BABU SO HAUSA NOVEL

BAJININA BACE COMPLETE HAUSA NOVEL

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________
????BA JINANA BACE????
2021

        NA

HASSANA ABDUL AZIZ YAKASAI

MAMAN ISLAM

Page 10
Sai bayan kwana shida suka koma wajen malamin wanda Sailuba tace so take daga mijin har amaryar tasa su zamo a k’ark’ashin ikonsa sai abinda tace zasu Kuma su kasance suna matuk’ar jin tsoronta duk abinda ta basu umarni suyi mata shi jiki na rawa.

Sosai malam ya had’a mata mugun asirin da ta dawo gida ta aiwatar dashi cikin ruwan sanyi ta soma azabtar da Amina batare da wata tsangwama amma bauta iri iri hatta wankinsu sailuba sallamar maiwankin tayi Amina ce wankinsu da guga girki shara wanke wanke da duk wani aiki na wahala tana daga zaune zata bawa Amina umarni ita kuma babu musu zata aiwatar.

Cima mai kyau sutura mai kyau da tsada want bacci mai kyau babu abinda ta nema tarasa agidan Baffa ga kulawar dayake da ita amma uban aikin da ake jibga mata asiyasan ce yasa tafara wata irin rama wadda ‘yan uwanta suke tunanin ciki ta had’u dashi mai laulayi tunda basu tab’a katarin zuwa sun tarar da ita cikin wannan uban aikin kamar jaka ba dan boka yace mata ta kiyaye sannan kuma ya tabbatar mata da cewa duk sanda Amina tasamu ciki to aiki ya lalace sai an sabunta.

Haka Amina taci gaba da bautuwa a hannun haj. Sailuba a siyasance batareda ita kanta ta lura da hakan ba domin hatta abinci tare suke ci kuma zasu yi hira suyi wasa da dariyansu koda wasa bata tab’a nunawa Amina wani abuba duk da kasancewar bata k’aunar koda bud’ar idanunta taganta a gidan.

Bayan wasu’yan watanni saiga Amina tana zuba laulayi mai masifar wahala hankalin sailuba kuwa idan yayi dubu to atashe yake domin tunda Amina tafara zazzabi Baffa yakaita asbiti aka tabbatar masa da cikine da ita ya tsinci kansa cikin tsantsar farin ciki ga wata kula ta musamman dayake Bata duk da yana iya bakin k’ok’arinsa wajen danne farin cikinsa dan gudun kada Sailuba taji babu dad’i.

Tunda taji labarin cikin hankalinta yai masifar kad’awa lallai tasan cewa aiki ya lalace kamar yadda boka ya fad’a mata gaahi haj. Zakiyya basa k’asar ita da mijinta ya rakata ganin likita zafine ya had’ar mata dan dole ta danne damuwar ta tacigaba da bawa Amina kulawa ta musamman wanda ya d’auke hankalin Baffa akansu ganin ko baya nan ai sailuba tana nan.

Da k’yar ta samu lambar haj. Zakiyya cikin taahin hankali ta sanar mata da abinda yake faruwa itama ba k’aramin kad’uwa tayi ba dajin wannan labarin sai dai ganin irin halin da k’awar tata ta shiga yasa ta kwantar mata da hankali ta tabbatar mata da nan da k’arahen wata zasu dawo.

Haka dai haj. Sailuba ta daure tacigaba da bawa Amina kulawa na musamman yayin da aranata take kiyasta iya kwanakin da cikin ya rage ajikin Amina Baffa kuwa ba k’aramin Jin dad’in yadda sailuba take kula da Amina yakeba sai ta k’ara wani martaba da kima a idanunsa.

Saboda tsabar iya kissa ko aikin da take azabtar da ita dasu ta daina dan acewar ta lokacin guda zata kwabar da d’anbanzan cikin kowa ya huta, yanzun dai bari ta tayasu raino yadda ko wani abun yafaru babu wanda zai zargi dasa hannunta.


Haka sukaci gaba da tattalinta har zuwa sanda haj. Zakiyya ta dawo a lokacin har ya shiga wata na uku yayin da Baffa kullum cikin take tsantsan da tsantseni yake shima dama can shi mutum ne Mai yawan kyauta samun cikin Amina yasa ya k’ara sosai akan yadda yakeyi.

Kwana biyu da dawowar ta suka d’aga wajen boka sosai suka sha mamakin ganin yadda suna zuwa bai saurara da daga garesuba yabasu wani kullin magani yace “Susan yadda zata Shashi ashayi ba Madara ko gama Sha bazata yiba cikin zai soma murd’a maya ina tabbatar miki wannan cikin bazaya kwana dashiba ajikinta”

Tace “ranka yadad’e inaso ayi mata abinda bazata k’ara d’aukar cikinsaba”

“Bazai yiyuba domin tun farko na fad’a miki akwai yara atsakaninsu Kuma dole zata haifesu sai dai zaki iya yin yadda kikaga dama dasu shine kawai abinda nasani”

Bayan sun baro wajen boka suka dawo gida nan ta ninka kulawar datake bata har zuwa kusan sati tana tunanin yadda zata aiwatar da shirinta batare da wani abu mai kama da zargi ya ahiga tsakaninsuba wannan kenan.

Yau kam Amina tashi tayi sam batajin dad’i sai dai dauriya data rigayi dan kar ta d’aga hankalin mutanen gidan ganin yadda suke dai dai bakin gwargwadonsu akanta.

Tana zaune afalo saman dugowar kujera hah. Sailuba ta rako k’awarta Zakiyya har inda take haj. Zakiyya ta k’araso suka gaisa tayi mata sannu da jiki, da ido tayima sailuba alamar kawai ta aiwatar yau.


Koda ta rakata ta d’an Jima suna tattaunawa da k’awar tata kafin suyi sallama inda ta barta nan ta dawo tasame ta sai dai sab’anin d’azu yanzun idanunta alumshe suke alamun barci yafara fisgarta wani kayataccen murmushi ta saki ta wuce kicin dake ranata d’anyi dan d’aya ya wuce abincin mutum biyu ta dafa mai rai da lafiya daga ita sai Baffanta dan tasawa ranta yau abincin nan bazai ciyu awajen Amina ba.

Hakan cewa kuwa yafaru bayan ta gama dai dai lokacin ana kiran sallah ta fito da nufin tashinta sai k’eyar ta ta hango tana shigewa d’akinta, tabita da wani shegen harara aranta tana fad’in zanyi maganinki ne, daga haka itama ta wuce nata d’akin danyin tata sallar bayan sun idar kusan atare suka fito da Amina wacce takejin wata mahaukaciyar yumwa har hautsina cikinta yake saboda tsabar yunwar dake d’awainiya da ita ganin haka yasa Sailuba shigewa kicin da sauri ta had’o mata ruwan lipton ta kawo mata tace

“Kinga k’anwata fara da wannan naga yau du bakici komai ba bazai yiyu ki farada abinci Kai tsayeba” sosai hakan yayi mata dad’i dan tana da buk’atar hakan, batare da wani tunaniba ta kafa kai tashanyen tas tun kafin ta dire kofin cikinta yai wani irin masifaffen murd’awa wanda tun jiya takejin hakan, da mugun k’arfi ta dafe cikin gami da fad’in washhh, wani b’oyayyen murmushi tasaki ama azahiri k’arasowa tayi da sauri ta kamata “lafiya kuwa k’anwata?”
Ta bud’a baki kenan zatayi mata magana kenan cikinta yayi way irin fitinannen murd’awa sai cewa tayi”babu” cikin pretanding tace “babu me?”

Kasa magana tayi saboda azaba Saida ta Jima kafin ya lafa mata ta dubi Sailuba tace “dan Allah anty ki taima kamin ki Kira Baffa yazo yakaini asbiti mutuwa zanyi”

Da sauri ta nufi hanyar d’akinta tana fad’in “to bari na kirashi gwanda yazo kar wani abun yazo yafaru mushiga uku”

Tana shiga d’akin tasaki wani uban tsalle tana d’ebo shoki farin ciki fal ranta yau burinta zai cika zatayi kwanan farin ciki wannan alak’ak’an cikin zai bar gidansu ta huta daganin tashin hankali.

Muje zuwa
بسم الله الرحمن الر حيم
______________________

FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION

FCWA

{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________
????BA JININA BACE????

2021
NA

HASSANA ABDU AZIZ YAKASAI

MAMAN ISLAM

Page 11

Anan ta k’yaleta tana ta faman murk’ususu yayin da tai kwanciyar ta saman gado tana waya da haj. Zakiyya a maimakon Baffa sosai suke shewa, Jin kamar motsi yasa tayi saurin katse Kiran tana laluben wayan Baffa.

Anty shamsiyya ce ta shigo arud’e domin sanda ta shigo har Amina ta sume ga uban jinin dayake malala ta k’asan ta tana ganin haka tayi d’akin haj. Sailuba arud’e, sai dai tashin hankalin data gani akan fuskar sailuba yaci uwar nata dan hawaye tagani shab’e shab’e a fuskar ta tanama Baffa bayani halin da Amina take ciki.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button