BANBANCIN KABILA COMPLETE NOVEL

BANBANCIN KABILA COMPLETE NOVEL

Olamide ta ci kuka, kuka ta ke na fitan hankali. Shikenan ta rasa Abdallah, she wish she was with Nafisa, at least she will have a shoulder to cry on. Bata son ta fada a gida, kar hankalin mummy dana kannan ta ya tashi.

〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

Da Olamide ta kashe wayar, shima ya fara wani shafin kuka. Ya ci kuka kaman ran sa zai fita. Zai bi umarnin iyayen sa, amma yasan ko ya nuna mata so, bazai taba kaiwa wanda zai nuna ma Mide ba.  

Yana cikin kuka, wani idea ya shigo ma sa, sai ya dau wayar sa, ya kira Nafisa, ya fada mata komai still yana kuka.

“Inalillahi wa’ina ilahil rajiun! Wannan kuma wani irin damuwa ne?
Allah sarki habibty na, abun da take tsoro kenan, amma muka bata assurance cewan hakan bazai taba faruwa da ita ba. Man proposes, but God disposes. This is you guys destiny, kuyi accepting din shi, Allah ya hada kowannan ku da rabon sa, ka daina kuka, it’s breaking my heart wallahi. In kai kana irin wannan kukan, habibty na fa, ya zata yi. Allah sarki, I wish we were together, I would have consoled her. But any ways, this Saturday zamu koma school, and today is Wednesday, so it’s not too far.” Nafisa ta fada.
“Please console her even from the phone, saboda qalbi na is going through alot wallahi. Ina son abi na, amma iyaye na basu so, bazan iya bijire ma maganan iyaye na ba. I hope she forgives me for giving me her heart, but I hope she keeps my heart for me. Thank you for been a good friend to my heart, Allah ya saka maki da jannah.” Abdallah ya fada sai ya kashe wayar.

〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

Olamide na cikin kuka, taji wayar ta na ringing. Bata so dubawa ba, amma her heart was giving her to check it.
Tana dubawa, taga sunan Nafisa.
Ta daga da sauri. Tama kasa mata sallama, ta kara fashe da kuka, tana cewa “shikenan nayi lossing din ifemi, shikenan ni da shi har abada?
Wallahi I can’t love anyone man other than him. Na shiga uku na, me zan fada ma mummy?
Mummyn da she is really happy about these whole thing, me zan fada mata?” Haka Olamide ta ita maganganu tana kuka.

Da kyar Nafisa ta samu tayi consoling din Olamide, tayi shuru.

Amma tana kashe wayar, ta cigaba da kuka.

Har 10:30am Olamide bata fito ba, tun mummy bata yi magana ba, har tazo ta je dakin su Olamide da kan ta.

Mide na jin foot step na zuwa towards dakin su, Olamide ta tashi ta shiga toilet, ta bude tap.

Mummy na shiga, ta ji alamun ruwa a toilet.
Bata fita ba, ta zauna akan gadon Olamide.
Olamide na fita, ta fara mata masifa.
“Kinin seyo na (meke damun ki ne wai)?
Tunda safe baki fito ba, wa kike son ya dafa maku breakfast?
Wannan wani irin dabia ne?
Wato ke kina nan kina barci, mu kin bar mu da yunwa.” Haka mummy ta ita ma Olamide masifa.
Allah sarki Olamide ta ma kasa ce mata komai in ba mummy kiyi hakuri ba.
Mummy taja wani irin tsaki, har tana hararan Mide, sai tace “if you like stay there, sorry din ki zai dafa mana brakfast.”
Mummy na gama magana, ta fita ta bar dakin.

Tana fita, Mide tasa hannun ta a kai, tace “yau kam na ga ta kai na. Dame zan ji, da mummy ko heart?”.

Thanks for reading, zeexee love y'all.

Comment
Like &
Share.

~Zeexee ce~ ????️????️????️

[8/30, 1:21 PM] Abokiyar Fight????????: ????????????????????????
????
BANBANCIN KABILA
(Short story)
????????????????????????
????

TAMBARI WRITER’S ASSOCIATION

????(( Home of Expert and Telented writers, da tambarin mu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al’umah))

*T.W.A*

WRITTEN BY ZAYNAB (zeexee)

MARUBUCIYAR

-RAYUWAR HUSNA

  • MAHAKURCI MAWADACI (2020)

4️⃣6️⃣&4️⃣7️⃣

Bismillah

Har Allah yayi yau Saturday, Olamide zata koma school, ita kadai ta san irin dadin da take ji, at least she will have a shoulder to cry on. Saboda within Wednesday to this Saturday, ita kadai ta san abun da ta ji. Ko zata yi kuka ma a boye take yi, saboda bata son yan gidan su su sani.
Kana ganin ta, ka san abu na damun ta. Ko su mummy ma sunyi noticing, da suka tambaye ta, ta ce bakomai, tana jin ciwon kai ne, aka sata dole ta sha maganin ciwon kai.
Jiya which was Friday, da Mummy taga yanda Mide ta rame, ita da daman ba wani jiki gare ta ba, ta kara ramewa, sai wani uban kan daya karu.
Mummy was so disturbed, ta tambaye ta abun da ke damun ta, ko bata jin dadi ne bata fada ba. Sai tace ma mummy wai maleria kedan damun ta, amma ai tana shan magani, ta samu maganin maleria a cikin first aid box din su.
Mummy tace ko zata bar zuwa school zuwa next week, saboda a mata treatment mai kyau, da sauri tace a’a, bawai ciwon na wani damun ta bane, ta san abu kadan ke ramar da ita.
Mummy tace haka ne. Amma Hakeem ya kasa yarda da maganan, shi yasa jiyan da daddare, ya je dakin su ya same ta cikin blanket, daman Farida bata ciki, yayi sanda, har ya isa inda take, sai yaji shashakan kuka, ya yaye blanket daga kan ta, a zabure ta tashi, tana goge hawayen ta.
“Dan Allah Hakeem me haka?
Baka san meye knocking bane ko sallama, ko kuma rashin hankali ke damun ka.” Olamide ta fada mai kan ta a kasa, a dole tana rufe mai fuska karya ga hawayen ta.
“Koma meye, shi ke damu na. Ance maki ban san karya kike ba?
Tun ran Wednesday nake ta noticing change in you. Tun ranan fa idanuwan ki a kunbure suke, kuma suyi jazur. Na san mummy ma ta san karya kike, ta kyale ki ne kawai.
Yanzu dai ina son ki fada mun tsakanin ki da Allah, kar ki mun karya. Ni dan’uwan ki ne na jini, kuma baki da yan’uwan da suka wuce ni da Farida.
A matsayin ki na babban yaya wanda bata taba son taga bacin ran kanne ta, ki fada mun abun dake damun ki.” Hakeem ya fada hannayen sa akan shoulders din Mide.
Maganan sa yayi touching din heart din ta. Truely bata da wanda yafi su, ko Fisa ma a bayan su take. Ta kara fashewa da kuka, sannan tayi hugging din kanin ta.
Ta kasa fada mai komai, inba kukan da take ba.
Da AbdulHakeem yaga wannan kukan ba me karewa bane, sai yayi thinking of an idea din da zai iya sa ta bar kuka, ya ce “ko kina da ciki ne?” Hakeem bai gama rufe baki ba, yaji saukan mari.
“A’a ciko nake da shi.” Olamide ta fada tana hararan shi d jajjayan idon ta.
“Am very sorry aunty ta ta kai na, I hate to see a strong woman like you cry. Me ke damun ki ne please?” Hakeem ya tambaye ta disturbed.
“Hmm Hakeem, abun dake damu na ba kadan bane, amma karka dau wani mataki, and promise me bazaka fada ma mummy ba.” Ta fada.
Olamide ta san idan ta fada ma Hakeem, yana iya kiran Abdallah ya mai rashin mutunci, kuma gasiya bata son hakan ya faru, dan koba komai sunyi soyayya, kuma har yanzu suna son juna, kaddara ne dai kawai.
“I promise.” Hakeem ya fada.
Nan Mide ta fada mai komai.

Hakeem yayi fushi sosai, yace mata sai ya kira Abdallah, daya san a familyn su baa yarda a auri wani kabila, me yasa yace yana son ta, wato ya san hakan zai faruwa, amma ya zabi yayi breaking din heart din sister din sa.
Da kyar Olamide ta samu tayi calming din shi down, sannan ta tuna mai da alkawarin daya dauka.

So a gidan su, Hakeem kawai ya san abun daya faru.

Da sassafe Hakeem da Farida suka raka Olamide tasha, inda zata hau motan kano.
Hakeem ke driving. Farida kuma nata fada mata how much she will miss her, duk da cewa ba randa baza su yi fada ba.

〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

 Tun ran da Abdallah ya fada ma Mide abun nan, ya dawo kaman marasa lafiya.

Ran Thursday ma daya je gurin aiki, da kyar yake attending to patients, sai ya rubuta medication, sai ya kara gogewa, saboda rubbish kawai yake rubutawa.
Ko kuma inya tambayi patient abun dake damun su, in suka fada mai, kafun ya rubuta medication, sai ya manta abun da suka ce ke damun su, sai kuma ya kara tambaya.
Daya isa wajan aiki ran Thursday, ya fada ma abokan sa komai, duk sun tausaya masa.
Farouq yace Nabila bata sani ba ne, data fada mai maybe.
Yace ai jiya abun ya faru, kuma shine ma ya fada ma Nafisa.
Asim yace toh kar Allah ya sa Nafisa ma tayi fushi tace bata son shi.
Abdallah yace mai, karya damu hakan bazai faru ba, ai ba banbancin komai a tsakanin su. Suma din kaddara ce ta fada akan su.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Leave a Reply

Back to top button