BABU SO HAUSA NOVEL

BAJININA BACE COMPLETE HAUSA NOVEL

Ya fad’a yana d’age mata gira tareda murmushin da bata gane ko na meye ba, hararan sa tayi ta maida kanta can gefe tana shashshek’a, kafin ya k’ara magana aka kira wayarsa da sauri ya d’aga harda d’an russuna wa kamar yana gabansa, bataji abinda akace masa tadai ga ya amsa da to ya fice da sauri.

Lokacin da zai shiga d’akin dan amsa kiran Baffa sannan kuma Ammey ta fito daga d’akin cikin tsantsar tashin hankali da b’acin rai taci alwashin koda hakan yana nufin rabuwarsu sai an maido mata yar ta wallahi, ko kulawa da MD batayi ba ta fice ta ta wuce d’akin ta ta zari mayafinta rabonta da kwatanta yaji tun akan bada Maryam sai gaahi yauma ta k’ara kwatawa.

Yanayin da MD yasami Baffa na b’acin rai yasa MD ya k’ara nutsuwa ya k’arasa kusa dashi ya zauna kansa a k’asa Saida ya nutsu Sosai ya gaida Baffa wanda tsabar damuwa yasa ya kasa amsawa saboda tsabar tashin hankalin data jefashi.

“Muhammadu zan tambayeka ka dubi girman Allah ka fad’amin tsakani da Allah nake so kafad’a min iya abinda ka sani’ karka min k’arya, kar ka min k’arya, karka min k’arya, Muhammadu kada ka duba halin da kuke ciki kai da Sailuba asalin gaskiyar nake buk’ata”

Shiru MD yayi na d’an wani lokaci yana son tuna komai ko abu guda baya son ya manta (????????) MD fa ka fad’i gaskiya banda heri????????

Kallonsa Baffa yake yana jiran amsa, dan haka ya kwashe iya abinda ya sani komai bai rage ba kafin ya k’arasa jikin Baffa yayi wani irin sanyi wata irin nadama ta saukar masa take ya hau zufa jijiyar kansa tayi wani irin tashi, waima me ya hau kanshi da har ya manta halin Sailuba ya d’auki tarbiyyan gudan JININSA ya bata matar da ita kanta tarbiyyar take buk’ata take ya kama hawaye abinda ya firgita MD kenan ya rik’a rarrashin sa tareda kwantar masa da hankali

Wasa ya fara

MAMAN islam ce

بسم الله الرحمن الر حيم
______________________

FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION

FCWA

{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________
???? BA JININA BACE????

2021

              NA

HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI

MAMAN ISLAM

Page 40

Bai saurare shi ba ya tashi a fusace ya fita, yana fita MD ya mik’e ya buga uban tsalle yana rawa har da d’ebo shoki a aransa yake fad’in yau wata zata kwashi kashin ta a hannunta yadda Baffa ya fusata dinnan.

Wani abun ta kaici Baffa a fitinensa ya shga d’akin Sailuba ya balbaleta da ruwan bala i amma tana d’agowa suka had’a ido sai ya nemi tashin hankalin ya rasa saima rarrashin ta da ya somayi ita kuma tayi wani kicin kicin da rai.

Sanda haj. Amina ta isa gidansu malam Babba yana k’ofar gida da daliban sa tsabar idonta ya rufe bata gansuba kanta tsaye d’akin Nanne ta wuce cikin wani irin yanayi mai wuyar fassara, ita kanta Nanne ganin ta haka sai da gabanta ya fad’i da k’yar ta rarrasheta ta daina kukan da takeyi.

Ganin halin da yarsa take ciki yasaka ya sallami mutanen nasa ya taso kai tsaye d’akinsa ya wuce yasa aka kira masa duka matan nasa harda Amina wacce tai wani wujuga wujiga tsabar tashin hankalin data tsinci kanta a ciki.

Sai da malam ya fara yimata fad’an fitowa da tayi batare da sanin mijinta ba dan duk wanda yaga yanayin ta yasan ba fitowar lafiya tayi ba sannan ya tambaye ta abinda yake damunta.

Cikin zubar da hawaye ta kwashe tun daga ranan data fara jan Maryam har zuwa yau ta fad’a musu komai, ba matan ba hatta shi kanshi malam Babba saida hankalin sa ya tashi danjin masifar da ake son d’ora masa jikar tasa akai sosai ransa ya b’aci ya rik’a maimata innalillahi wainnailahi raji un sosai yaiwa haj. Aminatu nasiha sannan yace tacigaba da jan yarta a jikinta ta kuma rik’a nusar da ita cikin hikima ta rika sata a hanyar data dace kada tace zata yi mata hayaniya shi yaro da dabara ake tarbiyyan sa ba da hayaniya ba.

Sunan zaune sai ga Baffan yazo hankali tashe tun bayan da ya fito daga d’akin Sailuba ya fara tuhumar kansa dalilin da yasa yakasa yimata bore kamar yadda ya fita da niyyar yi mata.

Bayan sun gaisa da malam ne yake bashi hak’uri kuma yake rok’on abawa Amina hak’uri sannan yace koda yaje da niyyar daukar mataki akanta sai tayi masa kwarjini ya kasa tab’uka komai.

Malam yace” babu komai kaci gaba da addu a kuma kadaina sake wajen yin azkar insha Allah komai zaizo maka da sauk’i yanzu dai maganar gaskiya Baffa ya zama dole kasa ido akan tarbiyyan yarinyar nan”

Komai ya kusa karewa ma malam dan na tsaida auren Maryam da MUHAMMAD k’arahen watan nan da muke ciki insha Allah” ba malam Babba ba hatta Ammey ba k’aramin sanyi taji aranta ba sai taji duk abinda yake damunta ya kau, sosai malam yayi musu nasiha, kafin su baro gidan.

Acan gida kuwa suna fita haj. Sailuba ta fito nan ta sami MD da Nassar a falon ta saki wani wawan tsaki ta k’arasa kusa da su tace ” su agola ansami wuri kana tunanin d’an k’aramin makircin ka zaisa kay nasara ne? ni kumurcin kan dutse ne ban fito ba saida na shirya”

“Haba Sailuba karfa ki manta rana dubu na b’arawo rana d’aya na mai kaya ne yanzun dai ki mai da hankali kici lokacin ki amma ki sani komai lokaci ne karshen ki ya kusa fajirar banza”

“Kai dan ubanka ko Hasan ya isa ya zag…….. ” Ke tsohuwar banza gyara kalaman ki kada ki kara zagin bawan Allah yana kwance a raminsa yana hutawa kinsan wanda yasami shaidar mutane ya dace dan haka ya fi k’arfin ki shi d’in bawan Allah ne ba masoyin duniya bane dan haka na k’ara jin kin zage shi wallahi saina gurji bakin ki”

Ganin yadda ya rikice mata idanunsa sunyi wani irin juyewa tsabar b’acin rai yasa tai gum da bakinta sai d’an uban harara da take aika masa shima dataga ya d’ago zatayi saurin k’asa da kanta.

Sai da ya gama masife ta tare da zubar da ruwan rashin mutuncin son ransa kafin ya buga wani d’an uban tsaki tare da sakar mata hararan da yasa ‘yan hanjin ta kad’awa babu shiri ta shige d’akin ta tana tsine masa a ranta.

Su Ammey suna dawowa gida tasa maryam ta hau shiri dan tasawa ranta cewa ‘yarta tabar hannun wannan azzalumar matar, hakan yasa ko Baffa baisan da Maryam akai tafiyar ba sai da yagama shirinsa yasauko yana tambayar haj. Sailuba maryam ta gama shiri shine take sanar masa tare da Ammey suka tafi ransa ba k’aramin b’aci yayi ba ya rufe ta da fad’a domin yasan dan kar ya kaita w ajen mahaifiyar sa yasa ta bari aka tafi da ita yasan Sailuba yasan waye ita, yasan abinda zata iya aikatawa da wanda baza tayi ba, ya rasa mai Inna tayi mata da zafi haka da ta daina zuwa inda take kuma ta hana maryam ta kusance ta matar da ta rik’e ta ta kula da ita bata bari tayi kukan maraici ba yau itace abar wulakantawa awajen ta kwafa yayi ya fice cikin tsantsar b’acin rai da bak’in cikin yadda yake kasa d’aukar mataki akan abinda take masa ko yaso hakan sai tayi masa wani irin kwarjini yaji tausayin ta ya baibaye shi.

Maryam kuwa yau cikin wani irin farin ciki ta tsinci kanta bakin ta yak’i rufuwa tsabar jin dad’i, baza tace ga lokacin da sukayi doguwar tafiya irin wannan ba.

D’an d’ago kanta tayi daga kafad’ar Ammey ta dubeta “Ammey wai me yasa Mama bata son naje wajen Inna kinga fa bansan garin ba gashi Baffa yana yawan zuwa da Nassar amma ni sai ta hana me yasa bata zuwa kuma bata so naje?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button