BAJININA BACE COMPLETE HAUSA NOVEL
MAMAN Islam CE
بسم الله الرحمن الر حيم
______________________
☀ FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION ☀
FCWA
{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________
????BA JININA BACE????
2021
NA
HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI
MAMAN ISLAM
Page 19
Yajima yana gabza bala e kafin ya fice daga office d’in cikin tashin hankali,kai tsaye gidansa ya nufa lokacin haj. Maimuna tana hakimce saman kujera ta d’ora kafa d’aya saman d’aya mai aikinta tana durkushe agabanta da alama wani umarnin take bata.
Tana ganin shigowarsa ta sallami mai aikin sannan “sannu da zuwa alhaji lafiya naganka tun kafin lokacin tashin yayi”
“Na gaji nagaji nagaji haba dan masifa wallahi maimuna kin haifi masifa kin haifi fitina haka kawai ina zaman zamana zai je ya d’auko min masifar da bazan iya magance taba wallahi ba ruwa d’an iskan yaro haihuwar asara t”””””””””’ dakata malam Kaine haihuwar asarar ba d’ana ba me yai maka zaka zo kasashi gaba da masifa ai duk wannan tsinannen bakin nakane yake binsa”
“Zanci” ya lailayo wani katon zagi ya lafta mata,nanfa rigima ta balle wannan ba sabon abu bane agidan Abba AL HASSAN indai ransa zai b’aci ta ranar babu zaman lafiya.
Washe gari bayan tagama shirinta a dining ta tadda Nassar yana kari ta harareshi tace ” um su acici har an fara afawa
Maman Islam ce
بسم الله الرحمن الر حيم
______________________
☀ FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION ☀
FCWA
{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________
????BA JININA BACE????
NA
HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI
MAMAN ISLAM
Page 21
Haka tacigaba da karatunta cikin nutsuwa tun tana tunanin maganganun maman har tasaba ta daina saka abun aranta amma hakan baisa ta daina siyan muhimman abubuwaba aduk lokacin data ganta da wasu ‘yan k’udi masu nauyi, yayinda wani irin shak’uwa mai ban mamaki ya shiga tsakaninsu da name sake d’inta dan haka bata da aminan daya wuce Maryam da Halima.
Abangaren d boy kuwa da farko saida yaci alwashin d’aukan fansa Abban sa ya taka masa burki yace”kul dan ubanka karkaja min mutuwa kwanana basu K’are ba wannan yaron da kake ganinshi bashi da ruwan mutunci ko kadan dan iskane nake bafad’a maka nagaban kwatance dan haka ka nisanci wannan yarinyar domin ba ‘yar kowa bace face’yar Baffa Abubakar”
Saida d boy ya razana dajin abinda Abban nasa yace domin kaf yankin nasu babu wanda baisan waye Baffa Abubakar ba saboda tarin dukiyar da Allah ya hore masa da d’umin karamcin sa ga bayin Allah, sannan agefe guda yasha mamakin yadda take rok’on yayanta da ya k’yale shi haka duk da yadda ake fad’an rashin mutuncin yarinyar take yaji duk wani burinsa akan d’aukan fansa ya ruguje saima k’ok’arin son kulla alak’a da ita.
Agidan su Maryam kuwa babu abinda ya sauya sai tsarin yawon inda yanzun haj. Zakiyya ce take zaryan zuwar musu wanda idan suka shige d’aka har mantawa ake dasu dakehaj. Amina babu ruwanta da ahiga abinda babu ruwanta bata tab’a sanin wainar da suke toyawaba.
Yayin da MD ya diga ayar tambaya akan wannan ziyarar takawar wannan matar mara yankewa hakan yasa batareda da sanin kowa ba ya nemo CCTV camera saida yabari ranan sun fita gantalin bin malamansu da suka saba yasa aka jona aka saita komai tareda recording d’in duk abinda zai rik’a faruwa akaf gidan ta ko ina har d’akin Ammey batare datasan anyi hakanba.
Rannan MD ya kawota makaranta dake sauri yake abakin get ya sauketa sannan yace idan lokacin tashinsu yayi ta fad’a masa zaisa driver ya maidata gida yau yana da wani meeting wanda sai dare yake tunanin zasu dawo k’ala batace masaba kuma dama yasan basatace d’in ba, bai jira komaiba yaja motarsa da azabar gudu yabar wajen.
A hankali tafara takawa zuwa bakin get d’in tunda tafara zuwa makarantar shekara d’aya kenan da d’an wani abun bai tab’a ajeta anan d’in ba sai yau, ta kusa kaiwa bakin k’ofar kamar yadda ta saba koda yaushe sai ya kaita har parking space na makarantar sannan zai ajeta ya juya.
“Hey hey” taji muryan wanda bazata tab’a mantawa ba arayuwarta domin shine mutum na farko da babu wanda ya tab’a yi mata irin tozarcin da yayi mata, batasan lokacin data saki wani matsiyacin tsaki ba ta juya yayin da shi kuma yayi saurin shan gabanta da motarsa, a mugun fusace ta d’ago ta watsa masa wani mugun kallo sanda yake fitowa daga cikin motar.
Yana k’arasowa bata bari ya fad’a mata wani abuba tayi saurin cewa “wai kai wane irin mutum ne mara tunani wanda baisan darajan kansaba bare na waninsa?
Yau kuma takeni kake sonyi komai?
Wai dan Allah me yasa wasu mutanen baau da tunani ne kwakwalwarsu irin na kifine?
Yo inba hakaba ni banga dalilin gamin kifi da gada ba dazaka wani zo ka shamin gaba ina cikin tafiyana idan kuma hukuncin farko ne bai ishekaba akwai wanda sukafi wannan sai ka jira.
Duk abinda take fad’a bai katsetaba saida yabari tagama maganar ta kafin yace ‘Amincin Allah yatabbata ga sarauniya kuma shugabar masu yafiya, ba wani abune yasa na tareki anan ba sai dan na k’ara neman yafiyarki abisa abinda ya faru duk da nasan cewa saboda ke wannan boss d’in yayan naki ya k’yale ni amma duk da haka ina mai kara neman afuwarki na miki alk’awarin ko kallon banza bazai k’ara had’a ni dakeba pls pls pls” ya rik’a maimaitawa yayin da tayi masifar d’auke kanta ta juya da nufin bar Masa wajen batasan ya akayiba sai kawai ganinsa tayi zube agabanta basa gwaiwoyinsa yana cigaba da rok’on yafiyar ta bai ko damu da yadda mutane suka fara taruwa awajen ba.
Zaro idanu tayi ganin yadda ya zube saman gwaiwoyinsa ga mutane da abin kallo baya musu kad’an har sun fara taruwa awajen tayi saurin cewa “meye haka dan Allah jifa har an fara taruwa anan katashi”
“Ni ba damuwana masu kallona ba damuwana kawai kice kin yafemin”
“Tashi dan Allah” ta fad’a cikin sanyin murya “zantashi ne kawai idan kince kin yafemin”
“Na yafe maka amma bisa wani sharad’i to tashi” tasake fad’a can k’asan mak’oshi da sauri ya tashi yana fad’in”na gode na gode sosai ko wane irin sharad’i ne ki fad’a na miki alk’awarin tunda dai kin yafemin” fad’a yana binta lokacin data fara takawa cikin makarantar,bayan yabawa d’aya daga cikin abokansa mukullin motarsa suna takawa a hankali yayin da ta fara ce masa.
“Gaskiya yakamata ka gyara halinka da d’abi unka ba abune me kyau ba kowa ya rik’a maka shaidar baka da mutunci babu wanda ka ragawa har akai ga matakin da kowa zai fara jin tsoronka sam wannan zalunci ne babba dan Allah ka gyara kaga ni d’innan dakake gani duk abinda kake ji dashi nafika ko ranan ma shammata na kayi banda haka bazakayi nasara akainaba sai dai ni bana shiga harkan wanda bai shiga nawaba dan haka kaga ko makarantar nan banda kawa sai A A”
“Nasani sam ban kyautaba kuma na miki alk’awari insha Allah daga yau nima babu ruwana da sabgar kowa”
” Allah yasa” ta fad’a atakaice tana wucewa department d’insa.
Yana tsaye har ta shige murya k’asa k’asa yace “tamin Allah yasa tasoni nidai tamin badan komai ba sai dan nutsuwa da ajinta Abba kayi suruka irin wacce kake so ‘yar wani wanin ma wanda yai suna aciki da wajen k’asar nan”
(Su Kamal d boy daga sannu sarkin fawa lol????????????)