BANBANCIN KABILA COMPLETE NOVEL

BANBANCIN KABILA COMPLETE NOVEL

Da Adda Fadi ta bar wajan, sai Abdallah yace “qalbin Abdallah, dan Allah ki sake kin ji?”
“I will”. Ta fada tana murmushi.
“You should please. Adda Fadila bata da matsala wallahi, kuma in kika sake, zaki ji dadin ta. Inma so kike in bar ku tare ne anjima inzo in dauke ku, am okay with that, I just want you to be comfortable.”
“No, ba sai ka bar gidan ba, In Sha Allahu zan yi kokarin sakewa. Kuma tunda ina tare da habibty, sakewa kam ya zama dole.”
“That’s good. Habibty ki sa ta sake sosai please.”
“Baka da case ai.” Ta fada tana murmushi.
Sai Afra ta zo kusa da Olamide, tace ” kece wife din Uncle, wai kunyi dinner ne?”
Maganan ta ya basu dariya, Nafisa ta ce “Afi bama aure ba, dinner suka yi.”
“Ae, ai dinner shi ne aure, ko Uncle?” Ta fada tana kallon Abdallah.
“Ni kam ban san wannan ba Afin uncle, amma maybe qalbin uncle ta sani.” Ya fada yana kallon Olamide.
“Sunan ta kenan qalbi?”
“Ae sunan ta kenan qalbin Abdallah, amma zaki iya kiran ta qalbi.” Ya fada still idon shi na kan Mide.
Sai taje kusa da Olamide kuma, tace “qalbi ai dinner shi ne aure ko?”
Olamide ta kalli Nafisa, ta kalli Afra, ta kara kallon Nafisa, ta kara kallon Afra.
“Ki fada mata mana, tana jiran amsan ki qalbi.” Nafisa ta fada.
Olamide taji kunya sosai. Data ga still Afra na kallon ta in a way that says I need an answer.
“Amm Afra baby, dinner ba shi ne aure ba, dinner is just a party which takes place during wedding functions. Shi kuma aure, is the coming together of two different people, to become one.”
“Okay toh. Amma kuma zaku yi dinner?”
“A’a” suka hada baki.
Sai kuma suka kalli juna suka yi dariya.
“Toh aure kawai zaku yi kenan?”
“In Sha Allahu.” Abdallah ya amsa.
Sai ta kara komawa wajan Nafisa, tace “kema sunan ki qalbi ne?
Kema zaki auri uncle ne?”
“A’a ni kam sunana Nafisa, kuma wani uncle din zan aura In Sha Allahu ba wannan ba. Ai wanan na habibty ne ita kadai.” Nafisa ta fada tana taba kumatun ta.
“Wacece habibty kuma?” Tayi tambaya confusely.
“Aww sorry, amma qalbi habibty ta ce, kuma qalbin uncle din ki.”
“Toh naji.”
Suna cikin hira, Afra na masu questions, su kuma suna amsawa, Adda Fadi da mijin ta suka yi sallama.
“Ina ini” Olamide da Nafisa suka fada tare.
Sanda ya zauna, yace “an yi ni lafiya”
“Lafiya kalau. Mun same ku lafiya?” Su biyu suka fada.
“Lafiya kalau alhamdulilah. Kun zo lafiya, ya gajiyan biki?”
“Lafiya kalau alhamdulilah.” Suka amsa.
“Toh MashaAllah. Ina amaryar mu acikin ku, ko bata zo ba ne?” Mijin Adda Fadi uncle Isah ya tambaya.
“Kai love, wannan kuma wani irin tambaya ne. Ga amaryar nan mai jallabiya bakin nan.”
“Haba dan Allah! Wannan ai bafulatana ce.” Ya fada in shock.
“Kai ma dai zaka fada. Wallahi da Abdallah bai fada mun asalin ta ba, da ban yarda ba.”
“Ni dai haryanzu I find it hard to believe. Zan baki dan wani assignment amaryar mu, ki yi tambaya agida, afada maku asalin ku, dan ko kawu Dajjo ya gan ki, kuma ba’a fada masa yaran ki ba, bazai sani ba.”
“Haka ake cewa, kuma munyi tambaya, duk wanda muka tambaya, suce mu yarbawa ne”.
“MashaAllah. Shi yasa discrimination ba kyau, Allah mai yanda yake so da bawan sa. Allah ya kai mu lokacin auren ku.”
“Amin”Abdallah ya fada da karfi.
“Kai auta ko kunya” Adda Fadi ta fada.
“Toh kunyan me zan ji, addu’a aka yi kuma na amsa.
“Toh yayi”. Ta fada tana hararan shi.

Haka suka ita hira, suna dariya, har Olamide tazo ta sake. Cikin hiran ma suna ta tambayan ta questions, kuma alhamdulilah tana amsawa yanda ya kamata. Sun ci sun sha, saboda Adda Fadi bata bar su ba, sanda taga suna ci, kuma suna shan duk abubuwan data kawo masu.

6:pm nayi, Olamide ta ma Abdallah text, wai ya koma da su, yasan dai gobe zasu koma, so they are things they will like to do before going back. Yana ganin message din ya share, yayi kaman bai gani ba, ya dago kai suka hada ido, ya dauke idon sa. Ta kara mai wani message din, yaki.
Sanda tace “ammm Adda Fadi, zamu wuce, kin san gobe zamu koma, ya kamata mu dan zauna da kawar mu kafun mu koma, kuma zamu shirya wasu abubuwan mu.”
“Baki yi karya ba, amma why not ku bari anjima?”
“Haka nima nace, amma ta ki.” Abadallah ya fada.
“A’a ba wai taki bane, gobe fa da sassafe zamu koma, kun ga ya kamata mu tafi yanzu.” Nafisa ta fada tana murmushi.
“Toh in kuka koma, sai kuma yaushe?”
“Yaushe?” Olamide ta tambaya, sai tayi wani irin murmushin da dukan su suka yi dariya.
“Sai anyi auren kenan ko?” Adda fadi ta tambaya.
“A’a fa ban ce ba.” Ta fada a kunyance, tana wani rufe ido, muryar ta kasa kasa, amma sunji ta.
“Oho dai, mu dai munsan maanan haka.” Adda Fadi ta fada.
“Allah ya kaimu lokacin, ya daura ku akan duk wani makiyi, ya sa iyayen mu su yarda, kar suma su nuna banbanci, su yarda da wannan union din, saboda hadin nan In Sha Allahu zai yi kyau.” Uncle Isah mijin Adda Fadi ya fada.
“Amin” kowa acikin parlorn ya amsa.
“Toh Adda zamu wuce”. Abdallah ya fada.
Ai suna jin haka, suma suka tatara jiki suka tashi tsaye.
“Gaskiya ban ji dadin wucewan ku din nan ba, amma na ji dadin zuwan ku sosai alhamdulilah. My prayer is also for this union to happen wallahi, saboda kin gama mamaye zuciya na qalbin Abdallah. Allah ya sa iyeyen mu su yarda, kinga alokacin, zamu dinga haduwa anyhow. Gashi kema Fisa, idan Allah yayi, kema nan zaa kawo ki, wato three three kenan kuka yi. Allah yasa ayi auren ku kuma, ku zo Gombe, ku dinga zuwa wajan wannan addan ta ku, maybe ma by that time mun saba da Nabila, dan nasan Farouq zai kowa ta wajan fav sis din su.” Ta fada tana murmushi.
“Toh Allah yasa.” Olamide ta fada.
“Mu tafi.” Abdallah ya fada.
Zasu fita, Adda tace ku jira ni ina zuwa, bari in sa hijab. Tana barin wajan Olamide ta mika ma Afra leda, na thank you, cike da sweets da chocolate, wafers, da dai sauran su. Tana mika ma Afra, ta gani, tace “yay chocolate, nagode sosai qalbin uncle da adda Fisa.” Ta fada tana hugging din su.
Abban su ma yayi godiya, sai ga Adda Fadi ta shigo, itama da leda cikin hijab, ba zaka gane ma ba, sai ka kare mata kallo, ta ce “muje.”
Duk suka fita waje, Abdallah ya bude gate, sannan, ya fita da motan sa, alokacin Adda Fadi ta jawo hannun Olamide, tace “In Sha Allah, me and him, zamu san yanda zamu yi da family members din mu, dan Allah kema kiyi kokarin convicing din mummyn ki, wallahi ban taba ganin kani na yaso wata ya mace ba haka, kuma daga bisa duka alamu, kema kina son shi. Wallahi zuwan ki yau yasa nayi clearing kai na and my thinking akan tribalism. Am soo happy I met you wallahi. In Sha Allah I will always put you guys in my du’a. Kar ki ce a’a, dan Allah ga wannan.” Ta mika ma Olamide.
Olamide ta amsa, ta mata godiya. “Adda nagode sosai, Allah ya saka maki, ya raya maki yara. In Sha Allahu zan fada ma mummy, moreover, nasan ta wajan mummy bakomai, but still zan fada mata and thanks for accepting me, I can’t thank you less wallahi.” Olamide ta fada, bata ma san lokacin data yi hugging din Adda Fadila ba, har da wayen ta.
“A’a kar ki mun kuka Abdul ya gani yace na fada maki abu ne.” Adda Fadi ta fada tana goge mata hawaye, suka ji ana horn, sai Adda tace “ga wannan ki ba habibtyn ki, mu je kafun ace ina tsungulin ki.” Dariya su biyu suka yi, sannan suka fita, Olamide ta shiga gaba, daman Nafisa ta riga ta zauna a baya.
Data shiga, suna ta waving din juna, har suka bace ma juna.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Leave a Reply

Back to top button