BABU SO HAUSA NOVEL

BAJININA BACE COMPLETE HAUSA NOVEL

“Ni kaina bansan abinda yasa nayi miki hakan ba princess nasan ban kyautaba abinda nayi, abin yayi mugun damuna na rasa yadda zanyi na kasa runtsawa saboda neman dalilin da yasaka nayi miki hakan, sai dai dalilin dana samo bai min dad’i ba ko kad’an Maryam” ya k’arasa da kiran ainihin sunanta wanda sai yaune ta tab’a jin ya kira sunanta iya tsawon rayuwar ta, sai taji wani iri aranta sai dai bata d’ago kaiba bare tace wani abu.

Ga mamakinta sai ya kamo fuskar ta ya juyo da ita saitin tashi ta d’an kafe shi da ido yadda taga yayi mugun yin kalar tausayi idanunsa da ta kalla kuwa sai da gabanta yai masifar fad’uwa da sauri ta mai da kanta k’asa.

Abinda ya k’ara bata tsoro yadda ya zame ya durk’usa agabanta yana kallon cikin idonta yace “dan Allah princess in rok’i wani alfarma a wajen ki?”

Yadda yayi matan ne yasaka batasan sanda ta d’aga masa kai ba alaman shi take sauraro ” dan Allah princess ina so na zama amininki na k’ut da k’ut yanda komai zakiyi sai kin sanar dani nima duk abinda zanyi sai na sanar dake sannan dan Allah yaron jiya kar ki k’ara d’aga kiran shi namayi blocked d’insa dan Allah kimin wannan”

“Aini bazan iya abota dakai ba kai mugune baka da tausayi daman ai su sojoji basu da imani shi yasa na tsan”……….bai bari ta k’arasa ba yayi saurin rufe mata baki da hannunsa cikin sanyin murya yace “zokiji Allah na daina daga yau bazan kara b’ata miki rai ba”

Idan na tabbatar da hakan sai na zama friend d’in naka amma ni yanzun banyin abota dakai yasin dan zaka iya kashe ni wata rana ai dama Mama tace komai dad’in ka da ‘yan ” ke”

Ya buga mata wani shegen tsawa “wallahi kika Kuma min zancen d’an ubannan sai na sab’a miki kammani yanzun nan haba kin ishe ni da wani’yan uba’yan uba’yan uban…………ya dank’aro k’aton asher ya dank’ara kafin yaci gaba da fad’in duk wanda yasa miki wannan tunanin jakine shi dabba ne mai kwakwalwan kifi Kuma daga yau ina so kisa aranki cewa baki da wani d’an uba duk uwa d’aya uba d’aya muke agidannan tashi ki fita” ya fad’a cikin daka mata tsawa yana nuna mata k’ofa ai da gudu ta fella cikin rawan jiki dan yanayin sa ba k’aramin firgita ta yayiba.

Komawa yayi saman kujeran da ta tashi ya zauna tare da kwantar da bayansa yana fitar da wani mugun huci me azabar zafi aduniya bai tab’a ganin matar daya tsana kamar Sailuba ba ya tsane ta ya tsane ta ya tsane ta har baisan yadda zaiyi ba

MAMAN ISLAM CE
بسم الله الرحمن الر حيم
______________________

FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION

FCWA

{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________
????BA JININA BACE????

2021

             NA

HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI

MAMAN ISLAM

. page 28

Tana shiga d’akinta ta mai da k’ofar ta rufe kamar ance ya biyota ne, k’arasawa tayi bakin gado ta zaune tareda dafe k’irjinta da har lokacin bai bar bugawa ba ta “jarababbe kawai mutum babu abinda ya aje sai masifa ta fad’a tana kwanciya akan gadon bata jimaba kuwa bacci yayi awon gaba da ita.

Tunda ya zauna ya lumshe idanunsa zuciyar sa na masa zafi, so yake kota wane hali sai ya raba Maryam da haj. Sailuba domin wannan matar bata da maraba da matar shed’an muguwar hatsabibiya ce tasan takan mugunta shi kansa yana tsoron shirin da take kan ‘yar mutane domin yafi kowa sanin cewa ba rainon banza haj. Sailuba tayi wa Maryam ba dan bata aikin banza shi yasa yake son ko ta wane hali ya yakice Maryam daga jikinta kafin ta kai ga halaka ta.

Ganin zaman sai k’ara bijiro masa da wasu irin tunaninka yake yasa yai wanka ya bar gidan.

A falon Baffa kuwa bayan sun gama d’an tab’a hiransu kamar yadda suka saba Baffa ya d’an dubi matan nasa yace “yau ina so naje k’auye ba kuma zan dawo yau d’in ba sai Allah ya kaimu gobe”

A matuk’ar firgice haj. Sailuba ta d’ago tana duban Baffa cikin tashin hankali yaushe tayi wannan saken ca take ta riga da tagama da babin wannan tsohuwar me shegen taurin kan tsiya ai kuwa zata gyara mata zama yanzu dai ba ta ita take ba ta wannan ‘yar matsafin mutumin da aiki baya cinta take.

A fuska ma nunawa tayi tafi kowa murnan zuwansa a bad’ini kuwa ji take kamar tayi ta ihu domin har ga Allah tun lokacin da Inna ta bada shawarar ayi mata kishiya ta sha alwashin sai ta d’an d’ana mata guba fiye da wacce ta d’an d’ana mata.

Sai da ya fara zuwa wajen malam Babba kamar yadda ya saba yauma saida ya bashi rubutu yasha ya shafe jikinsa sannan yake bashi a duk lokacin dayake gari, kafin ya sanar dashi zaije ganin gida ba k’aramin dad’i malam yajiba domin hasashen shi yazama gaskiya cewa Baffa rabashi ake son yi da mahaifiyarsa shi yasa yaji sam baya son zuwa, amma duk wanda yake wannan abun sam bai kyautawa kansa ba.

Bayan fitar Baffa babu jimawa itama ta shirya ta fice bata zame ko ina ba sai wajen bokanta kasancewar haj. Zakiyya sunbar k’asar da mijinta yasa batama tsaya b’ata lokacin tab’a ta wuce abin ta.

Bayan tagama korawa bokan ta bayanin aikin da take son yayi mata ya jima sosai yana zane cikin k’asa kafin ya d’ago ya dubeta yace. “akwai abubuwa da yawa wanda kika jima kina k’ullawa duk tunaninki basa yiyuwa?”
Ya fad’a yana kallonta, shiru tayi domin batayi tunanin aikin da take yana ciba dan bata ganin nasara a ciki.

Aikin ki yana ci kuma abubuwan da kike sunyi yawa kuma duk ta sigar da kika d’auko hanyar wargaza komai tanan zai wargaje zaki sha mamakin rana da lokaci da waje amma kuma akwai cin amana da bayyanuwar asirinki daga baya daga wajen mutum mafi kusa dake wannan shine ki tashi kije da baya banda waiwaye daga yau bazai k’ara zuwa wajen uwarsaba sai dai ita tazo shi da garin nan sai dai yaje gaisuwar ta bayan ta rasu.

Tunda takwanta take waau irin mafarkai marasa kan gado sosai take jujjuya kai tana gumi babu abinda yafi rud’a ta sai tsintar kanta da tayi a wani a hali mara dad’i tana cikin jujjuya kai kamar wacce aka tasa ta bud’e ido a firgice, sai da tayi addu’ar tashi a bacci kafin ta mik’e cikin tashin hankali ta hau karanto hasbinnallahu wani imal wakil sosai abin ya tsaye Mata arai.

D boy ne a office d’in babanshi suna hira yake sako masa maganar Maryam Abba AL HASSAN yace ” ‘yar waye?”
” ‘yar Baffa Abubakar ce”
” Kai k’arya ne wallahi badani ba ka rasa wa zaka d’auko min a matsayin suruka sai k’anwar wannan bom d’in wallahi ba isa ba baka isa ba nace dan ubanka”

“Ni wallahi Dad ita nake so dan haka banga wanda ya isa hanani aurenta ba waima Dad meke tsakaninka da yayannata ne naga ko sunan su kaji saika firgita?”

“Ban sani ba dan uwarka kuma muddun nine ubanka ban yafe maka auren wannan irin masifar ba”
” Muddun kaga ban aure taba ka tabbatar mutuwa nayi amma kai baka isa hanani auren taba wallahi” ya fad’a cikin dukan teburin tsakiyar su cikin murgud’a baki kamar wani sa ‘ansa,

Wannan ba komai bane a wajenshi dan al amarin gidan Abba AL HASSAN babu tarbiyya ko kad’an da gaba d’aya sun gama sangarta d’an nasu kasancewar shi kadaine d’an da suke da.

“Tunda haka kace to wallahi babu ruwana duk abinda ya biyo bayan ka kar kasawa ranka cewa na san ka dan wallahi ko kallon inda kake bazanyiba.

“Ba damuwa” Kamal ya fad’a yana ficewa daga office din

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button