BANBANCIN KABILA COMPLETE NOVEL

BANBANCIN KABILA COMPLETE NOVEL

Ana cikin haka, aka kira zuhur, suka tashi suka yi sallah, suna idarwa, suka ji muryan wasu suna sallama. Daman da aka kira Sallah, Nabila ta koma dakin ta. So tana jin sallama, ta fito, taga kannan Farouq su biyu ne, daman sun saba, sai sukayi hugging din ta.
“Ku zauna, ina ta expecting din Ku tin dazu, me ya hana ku zuwa?”
“Aunty ki bar shirmanmiyan nan Hafiza, kin san ta ai, inba’a ci kwalliya ba, ba’a fita, shi yasa muka dade, hakan ma Umma ta koro mu”. Kanwar sa mai suna Nusaiba ta fada.
“Nikam Allah ya yaye maki wannan cutar, dan in kika yi aure, kuma zaku fita da mijin ki, sai dai ya bar ki a gida”. Nabila ta fada.
“Uhhmmmmm uhmmmmm, su aunty anyi aure, har ansan logic.” Hafiza ta fada.
“Toh kar insan logic ne,
Mtchww. Yauwa kawaye na guestroom, muje ku gaishe su.

Suka gaisa da su Olamide, aka kawo ma su abinci, suka ci, amma still hankalin Mide bai gama kwantawa ba, amma ta kasa nuna ma kawayen ta. Shi daya bar gidan Nabila by 11:30, ace har almost 2:00 pm, bai kira ta ba, hanya kuwa?
Hawaye taji ya jiko idanun ta, sai ta tashi ta shiga toilet kaman zata yi fitsari, ta fara kuka, a hankali, yanda baza su ji ba.
Bata kai 5mins ba, aka kwankwasa kofar toilet, Nusaiba kanwar Farouq, tace “Adda wayan ki na ringing”.
Olamide najin haka, ta fito da sauri, ta karbi wayar, tana ganin wanda ya kira ta, ta yi wani irin murmushi, sanda tayi hamdallah, kafun ta daga wayar.
“Assalamu alaikum! Ta fada zuciyar ta na bugawa, although taji dadi ya kira ta, amma bata san sakamako ba.
“Waalaikumus salaam qalbin Abdallah.”
Olamide taji wani irin dadi a zuciyar ta, sai ta amsa mai da “na’am ifemi”. Tama manta da akwai mutani a dakin. Suko sai kallon ikon Allah suke.
Abdallah ko data kira shi da sunan, sai yaji wani irin dadi na ratsa shi.
“Qalbin Abdallah guess what?”
“Ifemi I am not good at guessing, just tell me”.
“Toh shikenan, bazan so inga zuciya na a wahale ba, so, adda Fadi is ready to receive her in law to be In Sha Allah, tace muzo bayan Asr”.
“MashaAllah, naji dadi sosai, I thought bazata yarda ba, I thought this will be the last time da zamuyi magana, but mashaAllah she accepted me the way I am”.
“Alhamdulilah, she is sooo ready to accept you, ko mijin ta ma yana expecting din zuwan ku. So ku shirya keda habibty, by 4 dot zan zo”.
“Toh shikenan, sai kazo”.
“Please takecare of my heart, dan bana son inga zuciya na a wahale. Take care of Abdallah’s qalbi”.
“Okay, you should also take care of mine”. Tana fadan haka, ta kashe wayar, sai a lokacin tayi realizing ma akwai mutani a dakin, wani kunya ya kamata, zata koma toilet, Nafisa ta jawo ta. “Dawo nan marasa kunya. Wato ifemi, daman nasan pretending kike, akwai kalamun soyayya sosai abakin ki, sai ki dinga cewa zamu koya maki in lokaci yayi, ai yanzu kam sai dai ki koya mana.” Nafisa ta fada tana hararan ta.
“Haba habibty, kya dan tsake ni ai, kin wani rike ni kaman kin kama barauniya, dan Allah tsake ni. Kuma ni bana pretending. Then duk abunda nake yi, awajan ku na koya, especially Nabila”.
“A’a kar kiyi karya da ni, mu dai sai mun zo lectures ko Fisa?”
“Gaskiya kam”.
Suna na kan teasing din ta, suka ji muryan Farouq ya dawo, da sauri Olamide ta riko hannun Nabila, ta kai ta bakin kofan daki, ta tura ta waje, sai tace “je kiji da mijin ki.” Ta fada tana mata gwalo.
Kannan Farouq ma suka fita gaida Farouq. Tayi facing din Nafisa, ta ce “kin san Nabila ce power din ki kuma bata nan, toh ki shiga brain din ki. And yes wai mu shirya by 4 dot zai zo ya kaimu.”
“Toh mummy Olamide, amun afuwa, kar a cinye ni. Kuma in kika sa wasa, bazan je ba”.
“Haba habibtyn Mide, am sorry my sweet miyan kuka”.
“Baki ma ga abunda zaki kira ni ba sai miyan kuka, ba damuwa”. Nafisa ta fada tana faking hurt.
Daman kan gado suke, sai Olamide ta riko hannun ta, ta ce “haba habibtyn Mide, ban san ki da fushi ba, ki yafe ma troublesome habibtyn ki.”
“Naki, sai an bani cin nose.”
“Kaman me?”
“Kaman shawarma”. Nafisa ta amsa.
“Amma fa sai mun koma school In Sha Allah”.
“Naji bakomai”. Nafisa ta fada tana murmushi.
“Amma in na mutu ki yafe mun.”
“Ai dole na, Allah yasa mu cika da imani, ya jikan magabata.”
“Amin”.

Around 4dot Abdallah ya shigo gidan Farouq, ya fara parking, daman Farouq ya san da zuwan shi, sai ya shiga ciki suka gaisa, kafun ya mata text wai gashi nan ya zo. Sanda suka shafa almost minti 10, kafun suka fito. Suka sallame cousin din Nabila, da kannan Farouq, saboda maybe kafun su dawo sun wuce, kuma ma daga yau ai shikenan, sannan suka ma Nabila da mijin ta sai sun dawo.

Da suka fita, Abdallah ya ce su tsaya a inda suke, bari ya kawo motan nan. Suka jira shi, ya kawo motan inda suke, ya bude ma Olamide gaba, akunyace ta shiga, ita kuma Nafisa ta bude bayan da kanta, ta shiga. Sanda suka daidaita zama, sannan yaje gate yana horn, gateman din gidan ya bude gate, suka fita sai gidan Adda Fadi.
Su Olamide sai kale kale suke, shi kuma duk exciting place din da suka wuce, sai ya fada masu sunan, ya kasa boye murnan sa. Nafisa kawai ke magana, ba yanda bai yi da Olamide ta sake ba, amma taki. Ita kuma a bangaren ta, kunya take ji, shi ya hana ta sakewa.
Daya ga yayi yayi bata sake ba, sai yayi tunanin abun da zai fada, yasa tayi magana, wani idea ya zo mai, yace ” kin ga garin ifen ki, kuma where you will be staying very soon In Sha Allah”.
Tayi murmushi, tace “Allah yasa.” Saboda maganan tashi ma kunya ya bata.
Daya ga kaman baza yi magana ba, yayi shuru, domin ya gane kunya take ji.
Haka ya suka yi shuru, har suka isa gidan. The only time din data yi magana, shi ne da suka wuce wani shago, ta ce ya tsaya, dan daman sunyi da Nafisa, zata siyan ma yaran Adda Fadi abu. Daya tambaye su me suke so ya siya masu, tace bakomai, sai yace bakomai ne kuma tace ya tsaya, sanda taga da gaske yake ta fada mai, yace su zauna zai siya, tace mai a’a, ita zata siya, because it’s a gift from her, and zata so ta siya da kanta. Sanda yaga ta dage, shine ya kyale ta, amma yace mata Afra ta fi son chocolate, shi kuma Irfan ya fi son sweets, but suna son biscuit, but those are there best.
Da suka isa, instead yayi horn, ya mata flashing, ta fito, ta bude karamin kofar, ya shiga ta wajan, ya bude gate, ya shigo da motar sa ciki, ya gyara parking, sannan ya fita, Nafisa ta fita, sanda Olamide tayi addu’a, ta fito. Tana fita ita da Nafisa suka taka har inda Adda Fadi take, suka gaishe ta, ita kuma tun fitowan su, take ta kallon su, shi kuma Abdallah ya je rufe gate.
Da Olamide taga sun gaishe ta bata amsa ba, ta kara gaishe ta, dan alokacin har tayi give up, sai taji tace “common, you guys shouldn’t just stand there, give me hug.” Adda Fadi ta fada hannun ta a bude.
A kunyace sukayi hugging din ta. Ta riko hannaye su, tace su shiga ciki, su Afra da Abban su na can.

Suka shiga, Abdallah na biye da su, kuma ya ji dadin yanda Adda Fadi ta tarbe su.

Thanks for reading, and always been patient, zeexee loves you guys.

Comment
Like &
Share.

  Zeexee ce ????️????️????️????️

[8/30, 1:21 PM] Abokiyar Fight????????: ????????????????????????
????
BANBANCIN KABILA
(Short story)
????????????????????????
????

TAMBARI WRITER’S ASSOCIATION

????((Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al’umah))

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Leave a Reply

Back to top button