BABU SO HAUSA NOVEL

BAJININA BACE COMPLETE HAUSA NOVEL

Maman Islam ce
بسم الله الرحمن الر حيم
______________________

FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION

FCWA

{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________
????BA JININA BACE????
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI

MAMAN ISLAM

Page 5
Tun bayan raauwar mahaifin sa ya samu aiki acikin gari ya baro k’auyen su babu yadda baiyi Innar sa ta dawo kusa dashi ba mursisi tace ita tafijin dad’in zaman can tunda da nan tasaba saidai ta had’ashi aure da d’iyar k’anwarta SAILUBA wacce ta rika tun bayan rasuwa k’anwar tata wacce ta rasu awajen haihuwar ta ta biyu lokacin Baffa yana matakin secondary dake bording school ce hakan yasa sai lokacin daya dawo suke had’uwa da ita.

Allah ya jarabci Sailuba da matuk’ar son Baffa saidai bata nunaba kasancewar ansa ‘ya mace da kunya dan haka ta barwa ranta amma ta dage da addu ar neman zab’in Allah, itama tana danata ilimin daidai gwargwado domin ta kammala aji uku na wato k’aramar secondary sannan afannin addinin ma ta d’anyi nisa,

Koda wasa Baffa bai tab’a nunawa Sailuba cewa aurensu auren had’ine ba domin tun mahaifinsa sa na darai baya iya k’etare duk wani umarni da zasu bashi haka ma yanzu da ya kasance baya raye duk abinda mahaifiyar shi tasaka shi komai wahalar sa baya k’inyi mata

Dan haka yake shan albarka da addu o I kala kala daga mahaifiyar sa wanda yake ganin ci gaba arayuwar sa.

Tunda akayi auren su da Sailuba basu tab’a jin kansuba domin suna matuk’a zaman lafiya komai tare suke yi su kashe su binne tare yayin da Sailuba ta ganta a birni idanunta ya bud’e tafara k’awaye matan abokansa wanda daga baya takejin kanta ta wuce da ajinsu bazata iya alak’a dasu ba saboda d’aukakar da Allah yaiwa mijinta lokaci guda ta hanyar kasuwancin daya somo wannan kenan.

Matsalar farko da suka fara fuskanta shine rashin haihuwa lokacin da Inna taga an kwashe kimanin shekara biyar babu amo babu labari sai abin yafara damunta kullum bata da magana sai na son ganin ‘yan jikokinta, tun Baffa baya damuwa shima har abin yasoma damunsa, magani kuwa suyi na gida suyi na asbiti,

Wata rana Sailuba ta kaima babbar aminiyar ta ziyara wacce tun zuwanta garin bata da aminiya sama da ita bayan sun gaisa tasa ankawo mata kayan motsa baki mai aiki ta gabatar mata dashi ta d’an dubi aminiyar tata Zakiyya tace “ni kuwa ina DEEDAH” babbar ‘yar haj. Zakiyyan kenan murmushi tayi tace “humm Deeda rikici zakice min tana can d’akin ta tana faman kumbure kumburen banza wai sai nasa Abban ta yacanja mata mota, ni kuma banga abinda motar ta yayi ba shiyasa nayi banza da ita ta cika fitina yarinyar nan wallahi”

‘Yar dariya Sailuba tayi tace haba Zakiyya tilon ‘yar taki kikasayi mata wani abu gaskiya baki kyautaba tana ina ni tazo ta fad’amin duk kalar data ke so kiga aiki da cikawa” suka yi dariya yayin da haj. Zakiyya tace “kina shagwab’a yarinyar nan da yawa Sailuba ya kamatafa ace tasan cewa ba komai ne mutum yake so arayuwarsa yake samuba”

“Yauwa Sailuba ni kuwa ya batun maganin andace kuwa?”
“Wanne kenan cewar haj. Sailuba tana duban haj. Zakiyya na haihuwa mana” ta bata amsa cikin gaakiya da gaskiya wata ‘yar banzar dariya ta saki tace “wai ke anfad’a miki duk wahalar da su Inna suke amfani nake da maganin?”

Kallon rashin fahimta haj. Zakiyya tayi mata sannan tace “ban fahimce kiba k’awata kina so kicemin duk wahalar banza mukeyi bakya amfani da maganin?”

“To mai zai dameni dan ban haihuba kuma ni gaskiya koda zan haihun ma ban shirya yanzun ba saboda haka kuma daina wahalar da kanku da kud’ad’en ku wajen nema min magani domin ba na amfani daahi”

“Ke kuwa mai yakaiki aikata wannan d’anyen acikin k’awata kuma naga ko ba komai ai ‘ya’ya rahama ne bakisan wanda zaki moraba sai Allah”

“Nifa kin fara takuramin da wani wai haihuwa haihuwa ki k’yaleni mana dan Allah a a haka kawai nifa babu abinda na nema na rasa mijina bai tauyeni ba haka mahaifiyarsa nima uwata ce bata d’aukeni suruka ba dama can ni ‘yar k’anwar tane kuma rainonta dan haka banga abinda zaisani wahal da kaina dole sai na haihu ba”

“Bakya tunanin wata rana idan mijin naki ya gaji yace zai auro wacce zata Haifa masa yara kinsanfa babu wanda bayason ganin kwansa a duniya?”

“Ke dallah saurara taya kike tunanin zan bari hakan yafaru”? Baffa bashi da wata mata a duniya bayan SAILUBA kisawa ranki haka sannan kisa aranki cewa duk yadda yakai ga son yara dole ya hak’ura tunda mahad’in rayuwar sa bata buk’ata kin gane?

Haka rayuwa tayi ta tafiya Sailuba da mai gidanta Baffa ana cin uwar soyayya yayin da inna taci gaba da damun kanta akan rashin jikoki shi kuwa Baffa ko ajikinsa acewar sa haihuwar ma lokacine.

Ana haka ya kammala k’asai taccen gidansa an an wata unguwa tsaka tsaki yabar jerin gidajen ma aikata ya koma nasa, hakan kuma yasa yasamu cigaba sosai dan yakan d’auki wasu daga matasan unguwar irin maau zaman ban zan nan ya bud’e musu wani kasuwancin hakan ba k’aramin kima da daraja yajawa Baffa a idanun iyayen yara ba suna matuk’ar ganin girmansa.

Ganin lokaci yana taja yasaka Inna tace lallai lallai dole Baffa ya nemo mata ya k’ara aure domin bazai yiyu ace suyi ta zama babu aure ba tofa sai lokacin hankalin Sailuba yay masifar tashi dan batayi tsammanin hakan daka ta wajen innan ba.

Muje zuwa

Plss commmen and shire

Takuce maman islam
بسم الله الرحمن الر حيم
______________________

FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION

FCWA

{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________
????BA JININA BACE????
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI

MANAN ISLAM

Page 6
Takasa zaune takasa tsaye dole ta bazama gidan haj. Zakiyya neman shawarar ta, karfa kuyi tunanin haj. Zakiyya yarinya ce kamar sai luba ko d’aya kawai dai irin k’awancen nanne na yanzun dan ak’allah Deedah d’iyar haj. Zakiyya zatayi kusan shekara ashirin sannan bayan ita tana da manyan ‘ya’ya guda biyu da suke karatu a waje yayin da Sailuba a lokacin batafi irin shekaru ashirin da kwai zuwa da takwas dinnan ba domin lokacin da aka yi aurenta da Baffa duka batafi shekara sha takwas ba kunga kenan ak’alla yanzun suna da shekara goma da aure.

Tunda ta gama karanto mata damuwar ta tayi shiru tare da zubawa haj. Zakiyya wacce tai shiru tana buga k’afafunta ak’asa idanu, wata ajiyar zuciya ta sauke tace “kin yi shiru bakice komai ba k’awata kinsan cewa fa wannan ba maganar wasa bane domin nafi kowa sanin cewa duk abinda Inna ta zartar ya zartu domin Baffa baya iya tsallake maganar ta”

“Kuskuren da kikayi kenan Sailuba tun farko saida nace miki ki tashi tsaye ki kama Baffa a hannun ki kikace aike daga shi har uwar sa suna tafin hannun kiyanzun ai kin gani dama wacce uwace bazata so ganin jikokinta a duniya ba kika ce ke duk abinda kike so shi kike samu dan haka bazaki komai ba ai yanzun gashi nan naga ikonkine yake sama da umarnin innan awajen Baffa ko?”

“Dan Allah k’awata duk mubar wannan maganar naji nayi kuskure yanzu dai so nake mu samo hanyar da zan gyara kuskure na kuma mu to she duk wata hanyar da zata kuma b’ulluwa mai kama da wannan” wani shu’umin murmushi haj. Zakiyya ta saki kafin tace komai saiga mijinta ya shigo da sallama kamar mara gaskiya ya soma sand’a zai wuce “kai” ta buga masa tsawar da sai da tasaka Sailuba ta zabura tace “kai wanne irin dak’k’ine dan Allah me yasa bakajin magana duk abinda zan fada maka baya shiga kunnen ka wallahi alh. Lawan duk randa ka kaini bango agidannan bazamu kwashe ta dad’i dakai agidannan ba”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button