiyimin wannan temakon ‘yar uwata” ta k’arashe tareda zubowar wasu hawayen Mai uban yawa.

Wani irin tausayin tane ya rufe Baffa yasawa ransa Koda wannan ce kad’ai kwansa a duniya ya baiwa Sailuba ita halak malak ko ba komai Sailuba ‘yar uwarsa ce jininsa Koda baya raye ita mai rik’e masa ‘yarsa ne.

Ta ko Amina wani mugun kallo ta watsawa Amina kuma tasaki wani mugun tsaki mai k’arfin gaske tace”Allah ya baki naki kema maman Maryam shine sunan data rad’a mata tun bayan haihuwar Maryam amma kisani kome zai faru bazan iya baki ‘yata ba domin wannan ai zakunci ne ace an rabani da d’iyata wannan sam bazai yiyuba wallahi” ta k’arashe tana kuka bil hak’k’i domin yanayin kallon dataga Baffa yana mata shi yake nuna jin d’acin kalamanta, batareda ya k’ara duban inda takeba yacewa Sailuba

“Karki damu insha Allahu babu wani abu dazaki nema kirasa shi matuk’ar yayanki Baffa yana raye dan haka bazakiyi kuka rayuwarkiba” daga haka ya tashi ya d’auko Maryam dake d’akin uwarta tana baccinta hankali kwance ya dawo inda suke har lokacin Sailuba bata bar kukan datake ba yace.

“Gata nan na baki amanar ta ki kulamin da ita karki bari wani abun yasameta Kinga itake nan abinda Allah ya mallakamin a halin yanzu wannan kyautar ba kowa Allah yakewa irintaba nasan ko babu raina ke mai rik’e min ‘yatane dan haka bana so kisawa ranki cewa bake Kika haifi Maryam ba haka banaso tasan cewa bakece mahaifiyar taba”

Cikin wata irin razananniyar k’ara Amina ta sulale awajen ta fad’o k’asa sumammiya take suka yo kanta cikin tashin hankali suna jijjigata Baffa ne ya tashi da sauri ya kawo ruwa suka shafa mata take ta kawo ajiyan zuciya, zumbur ta mik’e tana wani irin kuka mai cin rai d’akinta ta shige da gudu yayin da Sailuba ta kalleshi tace ” Baffa ko mu maida mata da ‘yarta kar wani abun Kuma yazo yana dasamun jifa abinda takeyi”
“Karki damu zata rage kinsan dole ne taji babu dad’i ace ‘yarta guda d’aya tak an kyautar wanda bamu da tabbacin cewa tana da wani Kwan takakke bayan wannan musamman idan Kika duba irin yadda ta ringa samun cikin yana zubewa”

Ita ko Amina tana shiga d’akinta ta fad’a saman gado tana wani irin masifaffen kuka mai matuk’ar cin rai tasawa ranta kome zai faru wallahi bazata bawa wannan matar yar taba matar da bataso zuwan yarinyar duniyaba duk wani irin tuggu da ta dinga had’a mata wanda ya dinga sanadin zubewar gudan JININTA tana sane mutumin kuwa da baya son ganin kwanka sanyin idaniyarta a duniya ai baka da mak’iyi sama dashi mayafinta ta zara kawai ta fice agidan tana kallonsu har lokacin suna dining Baffa yana rarrashin Sailuba datace zata dawo mata da yarta.

Kai tsaye gidan su ta nufa tsabar rud’anin data shiga bai barta ta kula da malam dake zaune saman dakalin k’ofa ba ta shige d’akin Nanne wace fitowar ta kenan a wanka tana shirin zuwa duba surukar shamsiyya wacce ta sha ciwo Umma taje ta sake zuwa ita sai yau Allah ya nufa dake a tsarin malam baya yarda su fita rana d’aya sai dai d’aya taje d’aya ta jira.

Tagama zura hijabinta Kennan juyowar da zatayi taji fad’owa Amina jikinta tana wani irin mugun kuka mai masifar cin rai, take jikinta ya kama rawa ta rik’e ta da kyau tana tambayarta ta abinda ya same ta cikin tashin hankali domin tasan duk abinda yasaka Amina kuka to lallai abin yakai intaha.

Amina ta kwashe duk yadda sukayi da su Baffa ta fad’a mata cikin kuka ta k’ara da cewa ‘Kuma Baffa yace ko kallon yarinyar kar na K’ara you amatsayin ‘yata.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button