BANBANCIN KABILA COMPLETE NOVEL

BANBANCIN KABILA COMPLETE NOVEL

Data shiga ciki, ta samu Nafisa ta jingina da pillow, tayi lamo kaman bata jin dadi. Ta cire hijabin ta, tayi hanging din jakar ta, ta sa takalmin ta amazunin shi, sannan taje kusa da Nafisa, ta taba ta, tace “ya akayi ne habibty, tun awaje naga mood din ki ya chanza”.
Sanda tayi wani nishi, ta ce “babu, me kika gani”?
“Don’t ask me that, na san akwai abun da ke damun ki, ki fada mun mana please, kar ki bari hankali na ya tashi”.
“Babu komai fa, am just resting ne kawai”.
“Please stop telling me that, kin san bana taba kaunan in gan ki ahaka, hankali na na tashi”. Olamide ta fada helplessly.
“Ba komai my habibty, let just say ina missing din gida ne”.
“Ban yarda ba Nafisa, ban yarda ba. I thought am like a sister to you, then what is my role as a sister”? Mide ta tambaya.
“To always be there for me in any situation, and vice versa”.
“Then why are you not letting me play my role”. Alokacin, har idanuwan ta sun kada.
“Bakomai, kawai dai, kawai dai”. Bata iya completing din statement din ta ba, ta fashe da kuka.
Abun so ya samu, Olamide ma ta fara kuka. Sai suka rungumi juna suna kuka, Olamide na rarrashi Nafisa. Cikin kuka Nafisa ta ce “na sani inga ana miki shishigi, yana kona mun rai, na tsani inga mutum na nuna maki so agaba na, sai in dinga jin wani iri. Wallahi na dauke ki tamkar yar’uwa ta ta jini, shi yasa kika ga nake kishi akan ki. Kina nuna mun son da maybe in ma ina da yaya ko kanwa, da kyar sununa mun. Kuma soyayya bai tsaya akan ki ba, harda Mummy da kannan ki, kuna nuna mun so sosai. Shi yasa in naga wata na kokarin shige maki, sai inji kaman za’a kwace mun ke”. Ta fada tana kara volume din kukan ta.
“Shiiiiii, ya isa haka habibty, bana son kukan nan, kar ciwon kai ya kama ki”. Ita ma ta fada tana kuka.
“Zan daina, amma sai kinyi promising dina ba zaki bar ni ba, zaki tsaya da ni kaman yanda true sisters ke tsayawa da juna”. Nafisa ta fada.
“Am not perfect, and I don’t know what tomorrow holds, amma ina son ki sani I will always be there for you ore mi( kawa ta)”.
“Shikenan, na daina kuka, kema ki daina. Kuma nima na maki alkawari, I will always stand by you”.
“Yauwa, ki daina kishi, Fai’za ta Nafisa ne, itama Nafisa ta Fai’za ce”.
“Ae”. Nafisa ta amsa, tana goge hawaye.
“Kinga tashi muyi alwala, ana kiran sallah”.
“Okay toh. Amma me zamu ci ne da daddaren nan, wallahi yunwa nake ji”.
“Toh mu ci talliya mana”. Olamide ta fada.
“Gaskiya kam, tunda muna da stewssssss”.
“Hahhhh, gaskiya kam muna da su”.

Da suka idar da sallan magrib, suka sa talliya awuta, kafun isha, har ya dahu sun ci, kafun suyi isha. Suna idarwa, kaman su Halima na ganin su, suka shigo.
“Ooooh yes Olamis, mun zo shan hira. Kinsan jiya da kika dawo, bamu nan, munje gidan aunt dina, nan muka kwana”. Hafsah ta fada.
“Hmmm haka ne. Ko dai anje hmmm….”. Olamide ta fada tana murmushi.
“Kefa mun chanza, mun daina”.
“Allah yasa”. Nafisa ta fada.
“Ke zan mazge ki fa”. Halima ta fada.
“Ki mazge ta, adalilin me”? Olamide ta fada.
“A’a aunty, kar kiyi fushi. Mun san baki son ana tsokanan habibtyn ki”
“Gaskiya kam bana so, ko kadan”. Halima ta amsa.
“Ku manta da wannan, mu sha hiran mu kawai”. Hafsah ta fada.
“Ae ku sha hiran ku. Ba shekaran jiya na dawo ba, me ya hana ku zuwa shan hira”? Nafisa ta fada.
“Babu, kema fa kin san mun fita, kuma ai da muka dawo mun dan shigo ai”. Halima ta amsa.
“Ya isa. Kun san me”? Hafsat ta tambaya.
“Ya zamu sani”? Olamide ta fada.
“Kai habibty, you always have answers to every question”. Nafisa ta fada, tana dariya.
“Kuyi shuru mana”. Hafsat ta fada.
“Mun yi”. Suka fada a tare.
“Aha, Nabila fa ta kusan aure”.
“Wace Nabilan”? Olamide ta tambaya.
“Nabila kawar ku mana, bata fada maku ba ko?
Actually nima dai ba ita ta fada mun ba, naji ne, kin san gidan su ba nisa da gidan aunty na”. Hafsat ta fada.
“Ai ko in bata fada mana ba, baza mu je ba ko habibty”? Olamide ta tambayi Nafisa.
“Ae, mu bamu gayyan sodi”. Nafisa ta amsa.
“Kai! Why is your blood rushing, ai bata fada ma kowa bako, kuma dai kun san zata fada maku”. Hafsat ta fada.
Olamide tayi wani dariya, sai ta ce “abun ya yuwu da dan gombe kenan”. Tana fada, suka tafa da Nafisah.
“Toh ku ma yaushe za’ayi naku”? Halima ta tambaya.
“Randa Allah yaso. Kuma kema kin yi ne”? Nafisa ta tambaya.
“Toh ai na kusa, next year In Sha Allahu, maybe june’.
“Allah ya kai mu, amma still you have no right to ask us, tunda ba’a gwanjo ake samo mazan ba”. Olamide ta fada.
Duk suka fashe da dariya.
“Gwanjo kuma habibty?
Kin san gwanjo ma akwai grade ko”? Nafisa ta tambaya.
“Ae da anan ake samun su, da zamu dinga zuwa da wuri, dan mu samu grade, ba zamu ba in 9:am yayi , sai dai ya same mu acan”. Olamide ta fada.
Duk suka kara fashewa da dariya.
“Kai Olamis, baki da dama. Shiyasa nake son hira da ke. Although kin iya shunning din mutum, amma still kina da ba mutum dariya, but banda angry part din ki, lokacin da kike mantawa kinba mutum nickname, sai ki kira sa da sunan sa”. Hafsat ta fada.
“Bari kawai yar’faran habibty, ai in habibty tayi fushi, ta na mantawa da soyayyan da take nuna ma mutum. Kinga in tayi fushi, alokacin zaki ji tana NAFISA SULAIMAN”.
Duk suka fashe da dariya.
“Bari kawai ba zaku gane ba. Ai alokacin, nickname baya mun dadin fada, sai dai sunan mutum”.
“Toh Allah ya shirye ki. Ya zaki yi da mijin ki, ko shima da sunan sa za’a na kiran sa, in ya kai ki neck”? Hafsat ta tambaya.
“Ke abu kadan miji, baki gajiya ne. Toh ko shima, zan kira sa da sunan sa, so he will know am serious”.
“Toh ai it’s not my fault, at this stage of life, abun da ya kamata mu damu da shi kenan. In mu kayi aure kuma, mu fara maganan yara”. Hafsat ta fa.
“Toh sannu marriage consultant. Kai yar’fara, wanan aikin zai miki kyau fa”. Olamide ta fadi.
“Sosai ma”. Halima da Nafisa suka amsa.

Su Halima basu bar dakin su Olamide ba, sai 9:39pm. Nan ma, saboda Olamide ta masu complain cewan suna jin barci ne. Inba haka ba, basu ki aita hira ba har cikin dare. Wani hiran ma sai sauran hudun sun dawo.

〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

Da kyar Abdallah yake cin abinci, saboda tunani ya mai yawa. Of course shi ya san yana son aure, amma da wanda za’ayi shi ne matsalar sa. Ina zai fara. Kuma ko su Umma basu fada ba, shi bazai iya auren cousins din sa ba. Hamma Sudais din daya yi, yaga zai iya ne, kuma ma ai yayi hitting din jackpot, saboda matar shi akwai hankali. Ko adda Wasilan da take cewa ya zaba daga cikin su, ta manta da abubuwan da duka fada akan ta ne, ita da suke cewa zata auri mijin ta ne saboda kudin sa. Amma data yi aure, ta fara fita, tana daukan wanka, suka soya hali, ko wannan su ta zama yar dakin ta, iyayen su ma suka zama abokiyar ta. Ita kuma Adda Bilkisu, tana da kudin kan ta, kar ma ayi maganan na mijin ta, yasa suke ribibi akanta, ita da ma ba’a nan take zama ba, tunda Allah ya buda ma mijin ta, ya samu aiki a dubai, suka fara son ta, harda yayan ta. Basu ki yayan suce masu suzo su taka kan su ba, saboda tsabaragen son abun duniya. Ita kuma Adda Fadila, mijin ta akwai rufin asiri, ba laifi. Dan itama ba zaka ganta ka raina ta ba. Amma abun mamaki, sun raina iyayen su, amma suna son yayan su saboda abun duniya. In shima ya auri daya daga cikin su, shi ma zai zama dan so. But to hell, bazai bi abun da kawu Dajjo ke so ba. In sauran nayi, shi bazai yi ba. Shi zai bi umarnin iyayen sa ne.
“Abdallah! Abdallah!! Abdallah!!! Sanda Abba ya kira sunan sa sau uku, kafun ya amsa.
“Na’am Abba na”.
“Naga baka cin abincin ka ne”? Abba ya tambaye shi.
“Bakomai Abba, ai ina ci”.
“A’a, Abdallah bamu saba ganin ka haka ba, kai da you are always there to make us laugh”. Umma ta fada.
“Toh ai shi ne”. Abba ya fada.
“Bakomai. Bana ma jin yunwa, sai da safen ku”. Ya tashi zai tafi dakin sa, Abba yace ya dawo.
“Gani Abba na”.
“Zauna”.
Ya zauna.
“Nasan abun dake damun ka, kar ka damu da abun da tsohon nan ya fada, na shi kawai yake fada. Ni yanzu zan bari ne ya maka auran dole ne?
Kuma in aure ne, lokacin ka ne baiyi ba auta, in lokaci yayi, ba mai iya stooping din shi. Saboda haka, ka saki jiki ka ci abinci”.
“Ai kuwa. Ka daina damuwa da bad energy. In yaga sauran na dancing to his tones, toh ai ya kamata ya san mu kam bamu cikin su. Kuma ka auri koma waye, but make sure she will be a good wife and mother to your kids”. Umma ta fada.
“Am in support of what your Umma said. Ba dole bane ka auri bafulatana ba, ko bahushiya ka samu kuma ta zauna maka, ko shi bazai daura auren ba, ni zan daura agidan nan. Nine uban ka ba shi ba”. Daga yanda yake magana kasan ran Abba ya baci sosai.
“In Sha Allahu, nagode sosai Abba na da Umma ta, Allah yasa ku dade mana, Allah ya saka maku da aljannah, thanks for the support”.
“Bakomai, ai responsibility din mu ne as iyayen ka ko Hajaju”? Abba ya tambayi Umma.
“Kwarai kuwa”.
“Barci nake ji, gobe ina da morning duty”. Abdallah ya fada yana hamma.
“Toh, kuma kar adawo gobe ayi mana complain, dan naga yau da wuri za’a yi barci”. Umma ya fada.
“Toh ai ina huta gajiyan yau ne, gobe ma ai zan yi nashi gajiyan ko Abba na”. Abdallah ya tambaye shi”.
“Haka ne auta na., ko wani rana nada gajiyar sa”.
“Wannan kuma ku kukasani” .
“Manta da ita Abba na, kishi take” Abdallah ya fada. Yana magana, Umma ta dau pillow, ta jefa masa, amma yayi sauri ya bar wajan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Leave a Reply

Back to top button