BABU SO HAUSA NOVEL

BAJININA BACE COMPLETE HAUSA NOVEL

“Kina jina ko?” Ya k’ara sanda yake bud’e k’ofar falonsa, Maryam da take shirin bashi amsa kasawa tayi saboda ganin irin had’uwa da tsaruwan falon kasa daurewa tayi tace “wow gaskiya nima bari Baffa ya dawo wajena daban nima nake so kamar naka”

Ta fad’a tana shigewa cikin falon tana lumshe ido saboda daddad’an k’amshi da sanyin da ya bugi hancin ta sai da ta gama k’arewa falon kallo sannan ta juyo ta dubeshi”waye yake gyara maka wajennan?”
Ta tambaye shi saboda yadda taga wajen kalkal kamar d’akin mace.

D’an murmushi ya saki ya shafi fuskar ta “Ni nake gyara abuna indai ina so yamin yadda nakeso amma yanzun tunda gaki na dunga maleji danaki ko?”

Ya K’are da tambayarta, d’an tura baki tayi gaba cikin shagwab’a tace “hum um ai tunda maneji ne kawai kaci gaba da abunka,
Zo kiga ya fad’a yana jan hannunta zuwa saman benan dake falon, ta bishi har zuwa d’akin baccin shi take taga gado lafiyayye mai kyaun gaske “gyaramin zakiyi yau bani da lafiya” ya fad’a mata yana kallon yanayin ta, kafin ya juya ya fita, tana ganin fitar sa tayi wani irin sufa ta haye gadon tana wuntsilawa, wani irin taushi taji kamar auduga aranta kuwa fad’i take wallahi da sake bari Baffan ya dawo nima komai irin na bross na ke so ji gadonsa dan Allah kamar na wani yar sarkin ta k’ara nutsewa akan gadon.

Shi kam Muhammad har ya sauka ya tuna wayarshi da yabarta tun d’azun saman madubinsa dan haka ya koma ya dan d’aukowa nan ya shagala da kallon yadda take ta faman tsalle tsalle sam bataji motsin shigowarsa ba sai dai maganar sa taji.

“In kin gama Ammey tana kiranki” yafad’a yana d’aukar wayar shi datake saman meerrow ya juya ya fice ya barta batare da ya Kuma kallon inda take ba,

Ita kam sai da ta gaji dan kanta kafin ta gyara har bandaki sai da ta wanke masa kafin ta fito baya falon wani d’aki data gani ak’asan ta lek’a kawai sai taga computers da yawa aciki Maryam da Karam bani sai kawai ta shige kafin takai ga tab’awa sai gashi ya shigo kamar an jeho shi.

Ganin abinda take k’ok’arin yi yasa yai masifar had’e rai yace “me kika ajiyemin aanan” ya fad’a cikin dakakkiyar muryasa data sanshi da ita tun asali.

Maryam da kwata kwata bataji motsin saba sai maganar sa yasa ta juyo a d’an firgice ganin yanayin sa yasa jikinta ya kama rawa tace “nazo ne naga ko kana nan sai banganka ba shi ne shi ne

“Shine kika zo duba ajiyar da kikayi anan ko?”
Ya tambaya a dake take jikinta ya kama rawa ganin yadda yanayin sa ya koma kamar bai tab’a dariyaba

Muje zuwa

MAMAN ISLAM CE
بسم الله الرحمن الر حيم
______________________

FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION

FCWA

{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________
????BA JININA BACE????
2021

          NA

HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI

MAMAN ISLAM

Page 25

“Ni ka dai na min irin wannan Kal lon” ta fad’a a d’an tsorace cikin rawan murya, k’ara tamke fuska yayi yace ” tambayar ki nake me kika ajiya anan?”

“Dan Allah bross ka matsa na wuce kar Mama ta dawo bata ganni ba” ta fad’a idanunta na cikowa da kwalla tana nadamar shigo masa d’akin data lura kamar na sirri ne.
“Kar ki min kuka idan ba hakaba tattaka ki zanyi yanzun anan” ya fad’a cikin dakewa.

Take ta had’iye kukan, tana jiran yabata hanya ta wuce, Saida ya gama hukuntata da mayun idanunsa kafin yaja kunnenta da d’an k’arfi yajata zuwa bangarensu.

Fashewa tayi da kuka domin bada wasa yaja mata kunnen ba sannan Kuma ya k’ara da muguntar murd’ewa, ai Nassar yana hangosu yayi saurin ficewa daga gidan daman ya lura yau yayan nasu akan tsini yake.

Shigan su yayi dai dai da sallamar Mama wadda dawowar ta kenan taga yanda yake ja ma ‘yar ta kunne cikin bala i tace “kai bak’in mugu azzalumi mai tayi maka’ ko kuma muguntar daka saba ne ya motsa sakar mata kunne kar ka tsinka azzalumi mugu”

Ta fad’a tana daga bakin k’ofar atsaye dan tana masifar shakkar sa domin idan ya juye bashi da mutunci acewar mama kenan.

Shi kam yi yai kamar baijiba saida yagama jigata ta kafin ya hankad’a ta jikin uwar ta ya juya ya fice, yana jiyo yadda take ta surfa masa ashar tana tsine masa ya saki wani murmushi mai ciwo yana shafa kwantacciyar suman kansa.

Alwala yayi ya fice masallaci domin lokacin anfara kiran sallar magriba.

Acikin gida kuwa bayan Mama tagama tujaranta ta juyo Kan Maryam tace “ke kuma me kika Masa yake neman lahanta min ke?”

Cikin kuka Maryam tace “wai dan na shiga d’akin compute sa shine fa yazo ya kamani shine tun acan yafaramin bala I”

A firgice tace “na shiga uku ni Sailuba me yakaiki d’akin wannan d’an iskan?
Baby me had’inki dashi dazaki je d’akin shi?
Kodai kin fara shiga sabgarsa ne baby ki rufamin asiri kada ki ruguzamin shirin daya kusa kammala”

Da mamaki Maryam take duban maman nata ganin yadda ta fita hayyacin ta daga cewa ta shiga d’akin MD anya babu wani mugun abinda maman take k’ullawa kuwa?

Girgizata haj. Sailuba tayi da k’arfi tace “Maryam ki fad’a min yaushe kika fara mu’amala da Muhammad?

“Mama ba d’an uwana bane?
Maryam tayi mata tambayar cikin mamaki kafin taci gaba da cewa mama dan Allah ki fad’a min illar hakan naga kin rud’e ko zai iya cutar danine?”

Tayi mata tambayar tana mai wani irin kafeta da ido, take haj. Sailuba ta dawo hayyacin ta tace “ba haka bane baby kinsan in mace da namiji suka keb’e to na ukun su shed’an ne shiyasa kikaga ina kaffa kaffa dake”

Cikin k’osawa da zancen tace “babu ma abinda zai faru insha Allah mama, kuma ni ban tab’a shiga d’akin ba sai yau” boyayyar ajiyar zuciya ta sauke tace “to kar ki k’ara”
“Naji tafad’a tana shigewa d’akin ta domin harga Allah zancen ya gara gundurar ta.

Itama haj. Sailuba tana shiga d’akin ta ko maganar salla bata tsayiba ta lalubo no haj. Zakiyya ya doka mata kira,jim kad’an bayan ta daga babu sallama babu komai tace,

“Na shiga uku na na lalace” cikin rud’ewa haj. Zakiyya tace “lafiya k’awata me kuma ya faru daga rabuwanmu yanzu yanzun?

“Zakiyya’yar iskar yarinyar nan tana neman lalata mana shiri, nace zanyi maganin ta kin hana wallahi zata rusamin shirina na shekara goma sha bakwai adai dai lokacin danake hango nasara na kusantoni”

“Wai duk me yafaru kike irin wannan zantuka kamar na sambatu?” Haj. Zakiyya ta tambaye ta cikin sauri domin tanason tasan abinda ya firgita k’awar tata haka.

Batare da wani jinkiri ba haj. Sailuba ta kwashe duk abinda yafaru daga dawowar ta gidan ta fad’a mata ta k’ara da cewa “inajin tsoron kar su rusamin tsohuwar gabar da na dasa atsakaninsu tsayin shekaru,adaidai lokacin da nake son yarinyar ta kasance mara””””” da kata haj. Zakiyya tayi saurin katse ta “wai kina tantama akan aikin sabon bokannan ne?”

Haj. Zakiyya tayi mata tambayar cikin son karfafa mata gwaiwa” bana shakka amma ina tsoron tugun uban shegiyar matar nan kinsan shima tsohon d’an tsubbu ne”

“Karki damu k’awata idan yanzun yatashi mu atafe muka kwana” nan taci gaba da karfafa mata gwaiwa akan mugun shirin su.

Tana shiga d’akinta ta yi gaggawar shiga wanka domin ana shirin shiga massalaci ne lokacin, wanka tayi ta d’auro alwala ta fito d’aure da tawul bata tsaya wani shafe shafe ba ta zura doguwar riga ta saka hijab ta haye saman abin salla.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button