BANBANCIN KABILA COMPLETE NOVEL

BANBANCIN KABILA COMPLETE NOVEL

Throughout lokacin da Abdallah yake aiki, yaki kallon female patients, sai dai yaji complains din su, ya karbi card, ya rubuta masu magani, ya mika masu, next patient ya shigo. Haka ya ita yi, har lokacin break yayi, suka hadu da Asim, suka fara zuwa masjid, suka yi sallah, kafun suka aiki wani cleaner, ya siya masu drink da biscuit. Saboda basu son cin abincin a waje, gashi ba wanda ya kawo lunch daga gida acikin su. Never the less, by 2 something zasu bar wajan aiki. Kuma gaskiya sunyi missing din Farouq Sosai, click din su bai yi complete ba without him.

Da Mide tayi cutting din call din, ta dinga murmushi, kaman ya na ganin ta. Bai fi 5mins ba, Nafisa ma ta gama waya. Sai ta kalli Mide, taga fuskar ta na dauke da murmushi, kuma if she could recall, she have been smiling like this for the past 5mins. Ta taba goshin Mide tace “naji jikin ki ba zafi, balle ince high fever ke damun ki.”
“High fever kuma, me kika gani?”
“Ae high fever. Keda tun dazu kike ta murmushi, kinga abu na damun ki.” Nafisa ta fada.
“Kema haka, saboda kema murmushin kike.” Olamide ta fada tana murguda mata baki.
“Kya ji da shi ai.” Nafisa ta fada.
Olamide ta sa kan ta saman cinyan Nafisa, tace “barci nake ji, amma in aka shigo garin (Bauchi), dan Allah ki fada mun, saboda ina son inga garin ku.”
“Ai dole na, dole na tashe ki kiga garin habibtyn ki. Wai gani zan wuce gida, amma bazan shiga gida ba, this is too bad.”
“Baki so zuwa gidan ku ba dai.” Olamide ta fada.
“Haba habibty, kema fa kin san tun da muka koma, bamu samu munyi concentrating a karatun mu ba, sai ince mu kara zuwa gidan mu?
Ai sai dai mu kwashi carryover wannan semestern. Moreover ma Abba bazai bari mu zo ba, baki ga ma da kyar ya bari inzo Gombe din nan ba. Cewa fa yayi, inba bikin habibtyn ki bane, ba zaki ba. Sanda na ita explaining, Ummi ma tasa baki, kafun ya bari.” Nafisa ta fada.
“Toh naji Hajiya, ni dai in muka iso BH, ki tashe ni.” Olamide ta fada, tana gyara kwanciya.
“Toh naji kasa.” Nafisa ta fada.
“Oho koma meye, endavour to wake me up, kar kiyi barci fa.”
“Naji Mrs Yero.”
“Yauwa Mrs meye naki ma. Kinga Bila nata Mrs Ardo, ni Mrs Yero, naki fa?”
Sanda Nafisa tayi wani irin murmushi, kafun ta ce “Mrs lacca ce.” Nafisa ta fada tana rufe fuska.
“Toh! Harda guntun kunya?
You try Mrs lacca. Yanzu abun yayi sweet. Ardo, Yero and Lacca. Anyways kar ki manta ki tashe ni.” Olamide ta fada.
“Naji uwar mita.” Nafisa ta fada.
Olamide bata amsa mata ba, dan tasan inta amsa, haka zata ci gaba da jan ta da surutu, har su iso garin (Bauchi), gashi barci take ji.

Abun ba wuya, har sun iso Kano. Daman da suke hanya, Ummin Nabila ta kira Olamide, tace Faeeq zai zo daukan su, ya kai su gidan su Nabila, in suka huta, ya maida su. Kaman tace a’a, sai ta tuna, yanzu Ummi zata ce suna son juna ne, kuma bata son hakan ya faru, tace mata taji.
Suna sauka, daman Faeeq na jiran su, suna sauka, ya hango su, yana ganin Mide ya bata rai, sanda yaga Fisa, ya yi murmushi, yana jin dadi, alanbaran yaga masoyiyar sa, masoyiyar da bata ma san yana yi.

Da sauri, yaje inada suke tsaye, taje ta side din Nafisa, ya ce “sannun da zuwa arewa angel.” Sai ya kalli Olamide ya wani harare ta, itama ta maida mai martani. Nafisa ko murmushi kawai tayi, dan ta san yana neman tsokanan habibtyn ta ne. Sai kuma yace “kawo jakar in rike maki Fisa.”
“A’a na gode yaya Faeeq.” Nafisa ta fada tana mai faking din murmushi.
Yayi yayi da ita, amma haka taki, dan ta san duk abun da yake yi, yi yake dan yaba Mide haushi.

Da suka isa motan, Nafisa da Olamide suka zauna a sit din baya, sai Faeeq ya kalle su, yace “kun san niba drivern Ku bane. Maybe wannan yar yarbawan ta koya maki halin nan, dan gaskiya na san ba haka kike bane.”
Maganan shi ya bata ma Nafisa rai sosai, bata son yanda yake ma habibtyn ta. Rai abace, ta fita ta shiga gaba, ta zauna.
Duk yanda yaso ya ja ta da jira, taki amsa mai, sai kuma ya koma yana ta neman tsokanan Olamide, ita ma ta ki amsa mai, daya gaji, yayi shuru.

Da suka isa gidan su Nabila, an tarbe su da kyau, duk da ba Nabila, ummi bata nuna masu banbanci ba, suna shiga, suka gaida kowa da kowa, da shike basu gama komawa ba (yan biki), Ummi tace suje dakin Nabila, suka je, nan suka kira wayanda zasu kira, suka sanar masu sun sauka. Da suka fada ma Nabila suna dakin ta, ta fara kuka, wai ita tayi missing din su, in short tayi missing din komai. Through wayan suka ita rarrashin ta, har tayi shuru. Ummi ta aika akawo masu abinci daki, suka ci suka koshi.
Basu bar gidan ba sai bayan asr.

Thanks for reading y'all, I appreciate.

Comment
Like &
Share.

~Zeexee ce~ ????️????️????️
[8/30, 1:21 PM] Abokiyar Fight????????: ????????????????????????
????
BANBANCIN KABILA
(Short story)
????????????????????????
????

TAMBARI WRITER’S ASSOCIATION

????((Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al’umah))

*T.W.A*

WRITTEN BY ZAYNAB (zeexee)

MARUBUCIYAR

-RAYUWAR HUSNA

-MAHAKURCI MAWADACI (2020)

2️⃣9️⃣&3️⃣0️⃣

Bismillah

 Da suka koma gidan su (a school), suka gyara ko ina, daman Ummin Nabila ta riga ta basu abincin da zasu ci da daddare. So da suka gama, suka shiga wanka one after the other,  sannan suna alwala. 

Bayan isha, suka ci abinci, suka kai plate kitchen, kowanan su ta kwanta saman katifan ta, suna dan taba hira kadan, kiran Abdallah ya shigo. Tayi murmushi, ta kalli Nafisa, sai Nafisa tace “na san mai kira, you don’t have to behave like this, ki daga kar ya katse.”
“What am I doing din, bana son shishigi fa.” Olamide ta fada, ta murguda ma Nafisa baki, sannan ta daga wayan.
“Asslamu alaikum!” Olamide ta fada.
“Waalaikumus salaam qalbin Abdallah. Ya kike, ya gajiyan yau?”
“Am fine alhamdulilah, gajiya ma ya koma gidan sa.” Ta fada tana dan dariya.
“Baki da dama qalbi. So nace ba, yaushe zaki fada ma mummy, saboda mu san level din relationship din mu.
“Have patience, yau fa na dawo, ka dan bari ko jibi, a lokacin na dan yi settling.”
“Jibi kuma qalbi, I don’t think I can be that patient, why not gobe ki fada mata please, wallahi I want to know the level of our relationship, ina son in san wani matsayi zamu sa soyayyan mu, mu sani idan zamu yi taking din shi further.” Abdallah ya fada yana shafa kai kaman tana ganin shi.
“Toh naji, In Sha Allah gobe zanyi kokarin inga na fada mata. Kai ma, ya kamata ka fada ma su Umma da Abba, ka san dai there decision will also be needed.”
“Kar ki damu, amma inaga ba yanzu zan fada masu ba, sai naga na fada ma siblings dina, kin ga zasu samun baki, alokacin da zan fada masu. Kema dai kin san ni zan fara auran wace ba Fulani ba, so a hankali zan bi su. Kuma kinga idan suka yarda, in kika shigo family, ba zasu bari a wulakanta ki ba, kuma zasu duke ki tamkar ‘yar su ta ciki.” Abdallah ya fada.
“Ban gane ba, ai ba haka muka yi da kai ba, iyaye fa muka ce zamu fada ma?” Olamide ta fada tana kokarin danna fushin ta.
“Na sani, amma irin haka bai taba faruwa a familyn mu ba, ni ne fa na farko, kinga in ina son su yarda, dole sai na bi a hankali. Shi yasa nake son yayyi na su sani, saboda in lokacin fada masu Abba yayi, suma su sa baki, kar abun ya zo masu kaman shock.”
“Hmmmm naji.” Olamide ta fada, without any emotion.
“Bazan taba yaudaran ki ba, bana son muyi aure azo ana wulakanta ki ne, ina son kowa ya dauke ki da mutunci, ba zan so ace Umma ko Abba zasu sa ki agaba, kinsan aure is a life time commitment, so bana son situation din da zaki dinga samun sabani da surukan ki.” Abdallah ya fada calmly.
“Toh na ji, Allah yasa hakan shi ne mafi alheri.”
“Amin.” Abdallah ya amsa.
Daga nan, suka ci gaba da hiran su. Da suka gama, ta ajiye wayar ta, ta kalli inda Nafisa take, taga tana waya, sai ta kwanta da kyau, ta fara tunanin maganan da suka yi da Abdallah.
Allah yasa dai kar su samu matsala, dan tana ji a jikin ta kaman soyayyan su ba zai taba zuwa ko ina ba, tana ji kaman ita da Abdallah sun kusan rabuwa. Tana tunani tana hawaye. Wai meke sa ake nuna banbanci ne tsatanin mutani, me yasa iyaye basu son yaran su su auri outside yaren su ne, kar Allah yasa irin haka ya faru da ita, kar Allah yasa a raba ta da Abdallah, saboda in aka yi haka, gaskiya ancuce ta, saboda bazata taba mantawa da shi ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Leave a Reply

Back to top button