BANBANCIN KABILA COMPLETE NOVEL

BANBANCIN KABILA COMPLETE NOVEL

  *WAYE WANNAN SURAYIN?*

Sunan shi Abdallah, shakarun sa 25, medical doctor ne, kuma yana zaune ne da iyayen sa a jahar Gombe. Bafulatani ne gaba da baya. Su biyar iyayen sa suka haifa, Sudais ne First born, sai Bilkisu, sai Wasila, Fadila, sai shi Abdallah, autan su.
Familyn su ba Familyn masu kudi bane, amma alhamdulilah, akwai rufan asiri sosai, gashi kuma Allah da ikon sa, duk yaran suna da aiki masu kyau, hatta matan, Saboda Alhaji Umar Muhammad Yero baya barin yaran sa suyi aure basu gama karatu ba, sanan sai ya san yanda zaiyi, su samu aiki a wanan kasan tamu da samun aiki nada wuya.
Sunan Mahaifin sa kaman yanda na fada Alhaji Umar Muhammad yero, sunan Mahaifiyar sa Hajiya Rukayya Muhammad Yero.
Abdallah akwai shagwaba tamkar na mace, ba ranan da bazai dawo daga aiki baiyi complain ba, kuma kullum complain din na chanzawa.
Shi mutum ne da baya cika son hayaniya, indai ba da Familyn sa ba, amma in ya fita wajen, zaka rantse bai ma iya magana ba, saboda tsabarage miskilanci irin na sa. Amma agida kam, sai a slow, dan akwai tsokana agida, ga shagwaba. Yayyin sa Mata duka na biye masa sosai, dan duk abun da yake so suke mai, ba su son suga ran sa ya baci. Amma Umma da Hamma Sudais, kullum cikin tsokanan sa suke.
Suna da extended family sosai, kuma every end of the month, suke meeting, nan suke haduwa da duka cousins din su, aunties da uncles. Awannan meeting din ake hada wasu daga cikin su su auri juna, amma if you are so lucky, za’a bari ka auro daga waje, but she must be fulani. Tun lokacin daya fara aiki, shekara biyu kenan, ya san dole fa wata rana ayi tambayan mata, ko kuma ahada shi da cousin din sa, shi kuma kaf cikin su ba wanda ta mai, so duk sanda zasu yi meeting, either yace baya jin dadi, ko kuma ya daure fuska, ko ya zauna shuru kaman baya wurin don kar ma ayi noticing din shi.

 ~Wanan ke nan~

Da suka dawo daga masjid(shi da Abba), basu tsaya ako ina ba, sai a dinning.
“Umma ina abincin ne, karfa ulcer ya kamani yau” ya fada ashagwabe.
“Kai Auta, ai yanzu zata kawo, ka dan yi hakuri kaji, kuma In Sha Allahu bazaka kamu da ulcer ba”. Abba ya fada yana jan hancin shi.
“Kama mutu ne ba ulcer ba. Kana zaune anan ba zaka zo ka taya ni dauko abincin ba, amma kana mu maganan ulcer, ya dadde bai kama ka”. Umma ta fadi tana dauke da kuloli.
“Haba Hajiya, auta ne fa”? Abba ya fadi yana zaro idanuwa nan nashi kaman zasu fado,dan mashaAllah, Abba kam akwai manyan idanuwa, kuma kaman yanda kuka sani, magaji mafiyi, so Abdallah ma akwai su mashaAllah.
“Fada mata Abba, ni na rasa abun da yasa ta tsane ni” ya fada yana faking din kuka.
“Mtchwwwwww” Umma ta ja tsaki, sanan tace “ka tashi kaje kitchen, zaka ga plates da spoons, da cups, ka kawo su dinning”.
“Duk wannan ni kadai zan dauka, haba Umma nifa na miji ne, kuma mata aka sani da shigan kitchen ko Abba na “? Ya fada ya na kallon Abba.
“A’a ni ban san da wanan ba, saboda baya cikin Alqur’ani ko hadiths”.
Tunda yaji Abba ya fadi haka, ya san Abba bazaiyi bailing din sa ba, ya tashi ya tafi kitchen, ya kwaso abubuwan da Umma tace ya kwaso, daya bayan daya, sanan Umma tayi serving dinsu.
Cikin natsuwa, suke cin abinci, har suka gama, nan ma shi ya washe plates ya kai kitchen, sanan suka dan taba hira, kafun kowanan su ya wuce dakin sa.

〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

Farida na idar da Sallah, sanda Mummy ta bari tayi addu’a, ta ce kilode (meya faru), me yasa bakiyi adakin ku ba”?
“Wallahi Mummy Aunty ce, mon beru (ina jin tsoro).”
“Manta da ita, ba abunda zata miki kinji ko”? Mummy tayi magana tana daga gira.
“Toh Mummy Allah yasa. Kinga ma na manta ban dauki night wear dina ba”.
“Karki damu, in muna cin dinner kije ki dauka kinji”.
“Toh Mummy na”. Ta fada
Da Hakeem ya dawo, yaga parlor, ya ga wayam, shima ya shige dakin sa.
Abun ba wuya, har ankira Isha, nan ma yaje masjid, Mummy da Farida su kayi tare adakin ta, ita kuma Olamide tayi adakin su. Kowanan su na idarwa, yayi addu’a, duk suka fito daga dakunan su. Daman suna idar da Isha, suke fitowa dan suci dinner.
Farida na ganin Mide, ta manne ajikin Mummy, tana tsoron karta cafko ta, itako ko ajikin ta, dan kitchen straight ta tafi, ta fara kwaso kuloli, da kayan da zasu ci abinci da shi, ta kai parlor, tasa masu a tsakiyan parlor akan center Capet.
“Yau kuma ba’a dinning zamu ci ba”? Hakeem ya tambaya.
Mide ta mai shuru, kaman ba da ita yake ba.
Farida ce tace “ka manta ta ce bazata yi magana da kowan nan mu ba”.
Hakeem ya fashe da dariya, ya ce ” ai na manta ta zama kurma”.
“Ni kam ba ruwa na, ka ga dai saboda da kai yanzu ina cikin trouble ko”.
A fusace ta ce “kuyi shuru ku ci, ko kuma ku tashi mana anan”.
“A’a e ma binu (a’a kiyi hakuri), ba zamu kara ba” Farida ta fadi.
“Ni kam zan cigaba”. Hakeem ya fada yana dariya.
Abun ya bata mata rai sosai, sai ta ja tsaki ta bar wajan. Tana tashi, Farida da Mummy suka kalli Hakeem, Farida ta ce “shikenan ka ja mana wani masifan, kai baka san aunty Mide sai da rarrashi ba, ga shi ban dau nyt wear dina ba” ta fada kaman zatayi kuka.
“Ni kam Farida ki daina damun mu da maganan night wear, ba zaki rasa adaki na ba. Kai kuma Hakeem, ka san yanda zaka lallabi yayar ka, ta daina fushi, dan kai kaja komai”.
Ya ce “toh” yana wani hura hanci.
“Amma Mummy kin san ba zata saurare ni ba yau, sai dai gobe in Allah ya kai mu”.
“Allah ya kaimu”. Mummy ta fada.

“Amin” Hakeem da Farida suka amsa.

Aranan, ran Olamide abace tayi barci.

Ya kuka ga wanan salon? Allah yasa dai kunji dadin shi.

Thanks for reading, karku manta da sharhi, saboda sharhi is life????????????????????.

Comment
Like & Share

 ~Zeexee ce~ ????️????️????️

[8/30, 1:19 PM] Abokiyar Fight????????: ????????????????????????
????
BANBANCIN KABILA
(Short story)
????????????????????????
????

TAMBARI WRITER’S ASSOCIATION

????((Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al’umah))

*T.W.A*

WRITTEN BY ZAYNAB (zeexee)

MARUBUCIYAR

-RAYUWAR HUSNA

  • MAHAKURCI MAWADACI (2020)

3️⃣&4️⃣

Dedicating this page to those who commented on the first chap, I love you guys loooooooooooods.

Bismillah

Around 3:30 am na dare ya tashi, yayi sallan dare, yana yi har lokacin Fajr yayi, ya yi raka’a taini fajr, sanan ya fito parlor, suka hada hanya da Abba, suka je masjid.
Da suka dawo kuma, tunda yana da dutyn safe, ya fara shirye shirye.
“Ya ilahi, gaskiya I need a wife. Da ina da mata, duk wannan shirye shiryen ita zata mun. Kawai sai dai inji tana tashi na, ta ce qalbi ka tashi kayi wanka, ta cire mun kayan da zan sa, ta sa mun coat dina da briefcase di na waje daya, ta ciro mun covered shoe dina, shima ta sa mun a one side. Ina fita kuma ta mika mun ina sawa, in ta gama dressing dina, sai tace qalbi muje dinning ka ci breakfast. Ba kaman Umma ba, da zata dinga mu fada. In kuma na gama cikin breakfast, sai ta rike mun briefcase, ta raka ni har mota, sannan ka fun in shiga, tayi hugging dina, sai in shiga mota, ta mika mun briefcase, ni kuma in diga mata flying kisses, sannan in kuna mota, ita kuma ta dinga waving dina har in bar haraban gidan mu”. Ya fadi ya na wani irin smile.
“Amma gashi yanzu ni ke komai. Da ma lokacin da adda Fadi take nan ne, maybe data mun. Duk da cewa muna fada sosai, dan ita nake bi, still na san zata mun”. Ya fada with frustration.
Haka ya ita surutun shi shi kadai, har ya gama shiri, ya fita ya je dinning, ya ga ba kowa. Tun dama da kyar suyi breakfast tare inba weekend ba, ko kuma ran da yake da dutyn rana. Rai abace, ya shiga kitchen. Yana son ya fara girka indomie, yaga note akan kula. ” ka ci, ba dan halin ka ba”. Yana ganin handwriting din, ya san na Umma ne. Sai ya saki murmushi, ya dauki abincin, ya kai dinning, ya ci. Sanda ya koshi kafun ya kwashe kwanonin, ya kai kitchen. Daya gama kintsa komai, ya je dakin Umma, ya mata sallama, ta mai adawo lafiya, da addu’oi, ya je dakin Abba, shi ma ya mai, sannan ya fita, ya kama hanyar asibiti.
Yana driving yana bin kira’an sheik Abdulrahman Sudais, sai kawai ya fara addu’an Allah ya ba shi mata, shi ya fara gajiya da irin rayuwar nan, shima yana son yayi kyau kaman Hamma Sudais. Haka ya ita tunani har ya isa asibiti.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Leave a Reply

Back to top button