BABU SO HAUSA NOVEL

BAJININA BACE COMPLETE HAUSA NOVEL

Cikin tsantsar farin cikin daya kasa b’oyuwa ya k’arasa gidansa fuskar nan d’auke da annuri haka ya dinga abubuwa har dai Sailuba ta kasa daurewa ta tambayeshi yace mata babu komai kawai dai yajishine fresh shiyasa yake farin ciki.

Bata k’ara tsinkewa da lamarin ba sai washegari dataga yana shiri ta tambaye shi inda zashi yabata amsa da wajen Inna take taji ‘yan hanjinta sun kad’a tace “naga yau dukafa kwananka biyu da dawowa shine zaka kuma komawa?”

Dakatawa yayi da fesa turaren da yake ya dubeta yace “yanzu dai kina so kice dan na dawo daga gaida uwata shekaran jiyaifi ne kenan dan na koma yau?”

“Ba lafi bane amma gaskiya bazaka koma yauba ina laifin ka bari zuwa koda k’arshen watane amma daga dawowa sai ka wani kwashi jiki kace yau zaka koma nidai gaskiya ban amince ba”

Ta k’arishe da irin yaudararrun kalaman da malamain su yace su d’an rik’a had’awa dasu dan ba ko dayaushe ne aiki yake amfaniba wani lokacin sai an had’a da kissa.

Wani banzan kallo ya watsa mata kafin yace “to uwata ai tunda kin isa sai ki hanani zuwa tunda naga alama kin kai har kin wuce wuyanki yayi kauri” mts yaja dogon tsaki ya juya batare da ya kalli inda takeba ya fice.

Sau tari wasu abubuwan dayake mata sai yaga kamar cikin tsoronta yake ga wani d’an banzan Shankar ta dayake wanda indai zata bashi umarni sai ya bi.

Ita kanta Inna tasha mamakin maganar dayaje mata dashi ba k’aramin farin ciki tayi da irin da ya nemoba dan ita kanta ganau ce akan irin tarbiyyan Yaran malam Babba dan haka batare da b’ata lokaci ba ta tashi ‘kaninta d’aya da k’anin Baban Baffa suje suka kai dukiyar aure da kayan nagani ina so har da nasakun rana.

Babu yadda malam baiba akan su barshi ai shima Baffa d’ansa ne suka k’iya cikin mutuntawa suka baro gidan malam Babba suna ta yaba karamcin sa.

Sanda Sailuba tayi ido biyu da kawun ta dana Baffa saida tasha jinin jikinta domin tasan cewa banza baya tab’a kai zomo rafi.

Maman Islam ce
بسم الله الرحمن الر حيم
______________________

FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION

FCWA

{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________
????BA JININA BACE????
NA

HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI

MAMAN ISLAM

Page 8

Haka nan dai ta yi musu sannu ta kawo musu ruwa da abinci kasan cewar dare yakawo kai domin tsakanin garinsu da nan akwai d’an nisa hakan yasaka dole suka kwana dan ason ransu so sukayi subi motar ‘yan kasuwa.

Duk naci da son jin kwakwaf na Sailuba babu abinda ta fahimta dan babu wanda ya tanka mata har zuwa wayewar gari da suka shirya Baffa ya kuma maida shi har gida anan ne Inna take masa maganar dawo da Muhammad d’an amininsa dayake rik’o tunda shima Hassan shikenan d’an nasa k’wara d’aya kamar rai tundaga haihuwarsa da matar ta rasu bai k’ara haihuwa ba duk kasancewar shima alokacin matansa uku kuma uwar Muhammad itace amarya kuma da ita Allah ya bashi haihuwa wanda shima Innan ce ta raineshi da madara bayan ya isa yaye kuma k’iri k’iri Babba ya d’auke shi ya hana uban shi wanda saboda kara baiko kara waiwayar Baffa akan maganar ba dama matansa ba wani son sa sukeba sun masifar tsanarsa saboda tarin dukiyar da Allah ya horewa Hassan gashi duk cikinsu babu wacce ta haihu hakan yasaka ko k’aunar ganinsa basayi tun yana zuwa gidan idan Baffa ya kawoshi hutu har dai ya gane ba a buk’atar sa shikenan idan yazo sai dai yasamu Abbansa akasuwa suyi wuninsu anan susha hiransu.

Tsanar da Sailuba tayiwa Muhammad kuwa ta ninninka wacce matan babansa sukayi masa domin acewar ta akansa shi kad’ai Baffa ya tare baya kula kowa baya ganin kowa indai yana tare da Muhammad wanda bata da damar musguna masa dan akan yaron tayi imanin zai iya sakinta ga ubansa malamin k’auye injita koda tabi tak’asa babu nasara dan haka ta koma ci masa mutunci da wulak’anci iri iri ga d’an karen gori wannan ne yasamo asalin tsanar da Muhammad yaiwa Umma kamar yadda Baffa yasashi dole yake kiranta dan da farko Sailubanta yake kiranta dan Muhammed tayayyen mutum ne kaifi d’aya kuma mara tsoro sannan baida shakka duk abinda yayi India yasan shine kana tambaya zai ce shi ya aikata wannan abun sai dai kome zai faru ya faru ganin kima da darajar Baffan shine yasa har yake kiran sailuba da umma.

Ak’alla Muhammad yakai shekaru sha biyar a hannun Baffa tun baifi shekaru hud’aba ya d’aukko shi yanzun haka yana shirye shiryen turashi waje karatune dan atsarinsa yafison shima d’ansa yazamo likita kamar shi.

Bayan tafiyar Muhammad da sati biyu aka d’aura auren Baffa da Amina auren da yai mutuk’ar girgiza rayuwar Sailuba domin koda wasa bata tab’a kawowa Baffa aure nan kusa ba domin malaminta ya tabbatar mata da cewar an kawar da tunanin Baffa akan wata maganar aure kujifa wani shirme.

Lokacin da falonsu yake karb’ar bak’uncin ‘yan garinsu, ita kuma sannan tafice a matuk’ar gigice zuwa gidan k’awa aminiya kuma babbar mai bata shawara haj. Zakiyya.

A haukace ta shiga gidan lokacin mijimta yana durk’ushe yana mata matsar k’afafu yayin datake hakimce asaman kujera tana faman shan k’amshi yayin da shi kuma bawan Allahn yake tasharb’ar gumi abin dai gwanin tausayi kamardai yadda ta sharad’anta masa duk sanda wata k’awa ko ‘Yar uwa tata suka zo kuma hakan yazamar masa dole ko ya shiga tashin hankali da masifar ta.

Yau kam baisamu amsa daga haj. Sailuba ba domin a hargitse take dan tundaga bakin k’ofa take kiran “nashiga uku na lalace shikenan k’arshene yazo, yau ni Sailuba naga takaina” yayin da hawaye suke rige rigen zubo mata daga wannan ya fito wani zai tunkud’oshi.

“Lafiya k’awata naganki haka saikace wacce aka aikowa cewa iyayenta sun mace rana d’aya irin wannan tashin hankali haka?”

“Ai wallahi gwanda ace iyayena ne suka mace rana d’aya wannan tozarci da wulak’ancin da Baffa yayimin, baffa tozartani ya nunawa duniya ni ba komai bace Baffa yagama da rayuwata k’awata” tafad’a tareda rushewa da wani shegen kuka wanda yasake d’aga hankalin haj. Zakiyya tai k’uri tana binta da kallo kafin daga bisani ta sauke ajiyan zuciya tace

“Wai duk mai yai zafi kike irin wannan maganganun k’awata?” Majina ta fyace sannan tace “Baffa k’awata shine” ta rik’a maimaitawa babu k’k’kautawa,

“Naji shine, me yayi miki mai zafi haka?” ta katse da tambayarta “waini Baffa zaiwa kishiya?”

“Hmmm shine me?k’awata yanzun ke akan wannan kike d’aga hankakalinki indan wannan ne ai basai kin d’aga hankalinki abanzaba yau d’innan ma Baffa yana iya dawowa yace miki anfasa”

“Daga baya kenan k’awata aure kuma saidai wani amma wannan yafi mintuna talatin da d’auruwa”

A firgice haj. Zakiyya take kallon k’awar tata “aure Kuma? Aurefa kikace shi Baffan neyayi mana wanna cin mutuncin lallai yatarowa kansa dala ba gammo dan wallahi sai yayi nadamar abinda ya aikata manata Kinga yanzun dare yayi babu damar mufita amma gobe da asbah zaki fito mu kama hanya dole ne mu ladaftar da Baffa amma kafinnan zokiji” ta fad’a tare da rad’a mata wani abu a kunne duk da cewa abinda tace ya d’an sanyaya mata rai amma hakan baisa ta saki rantaba domin bak’aramin shammatar ta Baffa yayi ba amma tayi alk’awarin saita shayar dashi ruwan mamaki saita sa yayi nadamar abinda ya aikata mata wallahi

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button