BABU SO HAUSA NOVEL

BAJININA BACE COMPLETE HAUSA NOVEL

Idanunta ya rufe,
Zuciyar ta ya toshe
Tunanin ta ya b’ace
Imanin ta ya barta
Bata da wani buri ko fata illah tarwatsa rayuwar yarinyar da babu abinda tayi mata wanda ya wuce yi mata biyayya da gwada mata k’auna irin na uwa mahaifiya da ‘ya mai mutukar biyayya agareta.
Hakkan ne yasa Baffa yana shigowa ta fice dan boka yace kar ta bari su had’u dama dakon dawowar sa take wannan kenan.

Bayan Maryam ta idar da sallar tana shirin komawa b’angaren Ammey kiran name sake d’in ta ya shigo wayar ta ta d’aga tana fad’in ‘yar halak wallahi jikin Ammey ne ya hanani kiranki”

“Eh kyace haka mana saboda rainin hankalin da kika saba, yanzu sahiba ace jibi jubi daurin auren ki amma sai yau muke sani kin kyauta ai”

Dakatar da ita Maryam tayi ta hanyar cewa ” dake yar tsana ce ni shiyasa aurena zai kasance jibi har na kasa sani, ko shirin film ko kuma a littafi wanda suke shirya abu nan take”
“Idan kina musu ki bud’e data ki duba status dina mana ko muna da wata MARYAM BAFFA ABUBAKAR ne bayan ke?”
Ai bata tsaya jin k’arshen labarin ba ta katse kiran tana katsewa kiran Halima yana shigowa ta daga asanyaye saboda bazata iya katse kiran Halima ba amma bataso Kiran ba sai ta fara duba sak’on Maryam.

“Ba zaiyiyu mu zaga duka k’awayen mu yau ba dan haka waso duk ta whatsoapp muka tura musu katin gayyatar, idan Kuma kina da wani wanda zaki bawa idan kun dawo daga unguwar saina kawo miki sauran”

Da mamaki Maryam tace “ke nifa bangane inda wannan dogon sharhin naki ya nufa ba katin gayyatar me?”
Yadda tayi maganar ya tabbatar wa da Halima cewa Maryam bata san da maganar aurenta jibi ba dan haka tace mata “kun dawo ne?”
“Eh “kawai tace mata tana dafe kanta da ya soma k’ullewa da maganganun Halima da maryam

“Bari nazo yanzu” ta fad’a tare da katse kiran.
Ba a rufa cikakken minti uku ba Halima ta shigo d’akin ta karasa kusa da Maryam ta dafata tunda tayi sallama bata jitaba ta fad’a duniyar tunani.

Ba tare da ta ce mata komaiba ta mik’a mata iv mai d’auke da sunanta baro baro da sunan MD tareda tabbatar da d’aurin auren su ranan 2/3/2021
Sosai mamakin ganin katin ya kamata yaushe nema har tace tana son MD da za ayanke mata d’anyen hukunci haka?

Dafatan da Halima tayi ne ya maidota hankalin ta a hakanli tace “nayi matuk’ar farin cikin kasancewar wannan abun kuma nasan cewa kema baki san da maganar ba Maryam nasan wannan shirin Baffa ne dan Allah karki bujere”
“To” shine kawai abinda Maryam ta iya fad’a tana tunanin yadda MD zai d’auki abin yadda yake nacin soyayyar ta d’in nan bai samu gamshashshen amsa ba gashi yanzun ya sameta a arha, arha mana tunda tasan cewa wannan ba shirin Baffa bane na Inna ne dan Baffa duk abinda zaiyi sai yai shawara da ita da MD daga haka sukayi sallama da Halima bayan tayi mata nasiha ta bata ahawarwari sannan tace yanzun maman Niger zatazo tunda abin yazo a kurace ta d’an yi mata gyara sama sama Umma ne tasa a kirata.

Tana fita MD yana shigowa d’akin cikin wani irin sauri ya k’araso kusa da ita ya tsaya yace “my happiness kinga abinda nagani kuwa?”
“Eh na gani” ta fad’a a sanyaye haka nan maganar take sa mata wani irin fitinannen bugun zuciya “me kika ce akai to?”
A dan sanyaye ta kalleshi kafin lumshe idanunta ta bud’e akanshi zuciyar ta na wani irin fitinannen bugu har tana dafewa tace “me kake so nace to?
So kake naje nacewa Baffana ban amince da zab’in saba?”

Sam bai kula da yanayin ta ba ya duka ya d’an tsotsi tattausan lab’b’an duk kuwa da irin yadda take nuna masa bata son hakan ya dafa kanta yace “miki alk’awarin insha Allahu bazaki tab’a nadamar kasancewa na mijinki ba ya kuma manna mata wani kiss d’in a goshinta kafin ya fita da d’an gudun sa dan kar tayi masa magana, gane hakanne yasa ta saki murmushin da bata shiryawa zuwansa ba.

Bayan Baffa ya dawo daga massalaci ya shigo d’akin Ammey yaji dad’in ganinta akan sallaya itama tayi sallar tana jingine a jikin gado tana jan carbi.

K’arasawa yayi kusa da ita ya zauna dab’as yana dubanta kafin yakai hannun saman fuskar ta ya d’an shafo “ya jikin babyta?”
Ya fad’a da salon tsokana wanda rabon da hakan ya kasance an d’an jima sai abin ya bata dariya sosai, sai ta d’an murmusa tace “da sauk’i kafin takai hannunta saman nashi tace “Baffa”
“Na am” ya amsa mata cikin sanyin jiki

D’an Allah kada ka bari abinda yake faruwa da rayuwar Maryam yaci gaba da faruwa dan girman Allah, saboda kaga rayuwa ba tabbas idan yau mune gobe fa jibi fa haka wata rana bama nan an gina rayuwar ‘yata cikin wani irin gurbataccen yanayi wanda sam bai min dad’i ba Baffa, kasancewar Sailuba na ‘yar uwar ka bai kamata ace tayiwa ‘yarka irin wannan tarbiyyan ba, kasan mai yafi d’aga min hankali?”

“a a” ya fad’a yana kafe ta da wani irin kallo gabansa na mugun fad’uwa ya saboda yadda yaga ta koma kamar babu jini a jikinta, yayin da taci gaba da cewa “ce matafa tayi taje tayi duk abinda zatayi itadai karta sake ta d’auko mata ciki”
“Ita Sailuban?” Baffa ya tambaye ta a fusace nan ta kwashe duk irin abunuwan da maryam take fad’a mata idan sun keb’e ta fad’a masa tas.

Ran Baffa ba k’aramin b’aci yayi ba ya nufi part d’in Sailuba a fusace, sai dai abin ta kaicin yana shiga ya tarar bata nan a gogon hannun sa duba tara da rabi na dare, yaushe har nayi saken da Sailuba takeyin yadda taga dama a cikin gidannan?
Ni kuwa nace an maka dabaibayi ne malam Baffa shi yasa take yadda taga dama hhhhhhhh.

Tun yana saka ran dawowar ta har k’arfe daya ta buga wanda ya tabbatar masa cewa Sailuba bazata dawo daga yawon gantalin ta yau ba, ai kuwa ransa ya kai k’ololuwar b’aci yasha alwashin sai ya sab’ar mata fiye da kima.

Acan wajen boka kuwa irin yadda ya rika durza Sailuba ko Baffa bai tab’a yi mata irin wannan durzar ba iya bak’ar azaba awannan daren Sailuba tasha a hannun katon kafirin da babu Allah ko kad’an a zuciyar sa haka ya kwana abu d’aya da ita ga abin nasa mai mugun tsayin da ya wuce tunanin ta gashi mugun fitinanne ka masifar warin da yasa ta rik’a yunk’urin amai amma ta kasa yi bashi ya k’yale ta ba sai da garin Allah ya waye tangaram Kuma ya hanata yin sallar yace ita da salla sai in ta koma gida tayi, dake idanunta ya riga da ya rufe cikar burinta kawai take buk’ata ba wani ja ta amince hakanan ya wuni sa suk’ar ta kamar ya samu abinci.

Ganin k’arfe uku ya buga yasa Baffa komawa d’akin Ammey cikin tsantsar b’acin rai ga mamakinta saman dadduma ya tadda ta tana lazumi duk da kasancewar k’arfin hali kawai take hakan ba k’aramin dad’i yayi masa ba.

K’arasawa yayi kusa da ita ya zauna ya kamo hannunta yace “ki kwantar da hankalin ki Amina ta addu’ar ki ya amsu jibi daurin auren Maryam da MUHAMMADU inji Inna”

Wani irin kafe shi tayi da ido kafin ta fad’a jikinshi ta k’ank’ame tace “na gode na gode ba ka gama min komai naji duk wani fargabana ya kau Baffa Allah ya sakawa Inna da mafificiyar Aluannah.

Ta fad’a cikin fashewa da kuka yace “to meye kuma na kukan ‘yan mata na kunya ne ta kamata dan haka ta b’oye fuskar ta a k’irjinshi, ranan dai haka suka karasa wannan daren cikin farin ciki da nishad’i wata irin hira sukayi mai dad’i da tsayawa a rai Sosai Baffa ya samu sauk’in b’acin ran da Sailuba ta dasa masa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button