BABU SO HAUSA NOVEL

BAJININA BACE COMPLETE HAUSA NOVEL

Itama had’e ran tayi tace ni wallahi k’anina ba annoba bane haka kawai arik’a batamin sunan d’an uwa ubanmu fa d’aya sannan bani da wani k’ani bayan shi ni har ga Allah daga yau na daina hanayarar shi dan bazan masa abinda bros yake mana ba”

Murmushin dole mama tayi tace “haba shalele ba fa haka nake nufiba kawai dai ina gudar miki raini ne amma tunda kina son mu amalantar su ai bazan tab’a hanaki kome kike soba shalelena”

Ita kam maryam kama hannun d’an uwa ta tayi suka shige tana fad’in ina zuwa ne haka da yamma mama?”
“Gidan haj. Fauziyya zani zan amso wasu sak’o” tab’e baki maryam tayi tace “wato duk randa Baffa zai dawo sai anje amsar wannan sak’on da baya k’arewa tun ina yarinya nake ganin wannan sak’on daya k’i ci yak’i cinyewa” ta fad’a suna shigewa d’akinta da Nassar yayin da mama ta fice cikin sanyi jiki.

Suna shiga d’akin Nassar yace “wow Adda dama haka d’akin ki ya had’u gaskiya yafi nawa kyau sosai” yafad’a yana sufa agadonta, murmushi tayi tace “to ai kaine baka tab’a ahigowa d’akin nawaba” aikece Adda kullum cikin hantara ta kike kuma ni ina sonki tunda Ammey tace duk duniya bani da kamar ki dan ke kad’aice ‘yar uwata JININA” jikinta ne yai sanyi ta k’arasa bakin gadon ta jashi jikinta ta rungume tace “kayi hak’uri kaji d’an uwa na nima daga yau na daina biyewa mama ina cin zalin tilon k’anina a duniya kaji ko”

“To Adda dan Allah Ammey nama ki daina zaginta kinga wallahi tana sonki sosai ko sallah nayi saita ce nayi miki addu a itama tanayi miki” yanzu kam jikin maryam yagama sanyi tajashi jikinta ta rungume tace “na daina insha Allahu k’anina kaji ko?”

“To Adda naji yanzu dai bani sweet d’in dan bazaki min wayoba sauri nake zanje muci gaba da ball d’inmu da su boy” murmushi ta saki ta d’ebo sweet d’in mai d’an dama ta bashi domin itama gwana ce wajen shan kayan zak’i

6:15 pm

Dai dai lokacin motar bros ta shigo gidan ya dawo daga airport d’aukar Baffa Nassar daya dawo yanzun daga sallah magrib yasan cewa andawo kenan daga d’aukar mahaifin nasu ne ai kuwa wani ihun murna ya saki ya taho da mugun gudu.

Yayin da MD yai saurin fitowa ya bud’e masa k’ofar nan naga wani farin dattijo kal kal ya fito daga motar fuskarsa k’awace da kyakyawan murmushin daya k’arawa fuskarsa kyau, farine sosai d’an siriri kyakyawan bafulatani nasha mamakin ganinsa na kuma fara hasaso haj. Sailuba dan ita bak’ace irin k’irin d’innnan koda wasa maryam batayo kamar Sailuba uwar taba saima kamar da sukeyi da haj. Amina matuk’a kamar itace ta haife ta.

Da sauri Nassar ya rungume Baffa yana murnan ganin sa wanda ihunsa ne yasa maryam fitowa a miliyan har tana bangaje MD ta afka jikin Baffa tana “oyoyo Baffana gaskiya Baffa munyi kewar ka da yawa ko Nassar?” Ta k’are maganar da tambayar sa, yayin da Baffa da MD suka bita da kallon mamaki dan sunfi kowa sanin cewa kwata kwata Maryam da Nassa basa zama inuwa guda, basu k’ara mamaki ba saida sukaji Nassar yace “eh Adda kuma gaskiya inya tashi komawa saidai yaje damu tunda ku kunyi candy ni kuma zan tafi secondry kinga sai musha hutunmu kusa da Baffan mu ko?”

Hannu ta bashi suka tafa sannan sukaja Baffan nasu zuwa cikin gidan yayin da MD wanda ya daskare da mamakin had’in kan daya gani tsakanin maryam da Nassar ya bi bayanau, aransa yana ayyana ina ma zasu d’ore a haka da sai yafi kowa jin dad’i sannan wahalarsa na son ganin had’in kan su zai k’are lallai zaici gaba dayi musu addu a kamar yadda ammeyn nasu ta buk’ata ya tabbata wata rana maryam zata bar abinda takeyi wanda kowa yasan cewa zugar uwar tane yake tasiri aranta.

K’yale Baffansu sukayi ya shiga fat d’insa yai wanka yai sallar magrib yana idarwa ana shiga isha dan haka ya fito suka wuce masallaci da MD da Nassar,

Yayin da maryam da mama suka gabatar da tasu hakama Ammey tayi tata anata d’akin sannan suka fito dirning domin cin abincin dare basu tab’a zaman cin abinci mai dad’in wannan ba tunda suka zauna ba babu fad’a da hayaniya tsakanin maryam da Nassar shi kanshi MD satar kallon ta yake tare da mamakin abinda ya sauyata cikin sauk’i haka.

Aban garen iyayen kuwa Ammey hakan ba k’aramin dad’i yayimata ba domin bata da burin daya wuce ganin had’in kan ‘ya’yan nasu

Yayin da mama kuwa hakan yai masifar k’untata mata tayi wani kicin kicin da rai tana hararan maryam wacce ma batasan tanayiba domin sha aninsu kawai suke sha ita da d’an uwanata, yayin da zuciyar ta yake fad’a mata cewa lallai idan bata d’auki matamin gaggawa ba to shirinta na shekaru zai lalace dake ita ba mutum ce mai iya b’iye damuwa ba hakan yasa ta tashi a fusace tabar wajen tana dad’a d’aure fuska duk suka bita da kallo yayin da Baffa yatam bayi maryam ko anwa maman ta wani abunne”

Kagad’a ta motsa kafin tace “itafa mama bak’in cikinta dan taga mun shirya da Nassar ne mun daina fad’a ita kuma bataso shine kawai” dake maryam ‘yar gatsal gatsal ce kuma duk inda gaskiya take fad’a take kai tsaye batare da shakka ko tsoron wani abuba.

“Ungo nan” cewar Ammey tana ma maryam irin zagin nan nabaza yatsu tace “yanzun dan gidan ku mamar takice ‘yar bak’in ciki?”

“Eh mana Ammey muguwar ‘yar bak’in ciki ma kuwa itafa koda wasa bataso taga na rab’i k’anina tafiso na zauna bani da kowa bani da abokin ahawara ni kuma daga yanzun na daina lamunta randa babu wani acikin ku kenan bazanyi huld’a da d’an uwana ba ina bazai yiyuba”

Baffa yace “ga wannan indai kina neman abokin shawara kika same shi ai kin gama dan haka ki daukeshi d’an uwa amini zai baki ki d’aukeshi yaya aboki kuma aminin ki zakiji dad’in hakan wata rana”

“Tab ina wallahi bazan iya ba wannan mai kama da maka ikan d’aukar ran kullum fuska babu annuri ni wallahi ina masifar tausayawa matar sa domin ta shiga uku da bak’in rai wallahi” duka Ammey ta kawo mata ta goce yayin da Baffa tace

“Kika san inda rana zata fad’i?”

“Nassar taso muje muci gaba da buga was an nan idan har kabari nayi winning d’inka saina zazzage bankinka ka yarda?”
Tak’are da tambayarsa

“Eh na yarda amma fa idan nina cinyeki zaki sa Baffa nima ya sai min computer irin naki” ita ma tace ta yarda suka bar wajen tana hararan MD k’asa k’asa, wani b’oyayyen murmushi MD ya saki Binta da kallo k’asa k’asa ta yadda zai wuya ka gane ita yake kallo.

Baffa ya d’an dube shi da damuwa yace ‘Muhammad kafasan alak’ar dake tsakanin ka da ita dan haka ina so ka kawo k’arahen wannan bak’ar kiyayyar dan Allah na rok’eka” Baffa ya k’arasa yana had’e hannayen sa alamun rok’o iaka ya fesar batare dayace komai ba ya ture kujerar yabar wajen ba tare da yace komai ba, duk suka bishi da kallo, yayin da Ammey taji wani irin abu yana taso mata saiga idanun ta sun cika da kwallah Baffa ya dafe hannunta yana girgiza mata kai.

Sunan Baffa yasamo asaline tunda ga sunan kakan sa da yaci iyayen sa suka mak’ala masa Baffa shike nan Baffa ya bishi har zuwa yanzun da yaransa ma duk da hakan suke kiransa Baffa d’an gatane sosai awaken iyayen sa kasancewar sa shi d’aya rak hakan yasa yasami gado mai d’umbin yawa daga mahaifinsa bayan ya rasu gata da kulawa babu irin wanda bai samu daga iyayen saba yayi karatu tundaga matakin pir har zuwa dgreen sa na biyu duk afannin likitanci duk da kasan cewar su ‘yan k’auye hakan baisa Inna da baba hana d’ansu karatun boko dana zamaniba yanzun haka yana da ilimi mai train yawa daga na zamanin har na wajibin.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button