BAJININA BACE COMPLETE HAUSA NOVEL

Ammey ta d’igawa dogon sharhin ta aya “kamar ya zai samu mai kula dashi ban gane ba Ammey?”
Eh kinsan Abban ku Hassan?”
Na garin su Inna?”
Itama ta tambaye ta
“Yauwa d’iyar albarka shifa ina d’an sa da matarsa ta haifa ta mutu ta barshi?”
“Ba ance yana k’asar waje karatu ba?”
“An fad’i hakane kawai saboda wasu dalilai amma ba kowa bane face Muhammad”
Idanu Maryam ta zaro duka waje tana kallon Ammeyn da madaukakin mamaki
” Hum shine” Ammey ta fad’a tana daga mata kai ganin irin kallon da Maryam take mata.
Nan ta bata labarin MD kamar yadda Baffa ya bata tundaga haihuwar sa da mutuwar mamansa wanda ko abinda ta haifa bata sani ba da yadda Inna ta raune shi har ya girma da yadda matan banansa suka soma azabtar da shi duk da cewa ba gida day’a suke ba har dai MD ya fara wayo ya daina zuwa gidan har zuwa d’auke shi da Baffa yayi har yanzun da yazama wani abun sosai Maryam taji tausayin sa yayi wani irin kamata Allah sarki bawan Allah shi baima tab’a ganin mahaifiyar sa ba ta ayyana aranta “Allah ya jikanta da rahama” ta fad’a tana share guntun hawayen da ya zubo mata
“Amen” Ammey ta fad’a tana shafar kanta kafin tace “maza jekiyi wanka kiyi salla kinga lokacin ta ya shiga Kuma yanzun hajiya zata iya shigowa tunda magriba yayi kar ta ganki anan”
Batace komaiba ta fice a d’akin.
Taku ce
MAMAN ISLAM
بسم الله الرحمن الر حيم
______________________
☀ FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION ☀
FCWA
{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________
???? BA JININA BACE????
2021
NA
HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI
MAMAN ISLAM
Page 32
Tana fitowa daga d’akin daidai shigowar haj. Sailuba, idanunta k’yar abakin k’ofar Ammey dan sam bata son had’uwa da kowa wannan shine sa ar aikin ta na yau tana ganin Maryam da bata kula daga inda ta fito ba ranta yai masifar b’aci babu makawa wannan la’a nanniyar yarinyar ta b’ata mata shiri.
Tsawa ta buga mata tace “ke dan ubanki daga ina kike bana hanaki mu a’mala da wadannan matsiyatan ba?”
Da kallon mamaki Maryam ta bi mama wadda tun kafin ta kai karshen maganar ta ta gano kuskurenta tayi saurin fuskewa dan kar ta gano ta, amma duk da haka sai da Maryam ta hango tsantsar tashin hankali atareda maman tata.
“Lafiyan ki kalau mama?”
Kallonta mama ta d’an yi cikin alamun rashin gaskiya kafin ta wuce b’angaren ta cikin tsantsar tashin hankali.
Tana shiga bata bi ta maganar sallar magriba da ake ta kwad’awa a masallaci ba ta zari waya jikinta har rawa yake ta dannawa haj. Zakiyya wacce ita shigarta nata gidan kenan kira da mugun mamaki ta d’aga kiran tana cewa.
” Ya akayine k’awata ko zama banyi ba sai ga kiranki?”
” Na mutu zakiyya, shikenan kuma nawa ya K’are na shiga uku zakiyya da wannan la’ananniyar yarinyar na fara karo wacce boka yace har gwanda naga kowa dana fara ganinta?”
Ta fad’a cikin rushewa da wani fitinannen kuka cikin tashin hankali.
Ita kanta wani irin fad’uwar gaba ne ya rufeto mata agigice tace
“Ke kuwa Sailuba wanne gangancinne yasa kika bari kuka had’u?”
“Cikin kuka tace wallahi nima bansan zamu had’u da itaba kawai ina shigowa mukayi kicib’us”
“Allah yasa bakice zakiyi mata fad’a ba dan gudun kar kija mana matsalar kuma”
“Nayi, sai dai kafin na dire na gano kuskurena nayi saurin fuskewa”
Nan dai suka fara tsara yadda zasu sabunta shirin su tunda wannan ya ruguje.
Ganin yadda maman ta d’aga hankalinta har tayi hanyar d’akin sai kuma ta fasa aranta tace ai kina da kud’i zaki sha kan matsalar, ta juya ta shige d’akin ta batare da wani damuwa ba ta shiga wanka a gurguje tayi wanka ta fito ta kabbara salla bayan ta idar ta d’an yi kwalliya sama sama ta fice, duk suna wajen cin abinci kamshinta ne ya sanar dasu zuwanta, duk suka bita da kallo babu MD awajen duk sai taji babu dad’i dan tun d’azu take ta faman juya labarin da Ammey ta bata nasa tana da tausayi duk da kasancewar ba wai yasha wani wuya na azo agani ba amma rashin mahaifiya ba d’an k’aramin gib’i bane ga rayuwar yaro.
Tana shirin zama Baffa ya dakatar da ita yace taje ta dubo yayanta ko lafiya dan tunda ya shigo bai ji motsin saba, jitai gabanta ya wani buga da k’arfi take abinda ya faru agidan m Bash ya dawo mata sai dai bata da damar yiwa Baffa musu hakan yasa ta fasa zaman ta juya kamar kazar da kwai ya fashe wa aciki tayi waje duk suka bita da kallo yayin da Mama ta saki wani arnen tsaki tsanar yarinyar yana k’ara tasiri aranta, duk suka bita da kallo, basu kawo komai aransu ba tunda sunsan yadda ta tsani MD.
Tana tunkaran wajen bugun zuciyar ta yana k’ara yawaita sai da tashafe kusan 5 mint kafin tayi k’arfin halin kama mabud’in k’ofar ta tura a hankali kamar mai jin tsoron wani abu,
Tunda ya dawo salla yake zaune saman doguwar kujera ya jingina bayansa jikin makarin kujeran idanunsa a lumshe bai tantan ce halin dayake ciki ba abinda kawai zai iya ganewa itace ta cika masa zuciya duk inda zai motsa ta tokaresa.
Jin motsin bud’e k’ofar yasa ya maida hankalin sa wajen k’ofar shima bugun zuciyar sa yana kara yawaita bugu ya wani irin kafe k’ofar yay da kallo, a hankali ta shigo bakinta d’auke da siririyar sallama da k’yar ya iya dai daita kansa ya amsa yana dad’a binta da kallo ta d’an kalleshi suka had’a ido bata san sanda ta galla masa harara ba sai ya saki murmushi ya sani sarai takura ta yayi gashi ita kuma babu hak’uri shi yasa.
Bata san tasowar saba sai tsintar sa tayi agabanta ya dafa kafad’anta “babyna me kike sone kika ja kika tsaya anan ki shigo mana?”
Kallo ta bisa dashi mai kama da harara kafin tace “ni ba babyn ka bace, Baffa ke kiranka yace tunda ya shigo baiji motsin ka ba lafiya kuwa?”
“Inafa lafiya an shake min wuya da mugun k’arfi na kasa koda hadiyar yawu” binshi tayi da kallo mai kama da na tausayi dan sam bata gane me yake nufi ba tace “kasha magani me yake damun ka bross?
“Ke ce, ya bata amsa cikin bazata kece damuwa ta, kece tunani na, kece jina, gani na, walwala na, kuma jin dad’i na, Maryam kece komai na” yafad’a cikin muryan daya mugun karyewa ta daga kai tana kallonsa duk yayi wani iri ga damuwa nan kwance acikin idanunshi
” Kazo muje”
“Kije zanzo yanzu”
“Ni dai Baffa yace k’afa na k’afar ka”
“To jira nayi wanka”
Daga haka bai k’ara cewa komai ba ya haye saman sa da gudu.
Cikin 20 mints ya sauka sanye cikin blue jeans da riga ruwan toka kayan sun mugun amsar sa kunsan farin mutum kuma mai kyau duk shigan da yay amsar sa yake.
Tana can yawon kalle kallen ta a falon taji ya rik’o hannunta binshi tai da kallo yadda yayi mata kyau ga wani fitinannen k’amshi dayake yi ma mugun dad’i, har sukaje bakin falon babu wanda yace da d’an uwansa komai sai itace ma da suka zo bakin falon ta warce hannunta daga cikin nasa ta wuce ciki abinta murmushi ya d’an saki kafin ya rufa mata baya
Duk su Baffa suka bisu da kallo yayin da zuciyar haj. Sailuba kamar zaiyi bindiga tsabar fitina da tsanar ganin Maryam daya Kuma mamaye ta Baffa yace “maman malam daga aike kuma sai najiki shiru?”
Rasa me zata cewa Baffa tayi sai ta d’ago ta dubeshi shima ita yake kallo, kafin ta lalubo abin fad’a yay saurin cewa “sanda taje ina wanka”
“To ku gama cin abincin akwai maganar da zamuyi daku duka”