BABU SO HAUSA NOVEL

BAJININA BACE COMPLETE HAUSA NOVEL

“Gata can bross” Nassar wanda shima yaci kuka ya k’oshi ya fad’a yana nunota tana zaune kan wani dutse data gani abakin hanya jikinta yana wani irin rawa.

Da mugun gudu ya bud’e motar ya fita yana cewa Nassar kar ya fito a cikin ruwan nan, bak’aramin sanyin jikinsa yayi ba ganin yadda ta had’e Kai da gwaiwar ta tana faman shashshek’a, a hankali ya durk’usa agabanta ya dafa kafad’anta.

D’agowa tayi a mugun firgice domin batayi tunanin ma zai dayiba asanin datayi mai na tsantsar rashin mutunci sannan kuma tasan ba wai yana sonsu bane kamar yadda mamanta ta fad’a Mata.

Wani irin kallo ta watsa masa da idanunta da sukayi wani irin ja wanda har lokacin basu daina zubo da ruwa “sorry” ya fad’a can k’asan mak’oshi cikin d’an rawa rawan murya “sorry for what?” ta tambaye shi cikin tsantsar b’acin rai da bak’in cikin abinda yai mata.

“Zo mu tafi” ya fad’a yana kallon yadda ruwa yake tsiyayo Mata tundaga kanta yana kwanrawa kayan jikinta duk sun wani lafe mata ajiki dake ruwa ake tsugawa bana wasa ba, banza tayi dashi kamar bataji me yace ba.

“Dan Allah” ya k’ara fad’a kamar maijin tsoro, yayin da shima sanyin ruwan yafara ratsashi ” ba ruwana da kai kar ka k’ara shiga harkana babu ni babu kai mugu kawai” ta fad’a cikin rawan murya sosai yayin da wani irin sanyi yake k’ara shigarta hatta hak’orinta yana jin yadda suke bugan juna

“Dan Allah” ya k’ara fad’a kamar zai mata kuka mak’e mai kafad’a tayi tace “um um na tsan……….wani irin fisgota yayi kafin ta k’arasa ya had’e bakinsu waje guda yana mata wani irin shan mugunta sai da ta raina kanata kafin ya sakar mata bakin cikin wani irin b’acin rai yace “sai wancen dan iskan saurayin naki ne baki tsanaba ko?
Ni kikewa wannan abun akan na nuna b’acin raina akan kina kula wani banza can daban ko na gode” ya fad’a muryan shi na d’an rawa kad’an.

Sai yanzu ta gane dalilin dayasa ya gane mata wannan bala in yabarta a cikin tashin hankali da tsoro jitai ranta ya dad’a mugun b’aci zuciyar ta ya wani irin dakewa ta mik’e kawai ta kama tafiya dan taci alwashin bazataje a motarsa ba “ke meye haka?” ya fad’a cikin d’an tsawa tsawa ko kallon inda yake batayi ba taci gaba da tafiya.

Duk irin yadda yaso rarrashin ta abin gagara yayi hakan yasaka shi tattare hannun riga ya sunkce ta tana wuwulla k’afa tana komai ya nufi mota da ita

Plss manage

MAMAN ISLAM CE
بسم الله الرحمن الر حيم
______________________

FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION

FCWA

{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________
????BA JININA BACE????
2021

               NA

HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI

MAMAN ISLAM

Page 27

Bud’e motar yai ya wulla baya kusa da Nassar sai uban kuka take jijiyan kanta sunyi wani rud’u rud’u fuskar nan tayi jajur tsabar kukan da takeci.

Shiru Nassar yayi yana kallon yadda Adda nashi take kuka ga ruwan dayake ta faman diga daga jikinta rawan da jikinta yake kawai ya tabbatar masa da akwai zazzab’i atare da ita.

MD tuk’in yake amma ba acikin nutsuwa ba domin ba k’aramin bugun zuciyar sa kukanta yake ba ko kad’an baiji dad’in abinda yayi mataba sai dai ko kad’an zuciyarsa ta kasa amsar laifin ganinsa bai kamata ace ta tsaya magana da wani k’aton agabansa sosai abin ya masa zafi aransa, wata zuciyar Kuma cemai tayi inbanda abinka kasan waye da har zakayi saurin fushi haka “zai wuce d’an iskan mate d’in nan nata” ya fad’a asarari Kuma da k’arfi, duk suka bishi da kallo har Maryam datake kuka sai data tsagaita jin yadda ya bugi sitiyarin da mugun k’arfi.

Suna zuwa gida taba tsaya amsar wayanta ba ta balle murfin motar tayi cikin gida da gudu tana shashshek’a ta wuce mama da Ammey a falon duk suka bita da kallo, saida tasawa d’akin key tasan sarai sai Mama ta biyota jikak’k’un kayan ta cire ta shiga ta had’a ruwa mai mugun zafi har lokacin rawan sanyi take sosai ta shige cikin ruwan tana faman sauke ajiyan zuciya sai da ta gasa jikin ta sosai kafin tayi wanka ta fito ta shafa mai ta haye gado ranan bata had’u da Baffanta duk da irin yadda tayi kewansa.

Washe gari ma bata fito da wuriba sai da ta gama duk nuk’u nuk’un ta sannan ta salla wanka ta ta tsara kwalliya mai kyau da d’aukan hankali ta fito cikin nutsuwar ta duk suka bita da kallo har tayi wani fayau da ita.

Baffa ya dubeta yana murmushi ya mik’a ta hannu”zonan ki zauna, ya fad’a yana nuna mata gefensa nayi kewan ku sosai yarana” ya fad’a yayin da tasako hannunta cikin nashi ya zaunar da ita a kujeran kusa dashi.

Tunda ta fito ya kafeta da ido sai yaga ta k’ara masa wani fitinannen kyau, gaida iyayen nata tayi, kamar ta share shi sai kuma ta gaidaahi cikin sanyin murya amsawa yayi yana k’ureta da ido, tai masifar had’e rai tana had’a tea.

Su Mama suna gama karyawa suka bar wajen suka koma falon Baffa da akwai abinda suke son tattaunawa.

Yana ganin fitar su ya ture nashi abincin ya kwantar da kansa saman tebur d’in yana binta da wani fitinannen kallo Nassar na ganin haka ta d’auke ragowar abincin sa yabar wajen.

Gaba d’aya ya takura da wannan banzan kallon nasa sai dai bata son tayi abinda zai gane hakan, kasa cin abincin tayi sai ruwan shayin da take ta karb’a tashi yai ya dawo kusa da ita kofin shayin ya karb’a daga hannunta ya zauna ya kai bakin ta, d’auke kanta tayi tareda k’ara tamke fuska.

“Kiyi hak’uri dan Allah, ya jikin naki?” ya fad’a yana shafar gefen fuskar ta, banza tayi da shi idanunta yana cikowa da hawaye ko abinda d boy yai mata bai sosa mata rai kamar na MD ba.

Juyo da fuskar ta yayi kusa da shi yana k’ara kai mata abincin bakinta “karki min kuka, kiyi hak’uri dan Allah” ya fad’a cikin sanyin murya, batare da tace k’ala ba ta yunk’ura zata bar masa wajen ya daka mata tsawar dayasa ta koma ta zauna batare da tasan tayi hakan.

“Wallahi yanzu sai na tattaka ki dan kinga ina lallab’a ki shine kike neman ki kawo min rainin hankali karb’i dalla malama” ya fad’a yana kai mata abincin baki ganin yanda yai kicin kicin da rai yasa ta bud’e bakin ya zuba mata abincin haka ya dinga bata tana karb’a tana hawaye har saida ya tabbatar ta k’oshi kafin ya bata ruwa tasha ya kama hannunta ta suka nufi part d’insa.

Duk jiya bai iya runtsawa ba saboda tunanin abinda yayi mata iya binciken sa nason gano dalilin yi mata haka amma amsar d’aya ne tayi waya da wani agabansa dalilin fushin sa akan hakan simple words INA SON TA duk ta yadda ya juya al’amarin amsar d’ayace abin ya masifar tayar masa da hankali bai tab’a tunanin hakan daga zuciyar saba sam batayi masa adalci ba kuma ta zalunce shi tayi mai abinda zai hana shi cika alk’awarin daya daukarwa Baffa, dan iya jiya kawai ba k’aramin tashin hankali ya shiga ba ganin halin data shiga sosai ya bama kansa laifi akan abinda yayi Mata.

Suna shiga falon ya zaunar da ita saman kujera ya zauna kusa da ita ya kamo hannunta yana murzawa a hankali wanda hakan yasa taji wani irin yarrrrrrrr ajikinta da k’arfi ta k’wace hannunta ga mamakinta sai ji tayi yace “bani da lafiya” shine abin taji ya fad’a cikin wata irin murya wadda take taji wani irin kasala ya rufeta saboda salon dayai maganar kasa ce masa komai tayi sai ma k’asa da ta maida kanta tana faman cukwaikwauye gefen d’ankwalin doguwar rigan da yake jikinta

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button