BABU SO HAUSA NOVEL

BAJININA BACE COMPLETE HAUSA NOVEL

“Jiki na rawa alh. Lawan yace ” dan Allah haj kiyi hak’uri ban kula daku awajen bane” sannan ya k’araso gaban haj. Sailuba ya durk’isa har k’asa ya gaida ita a sanyaye ta amsa idanunta har sun kawo ruwa tsabar tausayinta daya kamaahi sannan ya tashi sum sum ya wuce sama “kuma ka gyara min d’akin kafin na hawo”
“To” kawai yace mata ya wuce.

Dafa Sailuba tayi tace ” kinga k’awata muddun kikace zaki saka tausayi aranki to aikin ki bazai tafi yadda kike soba kuma ko sune suka samu dama abinda zasuyi miki sai yafi wannan domin sai sun kacaccala rayuwarki”

Haka dai haj. Zakiyya tayi nasarar yi mata hud’ubar shed’an akan su maida Baffa rak’umi da akala akan komai kamar dai yadda taga tanayiwa mijinta, cikin k’ank’anin lokaci aka rushe maganar auren da Inna ta da Baffa basu k’ara d’aga zancen ba har zuwa wani lokaci yayin da Sailuba tasamu hanyar sarrafa Baffa iya son ranta baya aiwatar da komai saida umarnin ta hatta abu idan zaiwa inna sai ta amince inbata yardaba anbarshi.

Akwai wani malam Babba anan k’asan layin da suke shi mutum ne na kwarai wanda yake amfani da ilimin da Allah yabashi shiyasa yasa yake da matuk’ar kima da daraja a idon mutanen unguwar duk lalacewar yaro badai kaji mummunar kalma daga bakin malam babba ba saida fatan shiriya da sanya albarka wannan yasu masa farin jini sosai wajen yara da iyayen su yana damatuk’ar kima a idanun matasan earia dama na kewayen hakan yasa ya bud’e makarantar ialamiyya wanda ake zama daga magriba zuwa sallar esha ranan alhamis da juma a yara da manya haka suke cika amakarantar.

Baffa yana d’aya daga cikin d’aliban makarantar haka kuma bashi uban dayafi malam babba kaf unguwar domin shine mutumin da baya duba girma ko matsayinka zai fad’a maka gaskiya kai tsaye komin d’acin ta kuwa, haka duk sanda Baffa yake gari bashi da wajen hiran yamma sai wajen malam babba haka nan cikin hikima yake dad’a yiwa duk Wanda suke tare nasiha da hak’uri da zaman lafiya da kowa tare da rok’awa duk Wanda ka gani ba akan daidai ba shiriya bawai ka rik’a zaginsa ko la antarsa ba domin hakan ayace wata rana sai ya faru akan ka ko akan d’anka.

Cikin matasan da alh. Baffa ya bawa aiki akwai ‘ya’yan malam Babba guda biyu Kamalu da kuma Usman yana matuk’ar jin dad’in aiki dasu saboda ingantaciyyar tarbiyyar da suka samu daga mahaifin su.

Oh na manta ban muku bayaniba tun lokacin Baffa yana k’auyen su yana da aminiya gsai d’aya Hassan Wanda suka kasance tamkar uwa uba d’aya koman su tare sukeyi hatta wajen kwana ma idan ya sun kwana agidan su Baffa to gobe agidan su Hassan zasu kwana Wanda har hakan yaja wa iyayen su kusanci suka zamo kamar ‘yan uwa na jini.

Sai da aka shafe shekara guda Inna bata kumayiwa Baffa maganar k’arin aure ba saboda danne tan da akayi da k’arfin asiri sai lokaci guda yaje garin Wanda alokacin ma rabon data sanyashi idanunta ma an d’ebi wata kusan biyu mutumin da duk k’arshen sati sai yaje ya ganada mahaifiyar ta ya kai mata abubuwan bak’ata yanzu kuwa sai gimbiya Sailuba tabada umarni wannan kenan

Taku maman islam
بسم الله الرحمن الر حيم
______________________

FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION

FCWA

{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________
????BA JININA BACE????
NA
HASSANA ABDUL AZIZ YAKASA

MAMAN ISLAM

Page 7

Bayan sun gaisa da tare da tambayar juna bayan rabuwa yabata uzuirin cewa baya zama ne shiya sa ta d’an jima bata ganshiba da mamaki ta rik’a kallon sa domin bata tab’a ganin uzurin daya hanashi gaida itaba Sai a wannan lokacin sai dai ta alak’anta hakan ne akan maganar auren data dameshi da ita hakan yasa tace “Allah ya kyauta”

Gyara zaman ta tayi tace “Baffa kamar dai yadda na takura maka na matsa maka har hakan yasa kake ganin kamar na matsa maka dayawa to Baffa inaso kasani ‘ya’ya suna k’arawa mutum martaba da kima idon al’umma kuma ‘ya’ya rahama ne sannan ni’emane da ba kowa Allah yake yiwad,,,irin wannan baiwar ba, kai yanzun ba abin alfaharinka bane ace yau ga sanyin idaniyar kaba kana dubansu kanajin dadi? to inaao ka saurareni da kyau yau muna biyar ga wata dan haka na baka daga nan zuwa k’arshen wata kafito da mata ka aura ko kuma ni na zab’a maka kamar yadda nayi maka na Sailuba”

Shiru yayi yana sharce gumin dayake tsiyayar masa har saida Inna ta kula da halin dayake ciki amma sai tai kamar bata ganiba gyara zaman sa yayi yace “dan Allah Inna ki d’an k’aramin lokaci zanyi yadda kike so amma Inna taya zan fara fad’awa sailuba wannan labarin?”

Sosai inna ta hasala abatunsa ta lura saboda bayason bacin ran Sailuba ne baya so dan haka ta had’e rai tace “au saboda b’acin ran Sailuba ne kai baka son barin baya to wllh kaji na rantse muddun ka bari k’arshen watannan yazo baka nemo matar aure ba ni zan nema maka ance maka ita Sailuban haihiwar take sone da tana so ai bazata rik’ka to she mahaifa tana d’inketa ba ko ance maka bansan halin da kuke ciki bane to ita aminan nata da tad’auki amanar zuciya da rayuwanta ta damk’awa sune suke kewayowa suna kawomin labarin komai dan haka ni na gama magana idan kuma ka isa kai d’ane ka k’etare magana ta kagani duk duniya babu wanda yakaini son Sailuba domin ita d’in ‘yatace halak malak kuma JININA CE sannan rainona ce sai dai a irin tarbiyyan da nabata babu wanda take amfani dashi sai na banzayen aminanta da suke d’orata a keken b’era har nagaji da fad’a mata gaskiya ta nuna bata buk’ata Allah yasani na sauke hak’k’in ta da yake kaina nabata kula da tarbiyyan da ko uwar data haifetane iyaka kenan dan haka na fita hak’k’inta sannan inayi mata fatan shiriya”

Tunda yake baitab’a ganin fushin mahaifiyar tasaba sai wannan karon domin daga shi har Sailuba lallabasu Inna take amma yau kam yaga tsantsar b’acin ranta dan haka ya rik’a lallab’ata har zuwa sanda yabaro garin.

Sai dai babban tashin hankalin sa yadda zai fuskanci gimbiyar tasa da wannan batun yasan cewa ba abune mai sauk’iba ya tunkareta da wannan babban al’amarin, koda yadawo gida haka abin yay ta damun sa arai har gimbiyar tasa tay ta tambayarsa damuwarsa yace babu.

Sau tari idan abubuwa suka sha masa kai yakan nemi shawarar malam Babba wannan karon ma yazo wajen malam d’in kamar ko yaushe neman shawara tare da baran addu a kamar yadda yasaba abin Allah kuma masu Karin magana sukace kaddara ta riga fata anan suka had’u da Amina d’iyar malam wacce tunda yake Allah bai tab’a sawa sun had’uba sai ranar dan dama ba wani sanin yaran malam d’in mata yayiba domin basu cika fitaba sai da babban dalili kuma bayan haka ma dole bazai san Amina domin ko acikin gidan ma abune mai wahalar gaske kayi katarin ganin ta atsakar gida domin koda yaushe tana d’aka.

Tunda yay arba da Amina ya nemi nutsuwar sa yarasa bai tab’a katarin had’uwa da abinda lokaci guda yai tsalle ya shige zuciya lokaci guda ba sai Amina, itace tayi masa kamun dashi da kansa ya kasa daurewa har saida ya furtawa malam Babba hakan, take batare da wani jinkiriba yace ya bashi Amina halak malak yaje ya sanar da mahaifiyarsa kuma insha Allahu k’arshen watan da muke ciki za ad’aura auren haka nan Allah yasanyawa malam Babba k’aunar baffa saboda Baffa mutum ne dayasan darajar manya haka nan ya iya mu’a mala da duk wanda suke tare daahi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button