BABU SO HAUSA NOVEL

BAJININA BACE COMPLETE HAUSA NOVEL

Sosai ta rarrasheta tace tunda abin haka ne kawai ta shirya cikin satin nan su wuce India can ne za ayi musu aiki mai kyau sun jima suna tattanawa kafin suyi sallama, sai lokacin ta d’an samu sassauci

Maryam kuwa d’akin ta ta koma cikin damuwa tasani cewa Mama bata kyautaba ko kad’an amma Kuma ita meye laifin ta da zai wani rufe mata k’ofa.

Ganin zaman bazai mata ba kawai ta mik’e ta saka mayafinta da niyyar taje wajen Halima ko zata d’an rage damuwa, daidai bakin get suka had’u da Baffa ya hanata fita dole ta dawo gida cikin k’unci.

MD kuwa tunda da yake babu Wanda ya tab’a zagar masa uwa ido da ido sai yau hakan ya masifar k’ona shi da k’yar yasamu ya rarrashi kanshi ya baro falon shi yasa ya kulle kanshi domin a halin dayake ciki baya buk’atar kusanci ga kowa atare dashi.

Ammey kuwa cikin fushi ta koma d’akin ta ranta a masifar b’ace tasha alwashin bazata k’ara yarda Sailuba ta rik’a juya ta ba tunda babu adalci a lamarin itama ya zama dole ta zage ta kwatar wa kanta yanci.

Haka da ranan mutanen suka kwana kowa zuciya babu dad’i da safe da zasu wuce islamiyya hankalinta yana kan k’ofar sa bata taba alamun ya bud’e k’ofar ba, sai ta tab’e baki a k’ok’arin ta nasan yakice tunanin shi aranta tunda shima fushi yake da kowa na gidan.

Sai dai duk irin yadda taso kore tunaninasa aranta hakan yak’i samu sosai tayi sanyi dan ko k’awayen ta na islamiyya sai da suka gane tana da matsala, sanda suke dawowa daga islamiyya shi kuma ya fito daga d’akin dake lokacin an yi kiran Azhar ne sai da ta d’an razana ganin har ya d’an fad’a daga jiya zuwa yau kacal bata kulashi ba ta d’auke kanta, Nassar ne kawai ya gaida shi, ya bita da kallo har tashiga ciki kafin ya juya ya wuce masallaci.

Koda ya dawo shima cikin gidan ya dawo lokacin har sunyi zaman cin abinci banda haj. Sailuba datake d’akin ta tun juya shima wajen ya tunkaro duk suka bishi da kallo har Baffa wanda yay mamakin ganin shi hakan Ammey tafi kowa shiga damuwar ganinsa a hakan.

K’arasawa yayi ya gaida su kafin shima su Maryam suka gaida shi Ammey ta zubawa kowa nasa abincin amma MD da kanta ta fara bashi dan ta riga tasan halinshi muddun yana cikin damuwa baya iya cin abincin sai dai yayi ta fama da tunani tana cikin bashi ya tsinci muryanta tana fad’in.

“Muhammad yakamata ka gane halin wannan matar ina rok’on ka daga yau komai zai faru kada ka k’ara cewa komai ka barta komai lokaci ne dan haka wata rana sai labari” sosai taci gaba da da tausar shi har ya kammala, itama Maryam ta tubure sai da ta bata itama kafin su bar wajen ta bisu da kallo.

Hannunta da Baffa ya kamo ne yasa ta juyo babu wannan walwalan dayaga tana yima yaranta yanzu, ya d’an murmusa yace “haba maratussaliha dan Allah ki saki ranki tun jiya ake fushi dani na takura da yawa” ya fad’a yana murza hannunta dake cikin nashi.

“Ai Baffa na lura baka Sona ko dan ni ba yar uwarka bace shiyasa kake nuna babanci muraran atsakanin mu”

“Dan Allah ki daina wannan batun Amina ta wallahi nima wani lokacin karkiga yadda abin yake damuna kawai dai tashin hankali ne bana so yasa kikaga ina biye mata”

Amma Baffa shekara ashirin sau d’aya ka tab’a bani kujeran nan ban tab’a cewa dan me ba yanzun ma nagane abin ba na K’are nane dan haka wallahi akan wannan komai zai iya faruwa”

“Dole na baki Amina tunda baki tab’a yi min haka ba sai yau dan haka komai zai faru kece da wannan kujeru na bana” nan dai yaci gaba da tausarta har yasamu ta d’an sakko sukaci abincin tare.

Kai tsaye suna fitowa d’akinta ta dosa dan yau tana buk’atar zuwa gidan su Maryam tana shiga suma suna shigowa yi tayi kamar bata gansuba sai da ya k’araso kusa da ita ya d’an dafa kafad’anta ta juyo ta harareshi.

Murmushi ya d’an saki ya sumbaci goshin ta bai ce komai ya juya ya fice daga d’akin ta raka shi da ido kafin ta juya tacigaba da shirinta.

Taku ce

MAMAN ISLAM

بسم الله الرحمن الر حيم
______________________

FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION

FCWA

{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________
???? BA JININA BACE????

2021

                NA

HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI

MAMAN ISLAM

Page 34

Cikin atamfa riga da sket kamar ajikinta aka dinka rigar tsabar yadda tayi mata d’as a jikinta, bata wani yi kwalliya mai yawa ba duk kuwa da yadda take da son kwalliyar, mayafin da ya dace da kayan ta dauka ta saka ta saka takalmi mai mugun tsini Allah yayi mata son takalma masu tsini ta fito d’as abinta.

Dukansu juyowa sukayi suka kafeta da ido ba k’aramin kyau tayi ba,kasa daurewa MD yayi sai da ya taso ya d’an matso kusa da ita yace,

“Bakiyi kyau ba” dan hararan sa tayi tace ” ai daman badan kai nayi kwalliya na ba bare ka kushe” murmushi yayi tare da mata gwalo domin yasan taji haushi ai kuwa ta k’ufula ta wani had’e rai, ta juya ta wuce d’akin Ammey karab sai a idon mama da ta fito zata fita jitai wani irin fitinannen tashin hankali yakawo mata farmaki da k’arfi tace “ke gidan uwar wa zakije ne” ta fad’a tana kafe Maryam da wani irin kallo.

Ba Maryam ba hatta MD da Nassar sai da suka zabura suka zuba mata ido, ita ko Maryam babu wani shakka ko tsoro tace “haba Mama wallahi har kin bani tsoro irin wannan ihun haka kamar aradu?”

Wani irin tuk’uk’i ne ya tokare haj. Sailuba ta kafe Maryam da wani shegen kallo zuciyar ta yana suya yaushe Maryam ta sami damar fad’a mata magana haka lallai in batayi wasa ba wata rana sai Maryam ta zageta anata haukan tunanin kenan.

Amma azahir cewa tayi “ni nake ihun bab? wai ma tukun me zakiyo ad’akin matar nan bana hanaki mu a’mala dasuba?”

“Hummm mama kenan ai duk randa babu ke dole itace uwata, ko baki tab’a tunanin hakan bane? kuma kadafa ki manta mama ba a raba hanta da jini mun riga mun had’u babu yadda zakiyi tunda ta haifa kin haifa dole ne itama ta sarara agidanna dan Allah mama ki daina irin wannan abun bashi da amfani ko kad’an haba”

Fashewa kawai haj. Sailuba tayi da kuka saboda tsabar tashin hankali da bak’in ciki kasa yi mata magana tayi har ta shige d’akin Ammey tana kallon ta.

MD kuwa wani irin annushuwane ya kamashi sanda Maryam ke fad’awa haj. Sailuba magana wani arnen murmushi kawai yake saki, yana ganin Maryam ta shige d’akin Ammey ya k’arasa kusa da haj. Sailuba yace “hajajju makkatu me kike tunanin zai faru duk ranar da wannan yarinyar tagane cewa ke ba uwarta bace uwar rik’o ce?
Ya zakiji lokacin da tasan cewa mahaifiyar ta kike sawa tanawa cin mutunci da wulak’anci
Me zai faru idan tasan cewa ba dan Allah kike rok’on taba kina rik’on tane saboda wani banzan dalili naki mara amfani?
Hhhhhhhhhhhh kad’an kika gani Sailuba domin Allah baya bacci”

Babu kunya haj. Sailuba ta kuma fashewa da kuka tana kallon MD kafin tace “hummmm Muhammad kenan na maka alk’awarin bazan bar hakan yafaruba sannan kuma ina Mai farin cikin sanar dakai cewa komai ya kusa zuwa k’arshe rayuwar Maryam zaiyi wulakantar da babu wani rayuwa da zata kai tata lalacewa zata bi maza zata yi shaye shaye zata yi sata zata zama abin kwatance da misali na miyagu da munanan halayya”

Sosai gabansa ya fad’i da jin furucin ta domin yasan zata aikata fiye da hakama jiyai hankalinsa yai masifar tashi ya dubeta da tsantsar b’acin rai yace “Allah ya fiki yafi waninki Sailuba kuma duk abinda kike tak’ama dashi insha Allah hakan ki bazai cimma ruwaba”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button