BAJININA BACE COMPLETE HAUSA NOVEL

Acan gida kuwa MD ji yai hankalinsa yayi wajen Maryam kamar ya bita sai dai yana binta Ammey zata gane saboda Maryam ne hakan kawai yasa ya yanke shawaran yakai ma m Bash ziyara.
Kar ku manta Baffa bai sanar da MD maganar aurensa da Maryam ba hakanan haj. Sailuba bata sani ba, bawai kuma saboda wani abu yak’i sanar da ita ba sai dan b’ata masa ran da tayi na barin Ammey ta tafi da maryam d’in alhalin yana son zuwa da ita wajen Inna wanda dama zai jene dan sanar da ita maganar auren Maryam da MD d’in ne.
Ku muje dai masoyana
Ina alfahari daku duk inda kuke a fad’in duniya
MAMAN ISLAM taku ce mai matuk’ar k’aunar ku
بسم الله الرحمن الر حيم
______________________
☀ FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION ☀
FCWA
{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________
???? BA JININA BACE????
2021
NA
HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI
MAMAN ISLAM
Page 42
Bayan ya gama shirin sa ya fito cikin k’ananan kayan da suka matuk’ar amsar sa,ya fito yana baza k’amshin sa mai kwantar da zuciya.
Yana sako kai haj. Sailuba na fitowa daga lambum kusa da Pat dinsa cikin wani irin sauri tana wage wage gudun kar wani ya ganta da ganinta ba abin arzik’i ta shuka a wajen ba, wani mugun kallo ya bita dashi cikin tsana sannan ya yaja wani uban tsaki ya shiga lambun dan haka nan yaji yana son ganin meta aikata awajen.
Da kallo ya rika karewa wajen kallo har idanunsa suka sauka kan wajen da aka hak’e da alama wani abun aka bunne awajen, gabansa ne yai mugun fad’uwa ya taka a hankali cikin nutsuwar sa ya karasa yana nazartar wajen kafin yayi Bismillah ya durk’usa dan tsabar saurin da take hatta abin hakar bata d’auke ba ta manta da shi a wajen.
Sai da yai addu a sosai kafin ya fara hak’a ramin da tayi, yayi mamakin yadda ta iya hak’a rami mai uban zurfi haka, yajima yana hak’a dan har ya fara tunanin babu abin da ta binne kafin yaji hannunsa ya caki wani abu mai mugun tsini da sauri ya janye hannun saiga jini yana bin hannun nasa wanda jini ya fara bi ga wani mugun radadi da ya zuyarci har kwakwalwar sa, mamakin hakan yasa kashi saurin lek’a ramin haba da sauri ya janye kansa yana sauke wani irin wahalallen numfashi sabo da wani fitinannen wari daya daki hancin sa, sai dai abinda ya gani yasa shi saurin komawa tare da dauke numfashi dan tabbas wannan masifar zai iya masa illah.
Mikewa yayi ya koma d’akin sa hankali a tashe ya d’auko hanglob jikinsa har wani rawa rawa yake sosai yazo ya hau fito da abin bakinsa d’auke da addu’a, yanzu kam rawa jikinsa ya kama sosai saboda tsabar mamaki.
Kan mujiya ne jikinsa duk wasu irin manyan allurai sai kuma wata ‘yar k’aramar benu da aka sa wata katuwar allura aka caki daidai zuciyar ta sai numfashi take fitar wa da k’yar ga wasu irin curin layu masu yawa suma a saman wata tsuntsu da baisan ko ta mecece ba itama daga gani ajikace take tama kusa mutuwa.
Idanunsa da sukayi wani fitinannen ja ya runtse da mugun k’arfi ya zauna dab’as a wajen cikin ciyayin gun ya dafe kansa da yake mugun sara masa da k’arfi yace “innalillahi wainnailahi raji’un Maryam ko Ammey zata kashe?”
Dan shi abinda ransa ya bashi kenan na ganin wannan masifar alluran dake jikin tsuntsayen da suke da rai ya fara zarewa kafin ya cire na jikin mujiyar gaban sa na wani irin mugun fad’uwa hankalin sa a masifar tashe bai ma yarda da kona kayan kai tsaye ba sai da yayi musu fitsari kafin yasa fetur ya Kone.
Tunda taga Ammey ta fara shiri tace itafa sai gobe zata dawo dan gajiyan hanya bai gama sakinta ba sosai Abdul jabbar da yake ta binta da kallo yasaki murmushi yace “kawai ki k’yale ta Ammey ma kawota nida Abdul Malik”
“Rufamin asiri Abdul jabbar Baffanku baisan nazo da itaba, kabari tunda bikin ta za ayi tazo tayi muku kwana biyu” sai da gabansa ya fad’i da yaji wai bikin ta za ayi dan har ga Allah tayi masa sosai.
“To ‘yata sai kinzo gyaran jikin ni da kaina zanwa ‘yata gyara na musamman, dake sana ‘ar tane gyaran amare da haka sukayi sallama.
Tana zaune cikin jin dad’in cikar burinta haj. Zakiyya ta kira tana d’agowa tace “ba nutsuwa ba kwanciyar hankali ita ba mahaukaciya ba kuma ba mai hankali ba sannan ita ba rayayya ba sannan kuma ba matacciya ba” hhhhhhhhh suka saki wata muguwar dariya haj. Zakiyya tace an aikata ke nan?”
Me zan jira k’awata kinajifa boka yace uban yatsaida aurenta da wannan tsinannen yaron dana fi tsana fiye da komai a rayuwata wallahi bazan bar wannan banzan auren ya faru ba na rantse kuma” ta k’arasa maganar tana huci
Har lokacin MD yana d’akin sa cikin tsantsar damuwa da nazarin son gane shin cikin Ammey ko Maryam wa akayi wannan bak’in asirin dayai masifar d’aga masa hankali?
Ya sandai wannan tarkacen bala in ba abin arzik’i aka shuka a cikinsu ba.
Kamar wanda aka tsikara ya mik’e zumbur domin kaiwa haj. Sailuba fatanyar ta da ta manta.
Yana fitowa ana budewa motar su Ammey gidan, dan haka ya dakata har driver ya shigo ya faka motar duk suka fito da gudu Nassar ya k’araso ya rungume MD wanda yai kasak’e yana kallon su, yana mai murnan ganin yayan nasa.
Da wani irin kallon mamaki Ammey tabi kayan hannun MD yayin da Maryam ta wuce ciki tana mai dok’in ganin mamanta.
“MUHAMMAD wannanfa me kayi dasu naganka futu futu haka?’
” Ammey” sai kuma yai shiriu zuciyar sa na wani irin zafi yay saurin dafe kansa kafin yace “wa take son kashewa Ammey ke ko ZUCIYA TA?
Muje dai
DAGA MAMAN ISLAM
???? BA JININA BACE????
2021
NA
HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI
MAMAN ISLAM
Page 43
Kallon Ammey yake dafe da kirjin sa wanda zuciyar sa take barazanar fitowa, itama kallonsa take da son k’arin bayani.
Dak’yar ya bud’a baki yace “Ammey wani aikin nayi mai wahalarwa Ammey me waccen matar take nufin yi ne akan ni da matata Ammey na rantse da Allah wani abu yasamu matata ni da kaina zan d’auke kanta da wu’ka da wadannan hannayen nawa.
Ya fad’a yana d’aga hannun nasa wanda suke wata irin rawa sama.
Da wani irin rawa Ammey ta danki hannun MD jikinta na kakkarwa tace “wayyo Muhammad rik’e ni zan fad’i” tayi luuuuuu da wani azababban zafin nama MD ya rik’o ta cikin wani irin rikitaccen yanayi yace “Ammey lafiya kuwa”?
“Kaini d’akina Muhammad banida lafiya” da sauri ya d’auke ta akafad’unsa yayin da jikinsa yake wani irin rawa jikinsa kuwa ta ko ina gumine yay masa wanka.
Da sauri ta janye wayar daga kunnenta tana fad’in “zan sake kiranki anjima k’awata” nakamakon juyowa da tayi sukayi ido biyu da Maryam da tajima abakin k’ofar tanajin irin mugun abun da maman tata take k’ullawa tambayar da Maryam take wa kanta shine
“Shin waye za’a haukata?
Waza a tozarta ya wulak’anta?
Waye zai zama abin k’yamar al’umma?
Me yaye mata take son ya zamo kamar mujiya?
Akan me take so yayi warin jab’a?
Shin dama mama tana yawon bin malamai ko yanzun ta fara?
Ta yarda da daukar wannan babban zunubin ko kuwa?
Dawa take wannan Killin?”
Inda haka ne mama baki da imani baki da tausayi baki damutunci matsayin ki na musulma ki rink’a had’a mugun k’ulli haka?
Duk tayiwa zuciyar ta wadannan tambayoyin, yayin da zuciyar ta yake wani irin bugawa sai taji hankalin ta yai masifar tashi wani irin tsoron maman tata ya mugun kamata da gudu ta juya ta fice daga d’akin cikin tashin hankali gaba d’aya idanunta ya rufe.