BABU SO HAUSA NOVEL

BAJININA BACE COMPLETE HAUSA NOVEL

“D boy ne yaron daya dakeni a schl”
“Meye hadinki dashi?”
Sai data d’an K’are Masa kallo, irin kallon dayake binta dashi sai kace wani tsohon maye yasa tayi saurin d’auke kanta.
“Mutunci ne tsakanina dashi?”
Ta amsa tana jan tsaki aranta ganin yadda ya fitineta da kallo.

Juyo da fuskar ta yayi saitin tasa ya k’ura mata ido yana mamakin furucin ta lallai ta sauya ba dan kad’an ba tunda har ta kula d boy wanda yagama wulak’anta ta a bainar jama’a.

“Amma baki da zuciya princess, mutumin da ya gama gurza miki rashin mutuncin a tsakiyar makarantar ku ke yamzun har akwai wani mutunci da zai had’a ki da shi?”

Shiru tayi saboda kallon da yake mata ya masifar ta kurata dan har jikinta ya d’an soma rawa rawa.

“Ni kadaina min wannan kallon” ya tsinci muryanta da yayi can k’asa sosai tana fad’a, kallon ya cigaba da binta dashi yayin da ya dad’a kusanto da fuskarta daf da tashi wanda har suke iya jin saukar numfashin juna.

Take jikinta ya kama rawa ta soma k’ok’arin kwace fuskar ta daga hannunsa, sai dai bai bata damar hakan ba dan ya rik’e ta gam

“Babu abinda yafi min dad’i kamar kallon ki kuma hakan yana saukar min da nutsuwa sosai, dan Allah Kar ki haramtamin kallon fuskar ki yin hakan zai cutar dani sosai.

Yanzu kam gaba d’aya ta ware idanunta akanshi Al ‘amarin bross d’in nasu ya fara bata tsoro anya bai samu wani ciwon ba kuwa?
Yadda yake mata d’innan gaskiya ya kamata a bincike shi

“Zaki iya min wani alfarma?”
Ya tambaya yana cigaba da kallon ta kuma har lokacin bai saki fuskar ta ba,
“To kasakar min fuskana sai muyi maganar”
Kamar zai ce wani abu sai kuma ya fasa ya sake tan kamar yadda ta buk’ata, ya kwantar da kansa jikin kujeran da suke kai yana maida numfashi.
Kafe shi tayi da ido aranta tana mamakin yadda yake da zallar kyau da mugun kwarjini.

Tana tsaka da kare masa kallon ne ya ware idonsa akanta yadda take binsa da kallo ya bashi mamaki
“Yadai yarinya? Irin wannan kallo haka ai sai kisa naji kunya” ya fad’a yana d’an gyara zamansa.

Ai kuwa wani irin fitinanniyar kunya ne ya kamata yadda ya kamata dumu dumu tana K’are masa kallo da k’arfi ta runtse idonta gam gam, yasaki wani murmushi ya d’an matsa daf da ita batayi aune ba sai ji tayi ya sakar mata wani kasalallen kiss a idanunta ai da sauri ta yunk’ura zata gudu bisa ga tsausayi sai taci karo da kayan da Hajara ta ajiye mata tun d’azu, saura kad’an ta kife wajen yayi wani irin fisgota ta fad’o jikinsa, wani irin ajiyar zuciya suka sauke atare.

K’ank’ame ta ya kumayi acikin jikinsa yana sauke wani irin numfashi wani irin abu na mai yawo acikin jikinsa ji yai wasu irin hawaye suna k’ok’arin zubo masa wanda bai san dalilin faruwar su ba.

“Zaki aure ni?”
Ta tsinci muryarsa da yayi wani irin mugun sanyi, a wani irin firgice ta d’ago kai tana kallonsa, har lokacin idanunsa a rufe suke gashi ya wani irin cukwaikwauye ta, shikenan hasashen ta ya tabbata yayanta yana da matsala banda haka ina aka tab’a auren JINI D’AYA?

K’ok’arin kwatar kanta ta soma amma ko gezau saima k’ara rik’e ta da yayi
“Ki bari mu fahimci juna dan Allah princess ina son na aureki zaki aure ni?”
Ya kuma k’arasa zancen da tambayarta, jitai hankalin ta yai masifar tashi take maganganu Maryam wanda su yi dad’ewa ya soma dawo mata inda take ce mata
“Da kyar inba sonki wannan bross d’in naku yake ba yadda yai mugun saka miki idonnan da alama dai bazai bawa wani daga waje damar d’auke masa wannan tsaleliyar budurwar ba”

Sanda maryam tai maganar hararan ta tayi tace “da alama kin sami b’acewar tunani name sake banda haka babanmu fa d’aya da kike wannan zancean aman babu tashin zuciya” ta k’arasa tana wani irin kallon Maryam d’in da kuma yin kamar da gaske aman zatayi.

A lokacin murmushi Maryam ta sakar mata tace “ai lokaci zai nuna kuma kinsan lokaci baya k’arya”

“Hmm amma wallahi name sake ban tab’a tunanin kina da tab’in hankali ba sai yau”

“Zaki ce na fad’a miki wallahi kallon SO bross yake miki bana sister ba kuma zaki tabbatar da magana na wata rana”

Ji tai wani irin fad’uwar gaba ya rikito mata lokaci guda ta ware idanunta akanshi tayi wani mugun tureshi da k’arfi ta mik’e daga jikinsa, ta doshi hanyar fita hankali tashe.
Shima ji yai hankalinsa yayi mugun tashi ya bita yana kuranta bata ko juyo ba bare yasa ran zata amsa sai ma wani maganar na Maryam da yake dad’a dawowa kanta a yanzun.

“Ki duba da kyau Ammey batayi shekarun da zata haifi mutum kamar bross ba sai dai ko k’aninta kuma idan kinje gida ki tambayi Mama”
Tsayawa tayi a jikin motar MD ya k’araso yana kallon ta hankali tashe’ yayin da Hajara da m Bash ma suka fito domin yadda MD yake kwala kiran Maryam princess princess ba na lafiya bane sai dai duk nacin m Bash wajen son jin abinda ya had’a su babu wanda ya tanka musu

Da k’yar Maryam ta iya d’ago idanunta da sukayi mugun ja tsabar damuwar daya kawo mata farmaki lokaci guda ta kalli Hajara ta daga mata hannu har da murmushin k’arfin hali tayi mata.

Shi ko MD bai iya yace komaiba ya figi motar da mugun k’arfi,duk da yadda hakan ya kad’ata yadda taga yana musu ganganci da rayuwa, amma bata d’ago ba saima mai da kanta datayi k’asa batare data shiryawa hakan ba wani fitinannen kuka ya kwace mata, wani irin wawan burki ya taka wajen wasu bushiyoyo ya faka ya kafeta da ido kafin a hankali ya d’ago da kanta yana kallon yadda take rusgar kuka sai kace wacce aka ce mata Baffa da Ammey ne suka mutu

“Ki rufamin asiri dan Allah ki tausayawa zuciya ta ki daina kukan nan haka”
Kallonsa ta kumayi yayin da kukan ya dad’a kwace mata wanda shi kukan nata yafi komai d’aga masa hankali
“Pls” ya fad’a a hankali amma ina bata saurare shi ba “dan Allah” ya kuma fad’a a hankali yana d’an janta kusa dashi ya soma share mata hawayen da k’yar yasamu tayi shiru amma bata ce masa kanzul ba.

Har sukaje gida bata k’ara yarda ta tanka masa ba duk irin yadda yake rarrashin ta kuwa,
Yana fakawa ta balle murfin motar tayi cikin gida da sauri ko kayan da suka siyo bata tsaya d’auka ba, binta yayi da kallo har ta shige kafin yasaki wani irin ajiyar zuciya mai k’arfin gaske.

Har lokacin Mama bata dawo ba dan k’ofar ta yana nan a yadda ta barshi da zata fita wani irin mugun tsaki tasaki wanda yasa Ammey dake fitowa daga d’akin ta zata shiga kicin, da kallon mamaki Ammey ta bita ganin yadda tayi mugun fita a hayyacin ta.

“Ke lafiyar ki ‘kalau ina yayan naki?”
Ammey ta k’arasa tana tambayarta ta fad’awa tayi jikinta tare da fashewa da kukan da yake ta cinta, rik’o ta Ammey ta yi hankali a tashe tajata zuwa d’akin ta zaunar da ita tayi abakin gado ta d’ago kanta tana share mata hawayen kafin tace
“Me yafaru, ko wani abunne ya samu yayan naki?”
Girgiza mata kai Maryam ta yi ” to me ya faru?” ta k’ara tambayar ta hankali tashe ” Ammey kece kika haifi Muhammad?”
Maryam ta tambaya tana kafe Ammeyn da idanunta da suka kad’a sukayi jajur,

“Me ya faru da har ya daga hankalin ki haka kike min wannan tambayar? ji dan Allah yadda ki koma ji yadda idanunki yadda suka kubura tsabar kuka, bana san haka karki karamin irin haka ji yadda kika tashi hankalin ki nima kika tayar min da nawa?”

Duk abinda yafaru ta kwashe ta fad’a wa Ammey, wani irin sanyi ne ya kwaranya mata arai ta rungumeta tana fad’in “yanzu ke dan wannan abun kike tayar da hankalin ki ai wannan ba abun tada hankali bane Kinga shikenan zai samu mai kula dashi ko”?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button