BABU SO HAUSA NOVEL

BAJININA BACE COMPLETE HAUSA NOVEL

“To yau kuma me ya had’aku keda sojan naki nasan dai dashi kike wannan maganar”

“Uhm besty wai ashe jiyan nan da muna hospital bross turowa yayi aka kama d boy karki ga yadda yasa yaransa suka mai dashi wallahi sai da nayi kuka”

“Ke banza ce wallahi besty mutum yayi miki irin wannan yarfin dan an bi miki hakkin ki shine har zai baki tausayi? bakisan d boy ba’ bakisan waye shiba wallahi da bross bai masa hakaba ya rik’a tunda yaga yayi na farko yaji dad’i haka halinsa yake”

Ajiyan zuciya ta sauke tace Allah ya kyauta,yauwa dear kikace Abba yana harkan dillancin gidaje ko?”
“Eh me yafaru?”
“Gida nake son siya besty”
” Ke kuwa besty duk yawan gidajen ku me zakiyi da wani gidan?”

“Bakiji me kikace ba beaty a maganar ki, kinsaka jimlar ku nawa ni kad’ai nakeso”
“To shikenan kamar yaushe kike buk’ata sai muje”
“Ki kira wayarsa idan da dama mu wuce daga nan idan babu damuwa tunda Kinga yanzun bamu da wata lacca”
“Yadda Kika ce besty hakan za ayi”

Daga nan direct unguwar su Maryam dake tayima Abbanta waya ya dawo yana jiransu sai da suka fara gaida mamanta kafin tayi mata iso har d’akin Abbanta sosai kwarjinin sa yaima Maryam dan daka ganshi kaga kamilin mutum mai cikar Kamala da mutuntaka bayan sun gaisa Maryam ta fita ta basu waje.

Kallonta malam Abdullah yace “yarinya me sunan kine?”
Tace “sunana Maryam Abba murmushi Abba yayi yace “d’iya tace ashe” itama murmushin ta saki wanda ya k’ara mata kyau.

“Maryam tace kina son ganina Allah yasa lafiya?”
“Eh Abba lfy dama ina son siyen gidane to shine nakema Maryam magana tace kana harkar gidaje”

Kallonta Abban Maryam yayi na d’an lokaci yana nazarinta sannan yace”ke yar waye ne ‘yata?”
“Baffa Abubakar” ta fad’a atakaice sosai ya jinjina take mamakin yadda akai tasamu k’udi ya d’auke tunda yanajin irin labarin jita jita cewa yarinyar tana mugun b’arin k’udi sannan akwaita da kyautar girma irin na mahaifinta sannan ansakar musu k’udi suyi yadda suke so, kasancewar su Kennan yaransa.

Kallonsa ya mayar kanta yace “to ‘yata kamar wanne kike buk’ata?”
Abba na baka zab’i mai kyau nake so wanda bai gaza 7 million ba” da mamaki yake kallonta kafin yace “shikenan ‘yata insha Allah zanyi miki kamar yadda zanyiwa Maryam” daga haka Maryam ta bashi dubu goma tace “Abba ga wannan ayi cefane”

Da k’yar tasamu ya karb’a dan shi d’in ba irin masu zarmewar zuciya bane.

Ba a wani dad’e ya samo mata gida mai kyau aka yi ciniki ta biya batareda sanin kowa nataba tabar komai awajen Abban aminiyar tata.

Tunda ga ranan dataganta da wasu ‘yan k’udi masu nauyi sai tasai abinda tasan duk lokacin data tashi zata siyar ta samu k’udinta.

Shin wai duk meye dalilinta nayin hakan muje zuwa daga
‘yar mutan YAKASAI

MAMAN Islam CE
بسم الله الرحمن الر حيم
______________________

FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION

FCWA

{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________
????BA JININA BACE????
NA

HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI

MAMAN ISLAM

Page 21

Haka tacigaba da karatunta cikin nutsuwa tun tana tunanin maganganun maman har tasaba ta daina saka abun aranta amma hakan baisa ta daina siyan muhimman abubuwaba aduk lokacin data ganta da wasu ‘yan k’udi masu nauyi, yayinda wani irin shak’uwa mai ban mamaki ya shiga tsakaninsu da name sake d’inta dan haka bata da aminan daya wuce Maryam da Halima.

Abangaren d boy kuwa da farko saida yaci alwashin d’aukan fansa Abban sa ya taka masa burki yace”kul dan ubanka karkaja min mutuwa kwanana basu K’are ba wannan yaron da kake ganinshi bashi da ruwan mutunci ko kadan dan iskane nake bafad’a maka nagaban kwatance dan haka ka nisanci wannan yarinyar domin ba ‘yar kowa bace face’yar Baffa Abubakar”

Saida d boy ya razana dajin abinda Abban nasa yace domin kaf yankin nasu babu wanda baisan waye Baffa Abubakar ba saboda tarin dukiyar da Allah ya hore masa da d’umin karamcin sa ga bayin Allah, sannan agefe guda yasha mamakin yadda take rok’on yayanta da ya k’yale shi haka duk da yadda ake fad’an rashin mutuncin yarinyar take yaji duk wani burinsa akan d’aukan fansa ya ruguje saima k’ok’arin son kulla alak’a da ita.

Agidan su Maryam kuwa babu abinda ya sauya sai tsarin yawon inda yanzun haj. Zakiyya ce take zaryan zuwar musu wanda idan suka shige d’aka har mantawa ake dasu dakehaj. Amina babu ruwanta da ahiga abinda babu ruwanta bata tab’a sanin wainar da suke toyawaba.

Yayin da MD ya diga ayar tambaya akan wannan ziyarar takawar wannan matar mara yankewa hakan yasa batareda da sanin kowa ba ya nemo CCTV camera saida yabari ranan sun fita gantalin bin malamansu da suka saba yasa aka jona aka saita komai tareda recording d’in duk abinda zai rik’a faruwa akaf gidan ta ko ina har d’akin Ammey batare datasan anyi hakanba.

Rannan MD ya kawota makaranta dake sauri yake abakin get ya sauketa sannan yace idan lokacin tashinsu yayi ta fad’a masa zaisa driver ya maidata gida yau yana da wani meeting wanda sai dare yake tunanin zasu dawo k’ala batace masaba kuma dama yasan basatace d’in ba, bai jira komaiba yaja motarsa da azabar gudu yabar wajen.

A hankali tafara takawa zuwa bakin get d’in tunda tafara zuwa makarantar shekara d’aya kenan da d’an wani abun bai tab’a ajeta anan d’in ba sai yau, ta kusa kaiwa bakin k’ofar kamar yadda ta saba koda yaushe sai ya kaita har parking space na makarantar sannan zai ajeta ya juya.

“Hey hey” taji muryan wanda bazata tab’a mantawa ba arayuwarta domin shine mutum na farko da babu wanda ya tab’a yi mata irin tozarcin da yayi mata, batasan lokacin data saki wani matsiyacin tsaki ba ta juya yayin da shi kuma yayi saurin shan gabanta da motarsa, a mugun fusace ta d’ago ta watsa masa wani mugun kallo sanda yake fitowa daga cikin motar.

Yana k’arasowa bata bari ya fad’a mata wani abuba tayi saurin cewa “wai kai wane irin mutum ne mara tunani wanda baisan darajan kansaba bare na waninsa?
Yau kuma takeni kake sonyi komai?
Wai dan Allah me yasa wasu mutanen baau da tunani ne kwakwalwarsu irin na kifine?
Yo inba hakaba ni banga dalilin gamin kifi da gada ba dazaka wani zo ka shamin gaba ina cikin tafiyana idan kuma hukuncin farko ne bai ishekaba akwai wanda sukafi wannan sai ka jira.

Duk abinda take fad’a bai katsetaba saida yabari tagama maganar ta kafin yace ‘Amincin Allah yatabbata ga sarauniya kuma shugabar masu yafiya, ba wani abune yasa na tareki anan ba sai dan na k’ara neman yafiyarki abisa abinda ya faru duk da nasan cewa saboda ke wannan boss d’in yayan naki ya k’yale ni amma duk da haka ina mai kara neman afuwarki na miki alk’awarin ko kallon banza bazai k’ara had’a ni dakeba pls pls pls” ya rik’a maimaitawa yayin da tayi masifar d’auke kanta ta juya da nufin bar Masa wajen batasan ya akayiba sai kawai ganinsa tayi zube agabanta basa gwaiwoyinsa yana cigaba da rok’on yafiyar ta bai ko damu da yadda mutane suka fara taruwa awajen ba.

Zaro idanu tayi ganin yadda ya zube saman gwaiwoyinsa ga mutane da abin kallo baya musu kad’an har sun fara taruwa awajen tayi saurin cewa “meye haka dan Allah jifa har an fara taruwa anan katashi”

“Ni ba damuwana masu kallona ba damuwana kawai kice kin yafemin”
“Tashi dan Allah” ta fad’a cikin sanyin murya “zantashi ne kawai idan kince kin yafemin”
“Na yafe maka amma bisa wani sharad’i to tashi” tasake fad’a can k’asan mak’oshi da sauri ya tashi yana fad’in”na gode na gode sosai ko wane irin sharad’i ne ki fad’a na miki alk’awarin tunda dai kin yafemin” fad’a yana binta lokacin data fara takawa cikin makarantar,bayan yabawa d’aya daga cikin abokansa mukullin motarsa suna takawa a hankali yayin da ta fara ce masa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button